Episode ~ 9

286 103 0
                                    

*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
                  _{Novel series}_
           *_[♠️SEASON.2 ♠️]_*

  *WATTPAD  @Smart_Feenert  ...✔️*
            *_[🥀Be ~ Smart 🥀]_*

*_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_*

*_🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂_*
*—•«»•—•«»•—•«»•—*
          *_Episode ~ 9_*

             _Suna cikin hakan sai ga su Gwaggo Uwani rutu-tutu sun fito daga cikin dakin da shirinsu na aiki.

A nan waje suka same su Hajiya zaune suna shan iska suna labaransu cike da nishadi da su har sun manta da wancan batun.

cikin mugun jin haushi ganinsu hakan Gwaggo Uwani ta ce "Sannunku ashe kun tashi?"

A tak'aice suka amsa mata da "Eh."

A gadarance ta ce "Sai hak'uri fa! d'azu kwata-kwata mun manta da ku ne, shi yasa bamu dibar maku kayan kari ba (brackfast) sai bayan da muka gama zuba ma cikakkanmu sannan muka tuna da ku a waje, ko wadannan ma dak'yar Allah ya sa aka samu wasu daga cikinmu  sun rage, shi ne aka tattara waje guda aka kawo maku."

Cikin nuna harkar rashin damuwa  Hajiya Munira ta ce "Eyya! Allah sarki ai ba komai ba ne, mu a koshe ma muke, mun gode."

     A hasale Uwani ta ce "A koshe kuke? ban gane a koshe kuke ba? naga dai yanzu safiyar ta ida wayewa balantana ku ce kun je restore kunci a can! to Nima me ye nadamar da kaina a kanku? hakan ma daidai ne gara da bakuci ba, ai cikinku ne! ke Mariya."

ta ce "Na'am babbar aunty."

"D'auke kayan abincin can dan Allah ki je ki samu inda ake zubarwa ki zubar a bawa karnukan su cinye, shayi kuma a zubdashi cikin makwarara ya bi ruwa."

Da sauri ta ce "Anyi an gama yanzu-yanzun nan Babbar Aunty."

Sannan Uwani ta sake maida dubanta ga su Hajiya da su har sun fara sha'anin gabansu, ta ce "ina fatar dai kun shirya ma aiki yanzu ko? dan ba zama za'ayi ba."

Hajiya ta ce "Mai zai hana kuwa Uwani? ai dan shi muke zaune a nan."

Cikin bacin rai Gwaggo Uwani ta ce "Oho to kun yi k'ok'ari!, sai a samu damar tashi ko?"

Hajiya ta ce "Kin yi saurin fad'a."

    —•«»•«»•«»•—

    Abangaren su Hajiya kaka kuwa.

su ma tin jiya ba wanda ya rintsa a cikinsu, aikin ne suke ta fafutukar yi kamar wajen da ake gudanar da abincin bikin rantsar da shugaban k'asar America.

               Ba su  suka futa ba sai misalin Qarfe 11:35am sannan suka k'ark'are aikin gabadai, na sakawa cikin takeaway ansa, na sakawa cikin kwali kuma an saka an manne, wanda za'a saka a kuloli shima an zuba an kulle. abin dai gwanin birgewa.

'yan biki kuwa sai k'ara halarta suke rutu-tutu ana kwasar hada-hadar  biki, masu cika jikkuna da abinci kuwa gasunan ko wanne ya make a gefen kujera ya na kyakyatar idanuwan jama'a yana durawa ciki, masu gulma suma gefensu daban dik wadda aka ga ta wuce da k'aramin zane sai an maganta, ma hassada kuwa an kasa zaune an kasa tsaye sai safa-da-marwa suke suna cizon dan yatsa.

Haka dai kowa ke ta gudanar abinda ya dameshi.

         A bangaren Angon Kuwa shi ma shirin ne yake  har na fitar arziki shida abokananshi, ba su tsaye ba su zaune, iyakar zanzana da matsuwa ganin an daura wannan auren Uncle Mukhtar ya nuna domin shi baik'i jinin ace  har an kawo Amaryar yanzu ba, domin minti guda ganinshi yake kamar 24hours ajima-ajima ya mik'a idanuwanshi ga agogon da ke d'afe ga tsintsiyar hannunshi.

D'ai daga cikin abokanan Angon ne wanda ake kira da Muhsinu ya ce "Dillah shege ka samu ka zauna tin dazu baka da aikin yi sai gewaye-gewayen mutane sai kace wani dan sanda, komai dai zanzanar mutum  da matsuwarshi  sai andawo daga  sallar juma'a za'a daura."

Uncle Mukhtar ya ce "ba dai za'a daura dinba? ai komai ya yi daidai dan sa ido kawai! aini tin yanda naga ka tashi ka cire a gogon dake saman bango ka kai toilet na san tsiyarka ce ta tashi sai dai ka manta da bayan agogon bango bature ya yi na hannu."

Muhsin ya ce "wannan ma Idan ka matsa man saina cireshi a hannunka, sannan inyi pulorshing dinshi."

Uncle Mukhtar ya ce "wallahi ba ka isa ba, mugu kawai dan bak'inciki."

Muhsin ya ce "Na ji amma dai sai an dawo daga masallaci za'a daura komai matsuwar mutum."

Uncle Mukhtar ya ce "D'an iska koma dai ya ne yau da sabon ango za'a kirani ku kuma sai dai a kiraku da tuzuraii." aiko kamar daman jiraye suke gabadayansu suka ke ce da wata tulluk'ar dariya suna ce wa "Munji dai mu ma ai lokaci na nan zuwa shege, kuma kafin wannan lokacin dik kun tsufa kun fara ambaliyar yara."  haka dai suka yi ta firarsu cikin nishad'i mai cike da wayewa.

  B'angaren Iyaye maza, ba'a barsu a baya ba wajen nuna tsantsar farincikinsu ga wannan lalurar.

Alhaji kabiru ne shi da Alhaji Ibrahim keta dawainiyya da abokanansu wad'anda suka zo daga wasu garuguwan da kuma k'asashen duniya, sabida wannan daurin auren.

Haka dai Farinciki da annashuwa ke ta tafiya yana zagayowa a cikin wadannan iyalan.

                —•««»»•—

B'angaren su Ammie.

K'arfe 2:13pm ko ina daga cikin gidan, cike yake da mutanen biki har na fitar arziki lungu da sak'o kowanne bangare ka duba cike yake da jama'a.        

Gwaggo Uwani ce zaune a cikin wani extra palourn tare da  tawagarta suna ta famar sharholiyarsu, a zage wancan a yabe wannan, inda ta fakaice idanuwan Atika dake zaune gefe, suka yi 4eyes ta kashe mata ijjiya guda alamar a fara wasar yanzu.

Ba tare da bata lokaci ba Atika tayi zubun ta mik'e tsaye ta sha kwana, ko minti biyar bata yi ba, ta dawo, inda tana zuwa ta kashe ma Gwaggo Uwani ijjiya guda alamar aikin ya kammala.
Follow me on wattpad and vote.

WAHALA DA GATA season2 Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang