*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*
*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
_{Novel series}_
*_[♠️SEASON.2 ♠️]_**WATTPAD @Smart_Feenert ...✔️*
*_[🥀Be ~ Smart 🥀]_**_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_**_🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*_Episode ~ 6_
Ko waccensu rik'e da k'ugu ansha damarar kugu.
D'aya daga cikinsu ce wadda ta fi su rawar kai, ta farayi ma Gwaggo Uwani kirari iska, kafin ta soma tambayar abinda ke faruwa.
Ta ce "Babbar Aunty 'yar Aljanna mai saka uwar d'iya sakin babbar tusa a gaban surukinta! mai sa yaro ya manta da uwarsa komai zamanta yar babbar kazat Uba wajen nuna mashi k'auna! Hayaniyar me muke ji ana yi a cikin d'akin nan tun dazu muna waje muna jin ta tana tashi, wanne shegen ne ya tab'a mu na ke tin yanzu mu maki maganinshi a cikin dakin nan, har sai mun mantar da shi hanyar da ya biyo ta kawoshi cikin gidan nan? fada mana koma mene ne mu ne daidai da talahwahhi irinsu, mu darje bakin munafukai yanzu a wajen nan."
Gwaggo Uwani ta mik'e tsaye cikin kasaita, ta ce "ku kyalesu kawai ku biyoni waje zanyi maganar sirri da ku kun san wajennan cike yake da Aku da Akwa." Cikin nuna masu su Hajiya Munira da tsinin bakinta.
Wata tantiriyar dariya suka kwashe da ita har da su shewa, suka ce "wallahi kuwa manya-manyan k'asungumai ma" sannan suka dunguma suka rufa mata baya zuwa waje tare da Ammie da yaranta, aka bar su Hajiya zaune a yashe saman kujeru suna kallon bangon dakin. ko uffan basu ce da su ba suka kawo na mujiya suka zura masu.
Bayan su Uwani sun fita waje suka koma wani gefe na daban gabadayansu suna kuskunniya, suna kaiwa karshen tattaunawarsu suka buga wani mahaukacin ihu na jin dadin zancen har da su gud'a.
D'ai daga cikinsu ne gwaggo uwani ta kira sunanta da Atika.
Atika ta ce "na'am ranki shi dade."
ta ce "shiga daki, ki fito da sheguna waje su zo su yi abinda ya kawosu! ku kuma ku fidda masu buhuhuwan can na fulawa waje suzo suyi donut da cake da pizzas da dai sauran'su."
Zuhriyya ta ce "Gwaggo ba an kira wad'anda zasu yi ba? naga fulawar har wajen buhu ukku ce fa."
"kinci gidanku bak'ar munafuka! ina ruwanki? wato ki nuna mana su k'annen Ubanki ne ko? to su zasu yi aikin idan kuma zaki taya su sai ki shirya."
"A'aaaaa Gwaggo! me ya yi zafi haka shi ba wuta ba? Allah ya baki hak'uri, ni bara ma na tashi na ba ku waje."
"Da dai ya fi kan, shugabar munafukai wadda ta yo gadon bak'in hali ga dangin ubanta shegiya."
Ba ta ce da ita ko uffan ba ta bar wajen cikin mugun jin zafin kalaman Uwani.
Ammie in banda kallo ba abinda take binsu da shi sai dariya hak'ora, wadda ba ta kai ciki ba domin ta tsane ganin abinda zai b'atawa 'ya'yanta rai, kawai dai ta fauze ne dan ba yanda ta iya da Gwaggo Uwani, domin dik tsabar rashin mutumcin da suke tak'ama da shi a tafin hannun Gwaggo Uwani yake, dan ko rabin nata bai kai ba.
—•«»•—
Ta b'angaren su Oga Hajiya Kaka kuwa, su ma aikin ne ake ta famar yi afujajun, inda aka raba aikin gida biyu, Aunty Zahra'u matar Uncle Uzaifa da Anti Asma'u matar Uncle mustapha da Aisha suna bangaren Hajiya khadija suna gudanar da na su, haka ita ma Hajiya Saudat tana can tare da tawagar ta suna gudanar da na su.
Ita ma Aunty Zilfa'u d'iyar Hajiya Khadija, ba a barta a baya ba wajen nuna tsantsar tsagwaron farin cikinta ga wannan lalurar, tin ana sauran kwana biyu biki mijinta Ya aminta da zuwanta gida da sunan sai bayan biki zata koma, sai yaranta su biyu twins wadanda kusan shekarunsu zasu kai daya dana fatima (Iman da Aimana).
