*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*
*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
_{Novel series}_
*_[♠️SEASON.2 ♠️]_**WATTPAD @Smart_Feenert ...✔️*
*_[🥀Be ~ Smart 🥀]_**_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_**_🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**_Episode ~ 13_*
Ko 5mins ba ayi ba suka isa wajen, inda binciken komai ba a tsaya yi da su ba. aka daukesu gabadai aka rumtuma cikin wani dan k'aramin cell da ko mutun biyar aka saka a cikinshi sai sunji jiki balantana mutum sama da hamsim.
Cikin wani irin yanayi mai cike da nadama, wasu suka dan samu waje suka zauna, wasu kuma suka yi tsaye carko-carko kamar itace, dan akan matsuwar wajen, wajen ma da zaka dan gincira kafadunka gashi kana gani amma wasu sun rigaka, ga kuma wani irin warin tsiya dake tashi a wajen yana ziyartar cikin kussayen hantunansu, wanda hakan yayi sanadiyyar burkucewar cikin wasu daga cikinsu, inda nan take suka shiga bankama sauran tusoshi masu bala'in warin tsiya kamar dunge.
Inda wasu daga cikinsu kuma suka kasa daure ma jin wannan shegen uban warin, suka shiga zabga amai a dik inda suka samu, wasu kuma suka shiga kurma ihu harda su k'arin Allah ya'isa.
Hajiya Munira ita da Yaranta makure suke yi a wani gefe, warin tusa da warin d'akin, dik ya gama bugar da su a wajen abin gwanin ban tausaye.
_suna cikin ihunsu na bidar taimakon gaggawar fita cikin wannan bak'in bala'in. wasu Police's mata guda biyu manya-manya da su ko waccen dam take da qaton tumbi ga kuma uwa uba k'iba sai kace samudawan dori, kuma da ka kallesu kasan basa wasa wajen gudanar da aikin'su.
A harzuqe suka bude k'ofar cell din da aka saka ma key aka rufe, suka shigo ciki, wanda suna ganinsu tafe kowa ya kama mazurun bakinshi yayi tsit kamar ba mutane a ciki.
Sai warin tusar daketa famar tashi a ciki kamar anbud'e Masai.
Inda kuma wasu daga cikinsu suka tsintsi kanku cikin d'agawa da jiji da kai, domin a tunanin anzo wajen belin su ne, su ala dole matan manya.
Sai dai a mamakinsu sai ganin suka yi Police's din sun jawo kofa sun sake gark'ame tare dasu a ciki, nan fa cikin kowa ya fara mird'awa k'ulululu... suka shiga hadiyar yawun k'arfin hali tare da sharce zufan dake famar gangaro masu a goshi.
kafin suyi yungurin aikata wani abu tini suka jiyo saukar kulki a saman jikinsu aiko nan suka mik'e tsattsaye gaba dayansu suka shiga kurma ihu suna farma junansu, gashi dakin ba fili ne da shi ba balantana su shiga zagaye-zakayenshi.
Iyakar harzuk'a Police's din sun harzuk'u domin dai ko waccensu babu alamun gajiya a tattare da ita kamar wad'anda ake k'arama tankinsu man fetur, sai jibgar k'attan banza suke kamar Allah ya aikosu, inda su kuma k'attan banzan sai famar ajujuwa suke, idan aka fadawa wannan afadawa wancen. sai da Police's din sukaga uwar bari sanan suka bawa kansu futu koshi kuwa badan sun so ba, sai dan gajiyar da suka yi wajen jibgarsu, sannan suka fita daga cikin cell din suka sake kullesu.
Ko minti biyu Police's din basu yi da fita ba, aka sake sakin wata makekiyar tusa wadda warinta gabadai sai da ya gauraye girman dakin. nan daya daga cikinsu ta ce "Billahillazi dik wanda ke sakar mana wadannan mahaukatan tusoshin masu bala'in kaifin tsiya da wari, wallahi ban yafe hakkina ba."
aiko nan kamar daman jiraye suke kowa ya bude katon bakinshi yana ce wa "shi ma bai yafe ba."
Cikin wadan'da ke sakin tusar, guda ta ce "Sai dai karku yafe wallahi! amma ba ubanda ya isa ya hanamu fitar da cuta a cikin cikakkanmu wlhy! dan ba wanda aka saka dole saiya shak'e warin, dik wanda ya ga ba zai iya jimirin warin ba, ba a hanashi debe dankwalinshi ba ya toshe kussayen hantunanshi da shi ba! dan haka, amma wlhy ba wanda ya isa ya hanani sakin abita idan na ji ta."
Nan wani sabon rikici ya sake gaurayewa a tsakaninsu, hardasu buge-buge bakunan junansu.
A harzuk'e Police's dinnan mata suka sake dawowa, wanda a wannan karon kuma dukan da suka masu ya ninka na d'azun, domin layi layi suka bi suna jibgarsu sai da suka fidda ma ko waccensu tambo a fuska sannan suka bar wajen, sai dai fa an samu canji domin a cikinsu ba wadda ta k'ara cewa ko uffa a cikinsu, inba shashshek'ar kukansu ba dake tashi a wajen.
—•«»«»•«»«»•—
2:50pm mutane ne gurguzu guda kamar wajenda ake gudanar da sallar ED, dik wanda ka kalla zakaga alamun annuri a shimfide a saman fuskarshiA b'angare guda kuma wasu hadaddin samari ne tsaye a wajen da suka yi parking din motacinsu ko wannen sanye yake da shadda orange wadda ta ji aikin bakin zare haka ma hulla da takallama baqaqe suka saka torms hadi'da baqin agogo, gaba dayansu ko mai nasu iri daya ne wanda hakan ya bada tabbacin amsar sunansu da suka yi na manyan Abokanan Ango.
Uncle mukhtar ne tsaye a tsakiyarsu, wanda yake sanye da wata jahilar shadda getzner bak'a wadda babbar rigarta ta samu fitowa kalar orange, inda cike take da aikin zare bak'i, wanda iyakar tsaruwa aikin yayi kuma ya kakkantu sannan ya ji cash, inda yake sanye da wasu hadaddin takalma orange'color masu ratsin baqi a cikinsu, haka ma hullar kanshi ita ma orange ce tare da wani tsadadden agogo baqi kwalliyar cikin shi kuma orange, wadannan kalaluwan biyu dana fada ba qaramin doboshi sukayi ba, sunyi matuqar fito da hasken fatar jikinshi da kyau.
Inda a bangaren guda kuma.......
Follow me on wattpad and vote.
YOU ARE READING
WAHALA DA GATA season2
FantasySeason 2. "Hhh ai gaskiya ne Rukayya ni wlhy kin san Allah sai yanzu na san nayi dace da sarakkuwar ta gari domin waɗancan dik sheguna ne matsiyata." "Sosai ma Hajiya! ai Aunty Balkisu kam, ta wuce kowa a cikinsu, sannan ta......" Sa...