57

379 22 0
                                    

*🤦‍♀🙆‍♀ILLAR RIK'O*

  _*('yar rik'o)*_

        *Na*

_*Aysha Isa (Mummy's Friend)*_


*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS*
_(Gidan zaman lafiya da amana, In Shaa Allah)🤜🤛_

_*Addu'arku ta karb'u yau na sambad'o maku illar rik'o. Wlh ban manta da shi ba sai dai a gasky yana bani kiwuyan typing cox makarantan shi basu dayawa.*_

_*🗣🗣🗣My aunty @ Aishan Umma have long being looking for you amma har yanzu shiru, Allah yasa wannan shirun ta lafiya ce,  please me lambarta yayi sending 🙏🙏🙏🙏*_

_*Aunty Ringim*_
_*My Teema*_
_*Aunty Aisha*_
_*Aunty Jidderh*_
_*Husna*_
_*Kusani don ku d'aya ya saka nayi typing yau sabida haka yawan sharhin ku will determine my next post😜😜😜*_

_*BIMISMILLAHIR-RAHMIR-RAHIM*_

_*Page 57*_

Kasa magana tayi jikinta sai rawa yake kwalla taf cike a idonta.

A tsawace Jabir yace "bake nake magana kin min shiru?"

Durkushewa tayi a gub ta fashe da kuka maimakon ta bashi amsa gabanta sai dukan uku-uku take.

Tashi yayi a hasale, hannunta yaje suka fito daga office ya kulla direct din yayi parking motar sa yaje ta bude ya jefata ciki, ya zagayo mazaunin driver yaje su suka nufi gida. Suna isa gida ko gyara parking motar sa baiyi ya fito ya zo ya bude gefen da Luba ke zaune ya jawo da karfin sai da hannunta ya amsa don yayi fushi matuka, janta ya cigaba da yi har saida suka isa falo ya sake ta, fad'uwa tayi wanwas a kasa wanda ya jawo hankalin Ammi take zaune a falo tana jiran dawowarsu, mike tsaye tayi tace "subhanallah Jabir ya haka kuma,  zaka jimata rauni?"

"Ammi wallahi gwamma naji mata da wannan abin kunyar da take shirin jawo mana"

Ammi na jin haka gabanta ya shiga fad'uwa tabbas ciki ya tabbata kenan don daga jin maganar Jabir tasan da magana "hmmm toh ai ba haka ya kamata kayi ba,  bayani ya kamata kamin dan musan yanda zamu b'ullo ma al'amarin..."  ta karisa magana had'e zama.

Kujeran dake kusa da ita ya zauna sannan ya faro kora mata bayani.

"What! Ciki fa kace har na tsawon wata uku?"

Gyad'a mata kai yayi alamar eh.

"Luba wa ya maki ciki?"Ammi ta fad'a cikin kaushin murya, irin murya luba bata tab'a jin Ammi tayi magana da ita.

"Ya ilahi wa zance ya min ciki yanzu,  Suwaid zance wanda yanzu tsawon wata d'aya babu shi babu dalilinsa don har gidan da suke sheke Star su taje nimansa amma a kulle yake,  yanzu wa zata ce?,  na shiga uku Allah ka fiddani " Luba tace tana ta fashe da matsanancin kuka.

"ke bamu son munafinci fa lokacin da kike biye masa kin manta da irin haka zata iya faruwa ne don wallahi ko n bk rantsuwa zan iya yo kan cewa ba dole aka yimaki ba"

Kasa cewa komai Ammi tayi tana tunani a zuciyata tace "kodai tun fyad'e da tace anyi mata ne?,  anya ma fyad'e aka yima kuwa?,  wallahi ita Luba tsoro take bata don baka iya banbanta tsakanin gaskiyarta da k'aryata, bana wannan ba me zata cewa Abban Yusrah da iyayen yarinya,  ai cewa sakacin ta da rashin adalci ya sanya luba tayi ciki amma 'yarta kalau take, na shiga Luba kin tonar asiri gashi dama ya na k'are da Ina balle yanzu da haka ba faru kuma" hawaye ne ya fara zuba jan fuskatar tace "Luba don Allah ki fad'a min wa ya maki ciki?"

Shiru bata ce komai ba,  a hasale Jabir ya tashi ya rufeta da duka da k'yar Ammi ta samu ta kwaci Luba daga hannun Jabir.

"Jabir let her be,  Allah na shaidata kuma kuma shaida ne na rike Luba da amana amma ta rasa abinda zata saka min dashi sai.... "kasa karisa maganar tayi sakamokon kukan da yaci karfin ta, mikewa Jabir yayi ya koma kusa da Ammi,  hawaye ya shiga goge mata yana rarrashin ta shima kamar zai zubda kwalla don ya manta rabon yagan Ammi na zubda kwalla,  "Ammi don Allah ki daina zubda hawayen ki akan wannan yarinyar" yace cikin sanyi murya.

