Episode ~39

118 45 0
                                    

*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
*_{Novel series}_*
*_[♠️SEASON.2♠️]_*

* WATTPAD @Smart_Feenert ...✔*
*_[🥀BE ~ SMART🥀]_*

*_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂*

*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*Episode ~39*

--------

Bayan wasu 'yan watanni.

Sa'Idu munafuki ne mai mashin ya sauke a dai-dai asibitinsu Alhaji Kabiru.
Inda a hanzarce ya ciro ₦200 Ko canji babu ya mikawa mai mashin din ya kamo hanyar shiga cikin asibitin.

Tafiya yake kamar wanda zai tashi sama, irin wadda bai san a yanda yake yin ta ba,

Sai Allah-Allah yake ga cin ma office din Uncle Mustapha "dan ganin yake kamar ɓace mashi zaiyi"

Da kyar ya samu ya kawo daf da kofar shiga office din, ba tare da ya tsaya an bashi izinin shiga ciki ba ya fada cikin hanzari.

Ba tare da ya tsaya yin sallama ba, ya ce "Alhaji Mustapha kaji abinda ke shirin faruwa kuwa?"

Cikin mugun mamaki kamar daga sama ya jiyo wannan muryar, ya ce "Sa'idu! lafiya kuwa? Lafiya naga kashigoman cikin office a firgice ko sallama babu? ko cikin diyanka ne ba lafiya?" a jajjere ya yi mashi wadannan tambayoyin tare da tsareshi da wani kallon cikin yanayi na bidar karin bayani.

"To ba gwanda haka ba Alhaji? wlhy gwanda ace cikin diyana ne guda ya zama babu bisa ga wannan mugun abin da naji labarin yana bidar afkuwa."

Cikin shan kamshi Uncle Mustapha ya ce "kamar na me kuwa?"

Sai da yadan numfasa cikin wani salo na cikakken tantirin munafuki sannan ya ce "Wata magana na ji ga shanun-tallah suna bararawa! wai ƙanenka Muhammad zai koma k'asan London da zama bayan tiƙa-tiƙan gidajen main fetur da yake ginawa yanzu wajen guda takwas, ga company's din da gareshi na abubuwa iri daban-daban sun kai wajen guda goma shabiyar."

"Uhum Sa'idu kenan" Uncle Mustapha ya ce cikin murmushi.

Sa'idu munafuki, ya ce "To gaskiya ni a ganina idan har ka kuskura kayi wasa da wannan damar taka, wlhy zaka zo daga baya kayi nadamar abin."

"Dakata dan Allah Sa'idu, me kake nufi ne nifa haryanzu ban fahimce inda labarin ka ya dosa ba! Kuma dik waɗannan maganganun da kake meye ne a cikinsu wanda ban sani?"

"Toww! iko sai rabbul-izzati, yanzu kai wanne mataki kayi kokarin dauka dan ganin ka kauda yiyuwar wannan al'amarin?"

Wani wawan murmushi ne ya yi gaggawar kubcema Uncle Mustapha, ya ce "Ni miye nawa a ciki Sa'idu? in banda addu'ar Allah ya kara dafa mashi?"

"Aa gaskiya Alhaji Mustapha da sake a cikin wannan lamarin, ka daiyi tunani da kyau."

"Uhum Sa'idu kenan, nifa har yanzu na kasata fahimtar abinda kake son fahimtar da ni."

"Anzo gurin Alhaji Mustapha! ni abin da nake son ka fahimta a nan, shi ne, kayi duba da yanda kuke da tazarar shekara har biyu a tsaninku! Kai ka bashi ba shi ya baka ba amma a wajen dukiya fa? dik da kai ma kana da taka amma ko da hakanan kai ma kana bukatar ƙari!."

"Bangane ba!"

"Kwantar da Hankalinka Alhaji, yanzu zan fahimtar da kai komai! amma tambayata biyu a gareka, shin baka bukatar ƙarin dukiyar ne? Ko kuma baka buƙatar ƙarin ɗaukaka? Kamar yanda masu iya magana ke cewa "ko kana da kyau ka ƙara da wanka"

"Sa'idu kenan ai wannan shi ne burin ko wanne irin mutum a duniya! Amma yanzu me nene shawara?"

"Da kyau haka nake son ji Alhaji, Shawarar ita ce da ace wani mutum ya mallaki dik irin wannan tarin dukiyar mai yawa haka ai ya kamata ace kai ka mallake ta."

"Me kake nufi?"

"Hmm Alhaji kenan! maganar tana da kauri wajen faɗa amma idan kayi kakkyawan nazari da tunani akanta, sai kaga ita ba komai bace face cikar buri!"

"Ina saurarenka"

"To abinda nake nufi shi ne! mai zai hana mu kawar da shi daga doron duniyar nan? dan ganin komai ya dawo a hannunka."

"Shi wa Sa'id?"

Saida ya dan sake wani uban murmushi mai cike da mugunta sannan yace shi..........
Follow me on wattpad and vote.

WAHALA DA GATA season2 Where stories live. Discover now