Episode ~27

189 96 0
                                    

*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
*_{Novel series}_*
*_[♠️SEASON.2♠️]_*

* WATTPAD @Smart_Feenert ...✔*
*_[🥀BE ~ SMART🥀]_*

*_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*🍂بسم الله الرحمن الرحيم🍂*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*_Episode ~27_*

Cikin baccinta na Jin daɗi ta ji alamar wani abu nai mata yawo a cikin zane.

Sai dai dik da haka, ta share, a tunaninta dik cikin mafalkin ne.

Wasa-wasa abin ya fara yawa dan har ya fara wuce gona da irinta, wanda sai can ta fara jin ana gurgurar cinyarta.

Cikin zafin nama ta danƙe wajen da take jin alamun tafiyar shi a saman jikinta, wanda sai da ta rikashi ne ta tabbatar da ba mafarki ne take ba, sannan ta bude idonta.

Ganin wani zumdumemen abu rike a hannunta kuma a cikin zanenta ya saka ta zabura da ƙarfi tare da buga wani mahaukacin ihu tana fadin "Yau ta shiga ukku, maciji a cikin zanenta."

A firgice ya tashi daga nannauyan baccin da ya saceshi, jin ihun mahaifiyarshi kamar a mafalki, ya ce "Innadillahi Hajiya lafiya?"

"Mukhtar maciji."

"Maciji a ina Hajiya.?"

A ɗimauce tace "A cikin zanena sai sarata yake, wayyo ni na karb'e ukkuna a hannu." ta fadi kasa kwance sumammiya.

Balkisu da ke laɓe a bakin kofa tana saurarensu, sai kwasar dariyarta take ta mugunta
Inda a rikice kuma Uncle Mukhtar ya fito daga cikin dakin yana famar kiran sunan Balkisu, wanda ita tinda ta ga ya nufato hanyar fita, tayi saurin shigewa store.

"Aunty Balkisu.....Aunty Balkisu... Aunty Balkisu.....' kina ina dan Allah, ki kawo ruwa yanzu Hajiya ce ba lafiya."

Cikin masifa ta ce "Wai lafiya ake ta kwalaman wannan uban kiran haka? sai kace wadda ta ciyo bashi buhun shimkafa har lokaci ya yi bata biya ba, meye ne da baƙin wulakancin tsiya?"

A rauna ne ya ce "Dan Allah, dan Annabi Aunty kiyi hakuri wlhy Hajiya ce ta fad'i kas......" kafin ya ida ta ce "To sai aka yi me dan ta suma? wato sabida tsabar rashin mutumci har ni zanje na d'ibo ruwa na kawo a watsa mata dan wulakanci, wlhy idan har sai na kawo ruwan zata tashi saidai ta mutu a nan, ni ina ruwana? ai ba gareta aka fara mutuwa ba balantana suma! to ba zan kawo d'in ba" Haka dai tayi ta zabga mai baƙin jidali kamar uwar da ta haifeshi..

Inda shi kuma sai famar hakuri yake bata kamar almajirin da ya kashe tulun malaminsu a bisa kuskure...

*****

A bangarensu Ammie kuwa da kyar da wala'haula ta samu damar kwakwalo murmushin karfin hali, ta shiga yi ma wannan police din sannu da zuwa tare da bata damar zama a saman kujerun da ke dakin.

A takaice wannan police ta ce mata "Ai ba zama ya kawoni ba Hajiya, marar lafiyar nazo na duba halin da take ciki, ina son a yi man iso a wajenta na dubota idan ba damuwa."

Hantar Gwaggo Uwani ce ta kad'a, inda ita kuma Ammie cikin ta ya shiga tsuwa "kulululuuuu" nan sai ga zufa ta soma karyo masu dik da sanyin AC dake dukansu, kun san dama an ce "marar gaskiya ko a cikin teku ya fada sai ya yi zufa." da hanzari suka kalle junansu inda daga bisani kuma suka maida dubansu ga wannan police din, wadda gabadai ta gama karantar yanayin da suke ciki.

Cikin inda1inda Ammie ta soma yi mata bayani...
Follow me on wattpad and vote.

WAHALA DA GATA season2 Where stories live. Discover now