"Jabir me zance ga iyayenta da kuma kaka ku?,  kaima kasan sam bamu samun jituwa a tsakanin mu,  na Abbanku me sauki don shima shaida  ne kan irin tarbiya da na baku. "


"Karki damu Ammi In Shaa Allahu komai zai zo da sauki,  kinji Ammi na"yace yana me kwanto da kansa kan kafadarta.

Murmushi tayi tana sha kansa son d'anta yana k'ara ratsa cikin zuciyarta. Ganin tayi shiru bata ce komai ba sai murmushi take,  Jabir ya katse shirun ta hanyar cewa " Ammi muje nayi maki tausa kiyi barci.. ", mikewa tayi tace " tam muje " sannan nufi dakin Ammi, rarrashinta tayi kanan ya mata tausa har barci ya dauketa sannan ya baro daki. A falo ya sami Luba kwance nan inda ya barta tana barci, tunkarinta yayi  da k'afa,  firgit ta mike tana murza ido,  cikin tsawa yace " munafuka nan ne kika saba kwanciya?, salon a yazo a ganki nan kwance ace ana musguna maki"

Kura mashi ido Luba tayi baya kiftawa. 

"Zaki tashi ko sai k'ara maki wani dukan kin kura mani sai kace mayya" Jabir ya fad'a tsawace.

Da gudu ta tashi ta bar falon ganin ya nufota, da isarta ta fad'a kan gado tana mai da numfashi, can ta lula tunanin mafita kan Abba ya dawowa,murmushi ta sake da dukkan alamu ta samu mafita.

Haka su Bintu da Yusrah suka dawo daga makaranta suka tadda gidan sam babu dadi sabida rashin walwalar Ammi. Matsawa Ammi da tambaya Yusrah tayi har da Ammi ta fad'a mata dalili,  cike da mamaki Yusrah tace " ciki fa kika ce Ammi."

"Kwarai kuwa,  kuma wallahi kin bani mamaki Yusrah a ce kina sane 'yarki na dauke da juna biyu Anna ki kasa sanar dani, meyasa Yusrah?"

Zaro ido tayi gabanta na dukan uku-uku tace "wallahi Ammi ban sani ba. "

"Toh shi kenan ki tashi kije"

"Tam Ammi" har takai bakin kofa ta kara juyowa tace " Ammi don Allah kiyi hakuri wallahi bansani ba ne."

Murmushi Ammi tayi tace "nayi Yusrah kuma na tabbatar iya gaskiyarki kika fad'a min"

"Nagode Ammi" Yusrah tace sannan ta fice daga dakin.

Da yammacin ranar bayan Adda ya dawo daga wurin aiki Ammi ta sanar dashi abinda ake ciki, fad'a ya rufeta dashi yace "Wannan wani irin sakaci ne haka?,  ace kina tare da yarinya amma ki kasa gane tana da ciki har na tsawon wata uku,  haba mana Kuluwa"

Hakuri Ammi tayi ta bashi kan daga bisani ya d'an tsakaita fad'an yace "yanzu me kike son na cewa iyayen ta?,  a gefe guda kuma ga Inna don dazu ma mukayi waya da ita take shaida min tana tafe gobe"

"Innalillahi wa ina ilahi raji'un,  yanzu meye mafita?" Ammi tace tana me kurawa Abba ido.

"Sai indan ta zo zamu sani don nariga nace mata ina gari domin bansan zan zo na tadda wannan lamarin ba"

"Allah ya kawo ta lafiya " Ammi tace cikin sanyin murya.

°°°°°°°

Washegari safe Inna ta dako sammako don a gidan ne ma tayi karin kumalo. Bayan sun kammala karin ne Inna wacce ke ta faman bin Luba da kallo tace  " 'yanan zo nan. "

Mikewa Luba tayi ta koma inda Inna ke zaune ta zauna gefenta tare da sunkunyar da kanta sa kasa.

Sai da Inna ta k'are mata kallo tsaf sannan tace "hala kinyi rashin lafiya ne?,  naganki kinyi fari fat dake  sai kace mai shigar ciki"

Ras Ammi taji gabanta ya fad'i babu abinda take nanatawa a zuciyarta banda innalillahi wa ina ilahi raji'un.

K'ara tambayarta Ammi tayi a karo na biyu amma shiru Luba bata ce komai ba illa ma kukan da ta fashe dashi.

"Mts,  munafuka kawai ana magana sai ta fashewa mutane da kuka,  bari ki ji inna ciki gareta kuma taki fadan ko na waye" Jabir ya fad'a a hasale.

"Ciki?! garin yaya haka ta faru kuma zaune?, ke uban waye ya maki ciki? "

Cikin kuka Luba tace " Abb ...... "




Muje zuwa

_*Mummy's friend ce🤩*_

ILLAR RIK'O ('yar rik'o)Where stories live. Discover now