59

335 23 0
                                    

*🤦‍♀🙆‍♀ILLAR RIK'O*

  _*('yar rik'o)*_

        *Na*

_*Aysha Isa (Mummy's Friend)*_

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS*
_(Gidan zaman lafiya da amana, In Shaa Allah)🤜🤛_

_*BIMISMILLAHIR-RAHMIR-RAHIM*_

_*Train your mind to see the good in people. Always remember that the good you find in others is a reflection of the good that is in you.*_

'''Please kuyi hakuri dani bana jin typing ne a 'yan kwanakin nan🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏, don Allah bear with mummy's friend'''

_*Page 59*_

"Don samun kwanciyar hankali da gujewa fad'awa irin wannan halin da muke ciki nan gaba."

Yusrah tace "Amma Ammi ni bana jin Bintu zata iya aikata hakan kuma...... ","Shhh" Ammi ta dakatar da ita sannan tace "wannan shine hukuncin da na yanke"mikewa tayi ta barsu gun zaune cike da tunanin sauyinta.

Hawayen da Bintu ke kokarin boye zubo kan kuncinta,  a gaskiya Luba ta cuce ta don gashi sanadiyar ta Ammi tace a maida ta amma ko bakomai yakamata Ammi tayi mata uzuri tunda ba ita ta aikata laifin,  amma bata gan laifin Ammi ba don dama ance wake d'aya ke b'ata iri, tashi tayi ta gudu ta nufi dakinsu,  drawern kayanta ta nufa kai tsaye ta shiga jera su cikin bakkonta tana kuka,  Yusrah ce ta zo ta dafata tace " Bintu don Allah kiyi hakuri."

Murmushin yak'e Bintu tayi tace " bakomai Yusrah Ammi tayi gaskiya kuma nagode da irin kaunar da kuka nuna min."

"Bakomai Bintu wallahi ni a matsayin 'yar uwa na dauke ki" cewar Yusrah,  hannun ta saka itama rana taya Bintu linke kayakinta.

************

Inna ce zaune kofar dakinta ta rafka uban tagumi,Hanne watoh matan Salale ce ta fito daga ta daki da k'aton cikin a gaba haihuwa yau ko gobe da kyar ta kariso gun inna ta zauna tace "Inna sannun da hutawa" shiru inna tayi ba tace uffan ba asalima bata ma san da zuwan ta,  daura kai Hanne tayi a kafadar Inna,  firgit Inna tayi, Hanne tace " wai Inna don Allah yaushe zaki daina wannan tunanin ne?"

"Sai ranar da Bintu na ta dawo gareni "

"Hmm! amma ai naji kawunta yace tana lafiya."

"Haka ne amma nidai nafi son na ganta da ido da ido,  yanzu fa rabon da inganta da ido tun bikin ku fa, akalla shekara 2 kenan don koda kikayi haihuwar fari ba zuwa tayi gashi har kina kan na biyu."

"Haka ne Inna amma don Allah ki kwantar sa hankalin ki In Shaa Allah tanan cikin k'oshin lafiya."

"Allah yasa,  zan basu nan da sati biyu idan bintu bata zo ba zan je na dauko d'iyata don a gaskiya hakuri na ya kusan k'arewa... "

"Kai Innan Bintu baza'a yi haka ba ma In Shaa Allah."

"Allah yasa"

"Ameen Inna, bari naje na daure sanwa" Hanne tace tana mikewa da k'yar.

Wannan kenan.

***************

Yau Umar ya waye gari haka kawai yaji yana muradin ganin Bintu,  shiryawa yayi cikin manya kayan kaftani fari k'al dashi sai shek'i yake kamar ango, part d'in  mummy ya nufa kai tsaye,   a falo  ya samesu zaune akan cushion Ummi na daga gefen ta, risinawa yayi har k'asa ya gaida mummy ta amsa masa, sannan shima Ummi ta gaida tace " yaya ka gan yanda kayi kyau kuwa kamar sabon ango?"

Mummy ne ka kare mashi kallo tace " ashe na kusan samu surika wannan kwalliyar haka?, 'yar gidan wacce yarinya da ta cancanci haka"

Susa k'eya yayi  yana murmushi yace "mummy gidan Abbanmu zani fa"

Muje zuwa





*Mummy's friend ce🤩*

ILLAR RIK'O ('yar rik'o)Where stories live. Discover now