74

427 21 0
                                    

*🤦‍♀🙆ILLAR RIK'O*

_*('yar  rik'o)*_

       *Na*

_*Aysha  Isa (Mummy's friend)*_

_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_

*LITTAFAN MARUBUCIYA*

_*1. Na Tsani Maza*_

_*2. Meke Faruwa*_

_*3. Ruhin 'Dana*_

_*4. Shi Nake So*_

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS (ZAW)*
'''(Gidan zaman lafiya da amana In Shaa Allah)🤜🤛'''

https://www.facebook.com/ZAMAN-A MANA-Writers-FANS-311893699485963/

*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*

_*Don Allah duk mai wannan littafin daga farko ta taimaka tamim sending ta wannan number 08146960525, nagode.*_

_*Ga masu niman wannan littafin daga farko suyi hak'uri nima bani da ita, please in kun samu karku manta ku min sending ta wannan number dake sama. Zaku iya samun sauran littafaina a wattpad kamar yanda na rubuta a sama.*_


_*Page 74*_


"Ko kuma a kasheta kawai kowa ya huta. Ko ya kuka ce?" Gaje ta waigo gefen da su Luba da Baba ke zaune.

Luba ce ta fara magana tace " a'a ai kwara an haukatata da a kashe ta, ko Baba?" Luba ta k'arasa da tambayar Baba wacce ta zaune kusa da Gaje.

" Hmmm! Nidai in so samu ne kwara an barta a gidan sai a d'auke hankalinshi daga gareta ai yafi..."

"Duk naji zantukan ku, amma kusani kasheta ko haukatar da ita duk ba abu bane mai sauki don tsaye take kan ibadun ta, ga kuma yaran da take dasu duk ta horesu da haka..." cewan mall. Zalimu ( bokan)

"Allah gafarta mallam yanzu  ya za'a yi kenan?" inji Gaje cikin da fargaba jin abinda yace.

"Hhhhh! Ba abin tada hankali bane, bari mu fara ta kanshi mijin tunda ga Uwarshi nan zaune abin zai fi zuwa da sauki..." zane-zane yafara yi kan k'asan dake gabanshi, can sai ya kira sunan Abba har sau uku bai amsa ba, a na hud'un ne boka. Zalimu ya umurci  Baba da tazo ta kira shi, cikin tsoro jikinta gar ya soma b'ari ta kirashi,  kai kuwa tana kiran shi kiran farko sai ga Abba( Ahmad) ya fito jikin k'yalen dake take jikin bango d'akin. Mik'ewa Baba tayi cike da tsoro zata gudu ta bar d'akin don a iya rayuwanta bata tab'a ganin irin haka ba sai dai a wasan kwaikwayo. Dakatar da ita bokan yayi, ba shiri ta tsaya don ta riga ta tsorata da al'amarin shi, na take ta fara dana sanin zuwanta gun.

"Zo ki fad'a abin kuke min kuna son ya aikata"

Cikin sanyi jiki da tausayin yaronta ta k'arado gabanshi sunan shi ta kira sau uku kamar inda Zalimu ya umurce ta tayi sannan ta fara fad'in " ina son a cikin satin nan ka aure Luba, kuma bana son daidai ya rana d'aya na musguna mata, komai tace maka tana so shi zaka aikata, daga yanzu bayan ni mahaifiyanka bana son kaji magabar kowa sai nata,daga k'arshe ina son ta zamo mace d'aya tak da idaniwanka zasu rik'a gani a matsayin mata"
Duk maganar da tayi gyad'a mqta kai Abba ya dinga yayi, har saida  ta fara fad'in " Bana son na kuma ji ko ganin ka ambaci wata mai suna Kuluwa (Ammi) a rayuwanka.." b'acewa yayi abinsa maimakon ya gyad'a mata kai kamar yanda ya saba.

Dakatar da ita Bokan yayi ta hanyar fad'in " wannan ba huruminki bane, wannan aikina ne."

Hak'uri ta bashi, sannan yace Baba da Inna su basu wuri akwai aljanin da zai zo yayi ma Luba aiki, wani irin k'ara Liba taji cikinta yayi jin abinda yace, yayin da Baba da Inna suka fita suka bar d'akin shima mik'ewa yayi ya bi wata hanya. Yana barin d'akin na take duhu ya mamaye d'akin, jin tayi kamar hannu na yawo a jikinta, baki ta bud'e da niyyan yin ihu taji an cafkw bakin haka dai abin ya gama murzanta don ransa kafin ya k'yaleta ko tausayin cikin sake cikinta bai jiba, bayan komai ya lafa d'akin har yanzu dai cikin duhu take ji tayi an kaita wani wuri kafin ta ankara taji an kwara mata wani irin ruwa mai d'an banza wari dagta sama ta har kanta dama kuma babu komai a jikin nata, cud'a taji an farayi ta kowani lungu da sak'o na jikinta da sunan  wanka sai kace yarinya duk iya k'ok'arin ta nagani ko waye ta k'asa gane ko waye.

