*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
_{Novel series}_
*_[♠️SEASON.2 ♠️]_**WATTPAD @Smart_Feenert ...✔️*
*_[🥀Be ~ Smart 🥀]_**_🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂_*
—•—•—•«»«»«»«»•—•—•—*_Episode ~ 3_*
A palourn suka sameta ta na ta gudanar da sallarta ta azahar, dan a wannan lokacin ma aka fara kiran sallar La'asar.
sun kwashe tsawon mintuna suna jiran k'arewarta amma shiru ko samata babu domin raka'a daya kafin a kai k'arshenta sai an b'ata wasu 'yan mintuna.
Ganin abin ya k'i ci ya k'i canyewa ya sa Uncle mukhtar mik'ewa tsaye yana ce ma "Ni zan tafi! anjima zan dawo."
a sanyaye ta ce "Uncle a dawo lafiya.!"
Ya ce "Ameen" ya yi tafiyarshi, wanda kuma ko 3mins bai yi da tafiyar ba Hajiya Kaka ta sallame sallar ba tare da ta ce da fatima komai ba ta sake tayar da sallar la'asar, ita ma fatimar tashi tayi ta dauro alwala ta soma gabatar da tata, har ta k'ark'are sallar, Hajiya Kaka na zuba tata babu qaqqautawa.
Sosai fatima take kallonta cikin mamakin yanayin yanda take gudanar da sallar kamar wadda kwai ya fashe ma a jiki. Sai ka ce wadda ke rankon sallar shekara daya.
Sai da Hajiya kaka ta shahe wajen 15mins tana sallar, sannan ta qarqare gabadai, bayan ta gama addu'o'inta har ta shafa, fatima ta sauko daga saman kujera ta gaidata cikin hankali.
Ta ce "Hajiya an wuni lafiya?"
Cikin daga murya Hajiya Kaka ta ce "Munahuka! Da ban wuni ba zaki ganni halan Makira? wato ke gaki tsirarra da zuwanki kin dale saman kujeru kin zauna sai ka ce na gidan Ubanki, wallahi dik na sake ganinki a samansu sai jikinki ya gaya maki, innemar bak'ar shegiya debabbiyar albarka, sannan kuma na rantse da Allah dik maganar da kuka yi tawa ke da mahaifiyarki ta khairan ko ta shairan, billahillazi na barku da Rabbul-Samawati dan shi kadai ne zai iya fidda man hakkina akanku miyagun banza! Ba zaki tashi ba ne ki bace man da gani ba saina mazgeki wajennan? kin sako man idanuwa kamar bakuru kina kallona sai kace mayya! to sai ki shirya aiki na can waje yana jiranki, ko yanzu in jissa haushin buguwar Azumin nan a jikinki shegiya marar Imani."
A hanzarce fatima ta tashi ta nufi waje, domin fara aikin tin kafin Hajiya kaka ta aikata abinda take da niyya a kanta, wanda tana fita kuma suka hade da Hajiya Saudat a waje, ta tsaya tana gaida ta.
Tun a cikin kuryar daki suka jiyo muryar Hajiya Kaka na fadin "La'ilaha illallahu Muhammad Rasu lillahi sallallahu Alaihim wasallam." gabadai hankalinsu ya tashi domin su dik a tinaninsu wani mummunan abu ne ya faru da ita, kan suyi wani yunk'urin tafiya wajenta su dubo abinda ya ke faruwa, tini suka jiyo muryarta cikin balbalin bala'i tana fadin "Sama La ibilis! daga da wowarki yau yau d'innan har kun fara zabga tsiyar?, dan ubanki aikin gaidata na sakaki ko kuma aikina? tinda yau Allah ya jabceni da yin abincin sallah, billahillazi dik kika bari na cin maki a wajennan tsaye sai na barki kwance, shegiya talafaffiyar banza."
Cikin hanzari fatima ta bar wajen ta nufi hanyar kitchen ita ma Hajiya saudat dakinta ta koma amma ba dan tana tsoronta Hajiya Kaka ba, sai dai kafin ta ida kurdewa cikin d'akin, tini ta ji Hajiya kaka ta jefo mata magana da cewa "Andaiji haushi wallahi, shashasha." ba ta ce da ita komai ba ta ida kurdewarta ciki.