Haka dai kowa yake ta gudanar da na shi aikin, inda Aunty Zilfa'u da Aunty Rukayya da Hajiya saudat su kadai keta famar aikace-aikacensu a nasu bangaren, dan ita Oga Hajiya kaka ta riga da ta sadaukar masu da shi gabadai domin dai ba wani abin kirki da take barkatawa a nan sai dai bak'in bala'i da masifa da take bin yara da shi, a cewarta kowa ya ji a jikinshi.
—•«»•—
Gefen su Ammie kuwa, kowa ya gama aikinsa har yayi wanka ya canza tufafin sawarshi, sun komo palourn sun zauna sai firarsu suke zubawa ta ban haushi mai cike da zallar habaitayya masu gunar rai, wad'anda kuma ba kowa ake ma su ba illa su Hajiya Munira dake waje tin dazu basu tsaye basu zaune sunata bulek'en aiki, har shabiyun dare tayi basu ida qarqarewa ba.
Sai misalin 1:20am na dare suka samu suka k'ark'are aikin da k'yar da walahaula, sannan su ma suka je suka watso ruwa su kayi shirin bawa Oga barawo hakkinsa cikin gajiya mai dauke da mutuwar jiki.
Har zasu kurd&e dakin da aka ware masu su kwanta, suka jiyo muryar Gwaggo Uwani cikin isa da tak'ama take fadin "Hmmm su Hajjaju kenan sarkin mulki, ai da kunyi saurin bawa kanku hak'uri kun fasa ida shiga cikin dakin tin kafin a shiga a tadoku, domin wallahi ba wanda ya isa ya kwanta daki yau da sunan baccin jin dad'i, dan ba zaiyu a shalle wajen baccin jin dadi sanyi AC na dukan mutum a daki, a tashi gobe a makare aikin komai ba a barkata ba, dan haka a samu damar antayawa waje saman tabarmi a kwanta dan ba baccin jin dadi ya kawomu a gidan ba! ke Balkisu."
ta ce "Na'am Gwaggo."
"Tashi maza ku je ku dauko mana tabarmi ku shimfida mana a waje a nan kowa zai kwanta."
cikin gungunin k'uiya Balkisu ta miqe tsaye taja su Nadiya suka wuce su dauko tabarmin.
Su Hajiya Munira kuma tsaye kawai suke suna kallon ikon Allah tare da mamakin wannan dayen wulak'anci da aketa famar nuna masu dan anga ba su damu ba.
Atika tace "wlhy Babbar Aunty hakan da kika yi shi ne daidai Idan mutum ba zai iya kwanciya a saman tabarma ba to saidai ya kwana tsaye ko zaune."
gabad'ayansu suka kwashe da dariya har dasu tafawa.
Sosai Hajiya Munira ta fahimta da sabida su ne aka tsara wannan bakin munafurci na baccin a waje, suka ja bakinsu suka yi mueee sannan suka kawo na mujiya suka saka masu, dan tin lokacinda suka zo gidan suka ga dik take-takensu bai wuce na neman jidali a wajensu ba, suka dauke idonsu a garesu.
Ammie ta ce ma "Nadiya ta je daki ta dauko masu zannuwan gado a shimfida a saman ta barmarmin."
Gwaggo uwani ta yi saurin katseta da ce wa "a'a kar a dauko, dik wanda ke buk'atar jin taushi a saman wajen da zai gincira kafadunshi, ya cire zanen dake jikinshi ya shimfida."
Gabadayansu 'yan tawagarta suka ce "wallahi kuwa! Ehehheyyyy." dariyar 'yan tasha kenan ita ce wadda 'yan uwan Ammie suka barke da ita.
Yanda ta ce d'in hakan ne ya kasance domin a cikinsu ba wani wanda ya iya shimfida wani abu a saman tabarmar haka nan kowa ya kwanta, harda su Hajiya Munira domin ita ma abin ba k'aramin bak'anta mata rai yayi ba shiyasa ta fauze ita da yaranta suka yi kwancinyarsu haka nan saman tabarmin ba dan ransu ya so ba.
_Qarfe 4:30am Lokacin an fara kiraye-kirayen sallar Asuba, Hajiya Munira ta falka daga nannauyan baccin da ya yi mata tuzuruwar sata sabida sanyin da take ji yana ratsa cikin k'assan jikinta, sai dai ta yi mamaki sosai rashin ganin kowa a wajen da ba ta yi ba cikin 'yan uwan Ammie, ita kadai ce sai d'iyanta a yashe a saman wata guntuwar tabarma.
Follow me on wattpad and vote.
YOU ARE READING
WAHALA DA GATA season2
FantasySeason 2. "Hhh ai gaskiya ne Rukayya ni wlhy kin san Allah sai yanzu na san nayi dace da sarakkuwar ta gari domin waɗancan dik sheguna ne matsiyata." "Sosai ma Hajiya! ai Aunty Balkisu kam, ta wuce kowa a cikinsu, sannan ta......" Sa...