_(Hattara dai mata, wallahi wannan abun na faruwa da gaske,wasu ma akan idonsu bokayen zasu ce zasu masu wanka magani, haka zasu bari wani k'aton banza ya dirje ta wai da sunan yana mata wanka, duk wannan kuma yawanci kan d'ana miji ake yinsa wanda wani ma bai san kina yiba. Allah ta shiryemu kuma ya ganar damu.)_

Bayan wasu mintina aka maida ta dakin da take tun farko can sai taga harke ya gauraye d'akin, kayanta da tagani a gefenta ne ta kwasa ta sanya a jikinta ba tare da ta damu da tsane ruwa dake jikinta ba. Babu inda baya ciwo a gab'ob'in jikinta don da k'yar ma ta samu ta saka tufafi a jikinta. Wuri ta samu ta kwanta ko zata jiki d'an dama-dama, bata jima da kwanciya ba mallam Zalamu ya shigo d'akin su Inna na biye dashi a baya.

Zaman yayi kan buzunsa, itama kuma Luba ta mik'e da k'yar ta zauna. Wasu kulli magani ya fito dashi ya mik'awa Luba amsa tayi sannan yayi mata bayanin yanda zata yi amfani dashi.

Kafe bokan Luba tayi da ido zuciyanta na bata kamar shine ya aikata mata wannan aika-aikan, Allah ya isa ta rik'a masa a zuciyan har suka masa sallama bayan su ajiye masa makud'an kud'in wanda duk wayanci daga aljihun Baba ya fito, mik'ewa sukayi sannan suka d'auki hanyan komawa gida a lokacin har gari ya fara duhu ko.

Da k'yar suka masu abin hawa don dare yayi sanda suka iso bakin titin, koda suka isa gida mai gadi ya riga ya rufe k'ofa ko da k'yar suka samu ya bud'e masu k'ofa, d'akin su suka nufa kai tsaye ko wannensu wurin kwanciya ya nima babu maganar sallah.

B'angaren Abba kuma tun bayan dawowan shi daga wurin boka Zalimu yake jin kanshi wani iri haka dole ya bar aikin da yake yiya koma gida. A falo ya sannu Ammi a zaune amma ko sallama bai yiba hasalima bai san da zaman ta a gun ba. D'akinsa ya nufa kai tsaye ya fad'a kan gadonsa ba tare da ya cire ko takalminsa ba. Ammi ce ta shigo d'akin da sallama ta k'araso ciki, gefen gabon ta zauna amma abin mamaki wai har ya riga yayi barci ko, takalmansa ta cire masa ta kaisu ma'ajiyinsu sannan tazo ta gyara masa kwanciya, addu'o'i ta tofa masa ta lullub'e sannan ta bar d'akin cike da zullumi had'a da addu'a Allah dai yasa lafiya mijin nata ya dawo warhaka don ba haka ya saba dawowa ba.

Sai da ya d'auki kusan awani biyu yana bacci sannan daga bisani ya tashi. Sallan magrib da Isha ya gabatar a d'akinsa abinda bai saba ti ba don ko a gar ciwo yana iya bakin k'ok'arinsa ya tafi masallaci.

D'aki Ammi takai masa abinci don tasan da k'yar ne zai iya zuwa dining cin abinci.

Da k'yar Ammi ta samu Abba ya d'an ci abunci don da fari ce tama yayi ya k'oshi. Bayan ya kammala cin abin take tambayansa abinda ke damunsa sa, ba tare da b'acin lokaci bata amsa yace " Kuluwa aure nake son in k'ara kuma a cikin wannan satin."


Muje zuwa.

_Idan kece Ammi ya zakiyi?_

_Kuna ganin su Luba zasu cimma burinsu kuwa?_

_Wai ina labarin Suwaid ne?_

Ku kasance tare dani don jin wannan amsoshin.

_*Do comment so that I will be able to update soon.*_

_*🌹Mummy's friend ce🌹*_

ILLAR RIK'O ('yar rik'o)Where stories live. Discover now