—•–•«»•–•—
_Ammie ce kwance saman cambed a waje, ita da Balkisu suna mulmulniya a sama ta sanadiyyar dukan da Azumin ke masu, bacin sun gama cika cikinsu tab da abinci a cikin daki, inda Zuhriyya da Nadiya dake Azumin gaskiyar basu ji azumin kamar yanda su suke k'aryar suna ji ba.
Daddy ne ya shigo gidan shi da Ado direba, dauke da lododi cefane niqi-niqi a hannayensu.
Da hanzari su Nadiya suka tashi suka karbe kayan a hannun daddy, inda daddy kuma ya maida dubanshi gasu Balkisu dake kwance kamar kayan wanki.
Ya ce "Assha Yar'baba harda ke cikin masu Rakin Azumi?"
cikin wata kasalalliyar murya Balkisu ta ce "Wlhy Daddy Azumin daren sallah wuya ne da shi."
Ammie ta ce "Wlhy ni har kaina ma ke sarawa, ina jin zazzabi na son rabkeni."
Daddy ya ce "ku k'ara hakuri dai, ku samu ku idashi lafiya tunda daga yau ne kuma sai bayan sallah da za ku ranka wadanda kuka sha lokacin da ba kwa da lafiya! ga sauran kayan nan dai na sayo wadanda kuke buk'ata, Zuhra ke da Nadiya naga alamun kun d'an fi su jarumta, ku fidda kajinnan daga cikin lododin da suke karsu lalace anjima bayan ansha ruwa sai ku fara aikin."
Suka ce "Ok Daddy."
Daddy ya nufe part d'inshi ya watso ruwa ta dalilin gajiyar da ya kwaso, dik da ba wata gajiyar ba ce face ta zaman moto, domin komai Ado direba ke yi.
—•–•«»•–•—
Washegari da sassafe misalin karfe 8:am kowa ya tashi ya fara shirye-shiryen wankan tafiya Eid, Inda kuma ko ina ka duba zaka ga yara da manya, mata da maza suna shiga gida-gida suna kai Abincin sallah kamar dai yanda yake a al'adance a Sokoto.
8:40am dik masu zuwa Eid sun halarta a waje, inda wasu da motocinsu zasu je wasu kuma mashunansu, wasu acab'a, wasu napep, dadai sauransu, inda kowa ka kalla harmar tafiyar yake cikin sauri dan kar ya rasa sallar.
Bayan an je an dawo, aka fara shiryar da bukukuwan sallah, a bangarori daban-daban inda wasu ke tafiya gidan SARKIN MUSULMI wasu kuma MTA wasu gidan ZOO wasu FILIN SUKUWA da dai sauransu wajeje da dama acikin garin sokoto.
Ma sha Allah haka aka gudanar da bikin murnar sallah lafiya ba fada balle wata hayaniya, kowa yana cikin farin ciki abin gwanin birgewa.
—•—•:«»:•—•—
Bayan kwana Ukku da Sallah aka saka ranar auren Balkisu da Uncle Mukhtar sati daya da sallah wanda ya rage yanzu saura kwana hudu, inda ko ina ka zaga cikin bangare nan biyu shirye shiryen bikin ne ake gudanarwa .
B'angaren Amarya Balkisu kuwa tini sun gama tsara komai ita da abokananta akan ba wani event da za'ayi hatta da walima ba za'ayi ba, ita dai burinta ta shiga gidan.
Haka ko aka yi domin dik wanda ya tambaye dalili sai su ce lokaci ya k'ure bikin ya zo kusa da bikin murnar sallah, dan ko anko sunce ba zasu yi ba, fito na fito za'ayi ranar yinin bikin kowa ya saka kalar tifafin da ranshi yake so.....
Follow me on wattpad and vote.
YOU ARE READING
WAHALA DA GATA season2
FantasySeason 2. "Hhh ai gaskiya ne Rukayya ni wlhy kin san Allah sai yanzu na san nayi dace da sarakkuwar ta gari domin waɗancan dik sheguna ne matsiyata." "Sosai ma Hajiya! ai Aunty Balkisu kam, ta wuce kowa a cikinsu, sannan ta......" Sa...