*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*
*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
*_{Novel series}_*
*_[♠️SEASON.2♠️]_** WATTPAD @Smart_Feenert ...✔*
*_[🥀BE ~ SMART🥀]_**_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**Episode ~40*
"Shi Alhaji Muhammad din"
Cikin wani mugun firgice ya mike tsaye tare da cewa "What!!!!!! Sa'id kana da hankali kuwa? Kana cikin hayyacinka kuwa? Ka san abin kake faɗa kuwa? to tin wuri ya kamata na dakatar da kai ta hanyar shata maka layi, ka tsaya iya matsayin ka."
"Amma Alhaj........."
"Ya'isa Sa'id, dama sabida wannan zancen ne kabaro gidanka ka zo ka sameni a wajen aikina ka ɓata mani lokaci wajen sauraren wannan banzan shirmen naka? to zan maka warning na farko dana karshe karka ƙara zuwa man cikin Office da wannan banzan zancen naka, sannan ka fitar min daga Office bana son na sake bude idanuwana na ganka a nan""To shi ke nan Alhaji Mustapha! Allah ya huce zuciyarka amma yana da kyau ka zauna kayi kyakkyawan tunani a cikin wannan al'amarin zan jiraka a waj..........."
"ka fita nace ko?"
Jiki na rawa ya bar Office ɗin cikin mutuwar jiki, sai dai ya yi alwashin ba zai bar cikin asibitin ba, sai nan da 3hours idan har bai ji kiran Uncle Mustapha ba to zai haƙura da zancen ya yi mashi yanda yake so dan yana ji a jikinshi dan ya rasa yau bashi zai sa ya rasa gobe ba"
Bayan ya fita daga Office din, Uncle Almustapha ya kasa tsaye ya kasa zaune dik abin duniya ya bi ya addabe rayuwarshi, bai taba tunanin aikata wani abin da ba dai-dai ba ga wani ba, har ma ga 'yan-uwansa, ya dai san ko kadan baya son Fatima a cikin zuciyarshi, kuma yana nuna tsantsar kiyayyarshi gareta a fili sai dai ba mutumin da hankalinshi zai iya fahimtar hakan daga gareshi."
Haka dai tunanukka iri-iri suka yi ta faɗo mashi a cikin rai, sai saƙe-saƙe yake yana neman mafita wanda hakan yasa Shedan ya biyo hanya wajen wucewa ya hangoshi tsaye yana wasi-wasi! Kai tsaye ya ziyarce cikin zuciyarshi ya kara rura mashi wutar ƙiyayyar da yake yiwa Fatima ta dawo kan Mahaifinta....
Kai tsaye ya ce "Lallai gaskiyarka ne Sa'idu, tun wuri ya kamata ace na dauki wannan kwakkwaran matakin ba yanzu ba! amma ko yanzu ina ganin Lokaci bai kure mana ba."
_Nan da nan ya lalabo number Sa'idu munafuki ya danna mata Calling, inda shigar kiran kadai ke da wuya Sa'idu dake zaune a bakin wani iccen dake cikin harabar asibitin yana shan iska ya yi hanzarin daukar kiran.
Ko sallama babu Uncle Mustapha ya ce "ka sameni a Office yanzu ina jiran ka" kittt ya yanke kiran.
Sai da ya ja wani dogon numfashi na farin-cikin samun nasarar da ya yi sannan ya ce "Ba dai kai bane! dama na san zaka kira ai! ana kokarin saitaka a layi kai kuma kana kokarin kaucewa! uhumhahahaha." dariyar muguntar da tayi gaggawar kubcemashi kenan.
Ko 2mins ba a yi ba Sa'idu munafuki ya bayyana a cikin Office din Uncle Mustapha, inda kai tsaye Uncle Mustapha ya ce "Sa'id yanzu menene mafita?"
YOU ARE READING
WAHALA DA GATA season2
FantasySeason 2. "Hhh ai gaskiya ne Rukayya ni wlhy kin san Allah sai yanzu na san nayi dace da sarakkuwar ta gari domin waɗancan dik sheguna ne matsiyata." "Sosai ma Hajiya! ai Aunty Balkisu kam, ta wuce kowa a cikinsu, sannan ta......" Sa...