*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*
*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
_{Novel series}_
*_[♠️SEASON.2 ♠️]_**WATTPAD @Smart_Feenert ...✔️*
*_[🥀Be ~ Smart 🥀]_**_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_**_🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**_Episode ~ 18_*
Cikin sauri ta jefa kafarta guda a ciki tare da bisimillah kamar yanda wannan tsohuwar ta umarce ta da ta yi
Inda tana shiga kuma ta tadda kanta sama ta shiga dube-duben ko ina da ke cikin dakin.Murmushi ta yi cikin kwarewa ganin abinda Mahaifinta ya saka mata a d'akin, domin Naira ce ta sha iyo a cikin wannan mahaukacin dakin kamar kifafen cikin wani babban teku, wanda kuma tsayawa fadin haduwar wannan gyaran dakin bata lokaci ne, sai dai komai da ke cikin wannan d'akin, purple and milk colors ne idan ka cire Tv da muk'arraban tafiyarshi da suka antayo layin bak'ak'e.
Su Hajiya saudat biye kawai suke da ita, domin kusan ma ita ce ke masu jagoran shiga bedroom, k'arshen rashin kunya wadda suka gani a wajenta kuma suka tabbatar da halinta bamai kyau ba ne, sai dai fatansu kawai "Allah ya shiga tsakanin na gari da b'atacce."
'Yan matan amarya ne da sauran 'yan uwanta wadanda suka zo gidan tin karfe 2pm, suka taso cikin farin ciki su nai ma Amarya sannu da zuwa.
Bayan sun shiga d'ai daga cikin 2bedrooms d'in da ke cikin palour'n, suka zaunar da ita saman gado sannan suka juya suka yi tafiyar su tare da yi masu fatan zama lafiya, inda gidan ya rage daga ita sai 'yan uwanta da abokanan ta.
A hanzarce ta cire gyalenta ta cinnashi gefen gado sannan ta shiga kwasar dariyar k'eta.
Cikin mamaki Memu ta ce "Lafiya kike wannan 'yar banzar dariyar?."
Cike da wata mahaukacciyar dariya, Balkisu ta ce "Wai ba ku lura da kukan mahaifiyar Mukhtar ba ne halan? wlhy abin ya yi mugun bada d'anyar citta."Hansa'u ta ce "Wai shegiya daman kina nufin d'azu ba kukan gaske ba ne kike yi?"
Cikin zazzare idanuwa a waje, alamar tsoro, Balkisu ta ce "Wa? Allah ma ya isa tsakanina da ke Hansa'u, Ni me ye had'i ba da kuka kuma ina farin ciki? Yo ni rabuwa ma da mahaifiyata ban yi kuka ba, sai haduwata da waccen tsohuwar najadu? haskiya kin gama da ni Hansa! Ya ma ci ace na kwada maki biyar."
"Allah ya shiryeki Billy! wlhy ke mugunyar 'yar isaka ce fa."
Gabadayansu suka kwashe da dariya irinya mugunta.
Sauran 'yan uwanta ne dake gidan suka shigo cikin dakin da take domin yi mata sallama zasu koma gida tare da bata shawarwarinsu na tsiya dan dik wad'anda zata dinga azabtar da su Hajiya kaka ne domin su zama makami a wajenta.
Sosai ita ma ta yi amanna da shawarwarinsu har da biyarsu da godiyar iskanci tare da yi masu rakkiya har a bakin kofar fita palour.
Gidan ya rage daga ita sai abokanayenta hudu na hannun damanta.
Inda biyu suke palourn zaune a kan kujeru, suna waya da samarinsu biyu kuma na cikin bedroom tare da Amarya suna shek'e ayarsu.
Memu ta ce "Swthrt dan Allah yau karki yarda ki bari ya tsotse muna ke da yawa dik yanda za'ayi a dan rage mana ko da kadan ne."
Hansa'u ta ce "Wlhy kuwa dan kin san mu ma bayan kwana biyu zamu zo mu amshe namu a marcin......."
Follow me on wattpad and vote.
KAMU SEDANG MEMBACA
WAHALA DA GATA season2
FantasiSeason 2. "Hhh ai gaskiya ne Rukayya ni wlhy kin san Allah sai yanzu na san nayi dace da sarakkuwar ta gari domin waɗancan dik sheguna ne matsiyata." "Sosai ma Hajiya! ai Aunty Balkisu kam, ta wuce kowa a cikinsu, sannan ta......" Sa...