*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*
*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
*_{Novel series}_*
*_[♠️SEASON.2♠️]_** WATTPAD @Smart_Feenert ...✔*
*_[🥀BE ~ SMART🥀]_**_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**Episode ~42*
Daddy da Mummy kamar kauyawa suka zama wajen kallon wannan tsararren gida.
Gyaran muryar Ahmed ne da suka ji ya dawo da hankalinsu wajen.
Ya ce "Muhammad kuyi hakuri da wannan karamin gidan kuma kar kuji tsoron zama a cikinsa ko kadan, domin wannan gidan mallakinka ne kai da iyalanka, na san zaka yi mamakin yanda aka yi wannan gidan amma karka samu damuwa mu ida karasawa daga ciki dik zan maku bayanin komai."
Har a wannan lokacin Daddy bai samu bakin yin magana ba! sake kawai yake da baki galalalaaa yana kallon lungu da sakon dake cikin gidan kamar wani tsohon bakauye, haka ma Mummy ba a barta a baya ba wajen bada tata gudunmawar kamar dai irinta Daddy.Tsayawar da suka ga Ahmed yayi ne a dai-dai bakin wata babbar kofa, ya ankarar da su wajen fahimtar a bakin kofar shiga cikin main palourn ne suke.
Inda ko 10seconds basu yi da tsayuwar ba, saiga kofar ta bude kai tsaye ba tare da an saka hannu an budeta ba."Wa'izu billah wani makeken parlour ne suka ci karo dashi sai kace a katsar waje ko a kasar wajen ma sai wane da wane ne, kadai suka isa su iya mallakar irinsa, iya haduwa palour'n ya kai dik inda yake kai, komai a tsare yake abin gwanin burgewa.
Bayan sun shiga ciki, Ahmed ya shiga zagayawa da su a cikin gidan.
Ko ina sai da suka leƙa, da yake gidan wajen hawa uuku ne, penthouse.Inda a hawa na biyu suka cin ma su Zinatu ciki wani hadadden daki kwance a saman wani makeken gado sunata tantatsa baccinsu cikin kwanciyar hankali da walwala, haka ma kayan da suka zo da su ko wanne sunganshi a mazaunin da ya dace da shi, Abin dai gwanin burgewa Masha Allah👌🏻.
Bayan sun gama dube-duben ko ina suka dawo parlour'n kasa suka zauna saman kujerun dake kallon wani makeken Tv wanda yafi kama da Majigi "saidai bashi ba ne" kai tsaye suka ga Ahmed ya daga hannunshi sama wani abu kamar walkiya ya fito daga cikin tafin hannunshi ya baltsa wannan kyalkyalin a saman Tv
Nan take Tv ya fara aiki inda suka ga yaran Oga bakin get din gidansu suna ƙoƙarin fidda wasu manya-manyan galaluwan main fetur a cikin motar'su cikin tako mai hade da takatsantsan.
Nan Uncle Muhammad, ya nasa a cikin ranshi da cewa kenan har lokacin ya yi, kai tsaye yaga agogo ya bayyana a saman tv ya ga 12:55am.
Cikin mugun mamaki ya juyo ya kalle Ahmed cike da tunanin yanda aka yi har ya san abinda ke cikin ransa.
Kai tsaye ya ga ya sakar mashi murmushi tare da nuna mashi ya kalle tv'n dawutsiyar ijjiyarsa guda.
Ko da ya maida hankalinshi ga Tv ya ga har sun gama jajjera galaluwan bakin gefen ginar gidan wajen guda 30 cikin tashin hankali Mummy kalle Daddy taga shi ma ita yake kallo.
Nan suka sake maida hankalinsu ga tv suka ga sun fidda wata kwaranga (Ladder) sun aza saman ginar gidan kai tsaye wani ya hau samanta sai da ya kai saman ginar wani shi ma ya hau sama bayan sun kai ga zama saman ginar daf sannan wadanda ke kasa suka taimaka masu wajen cira kwarangar sama suka samu nasarar saukar da ita cikin gidan.
YOU ARE READING
WAHALA DA GATA season2
FantasySeason 2. "Hhh ai gaskiya ne Rukayya ni wlhy kin san Allah sai yanzu na san nayi dace da sarakkuwar ta gari domin waɗancan dik sheguna ne matsiyata." "Sosai ma Hajiya! ai Aunty Balkisu kam, ta wuce kowa a cikinsu, sannan ta......" Sa...