*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*
*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
*_{Novel series}_*
*_[♠️SEASON.2♠️]_** WATTPAD @Smart_Feenert ...✔*
*_[🥀BE ~ SMART🥀]_**_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**Episode ~43*
Cikin mugun tashin hankali Mummy ta taso tayo wajenshi tana jijjigashi cikin matsanancin kuka take kiran sunanshi.
Sosai shi ma Ahmed abin ya yi bala'in ba shi tausayi, a hanzarce ya taso ya yo wajen Daddy ya gyara mashi kwanciyar shi tare da dafa goshinshi na tsawon minti2 sannan ya ce ma Mummy ta kwantar da hankalinta lafiya kalau Daddy yake yanzu ya dan samu baccine zai fi abarshi ya dan futu na tsawon wani dan karamin lokaci, a sannan taji hankalinta ya dan kwanta, daga bisani kuma Ahmed ya yi sallama da ita akan zai wuce sai ya sake dawowa, godiya mai tarin yawa Mummy tayi ma shi, ya b'ace daganan.
~~~~~
A bangaren wajen su Alhaji Kabiru kuwa, safiya na wayewa aka dawo da gawawwakinsu gida.
Inda labarin mutuwarsu gabadai ya gauraye ko ina ba wanda baiyi bakin cikin rasuwarsu ba! banda kyakkyawar addu'a da kyayyawan fata ba abinda mutane ke binsu da su.Iyalansu gabadai sun shiga cikin wani mawuyacin yanayi abin gwanin ban tausayi.
Haka ma Uncle Mustapha ya yi nadamar abin da ya aikata ma kanenshi na kunar da ya sa akayi masu.
Sabida gashi ta sanadiyyar mugunyar shawarar da Sa'idu Munafuki ya bashi ta janyo sanadiyyar mutuwar iyayensu, haka dai ya yi ta tunaninsa barkatai marar amfani kuma marar kan gado, farin cikin'sa guda shi ne gabadai dukiyar iyayensu zata dawo a hannunshi.
2:00pm aka yi jana'izar su Alhaji Kabiru, Sabida sai da aka tsaya jiran ƴan'uwa da ke nesa suka zo sannan aka yi tare da su.
Bayan an gama aka yi masu rakkiya izuwa makwancinsu na gaskiya.
^^^^^
Bayan kwana40 da rasuwar su Alhaji Kabiru, yan uwansu na nesa dana kusa tare da abokanan arziki aka taru akayi addu'ar 40 sannan kowa ya watse.
Cikin Iyalansu kuwa kowa ya dauki dangana ya daurawa kansa, kwatsam saiga Uncle Mustapha ya bijiro da maganar karbar gadon fatima, tare dana diyan Uncle Uzaifa wanda hakan ya sa Zahra'u Matar Uncle Uzaifa ta bukace da a danka mata na 'ya'yanta a hannunta domin taga harkar kamar akwai zalinci a cikinta.
*_Bayan kwana biyu_*
Wasu manya-manyan Malamai suka hallara a cikin wani makeken palourn dake cikin gidan margayi Alhaji Kabiru, tare da dik wani Ɗa dake da gadon Mahaifinsa "wato bangaren Alhaji Ibrahim tare da bangaren Alhaji Kabiru.
Ɗai daga cikin Malaman ne guda ya fara bude taron da addu'a bayan kowa ya shafa ne aka shiga rabon gado.
Inda aka raba dukiyar su Alhaji'Kabiru gida biyu aka bawa yaran Alhaji'Ibarahim kashi guda yaran Alhaji Kabiru kashi guda.
YOU ARE READING
WAHALA DA GATA season2
FantasySeason 2. "Hhh ai gaskiya ne Rukayya ni wlhy kin san Allah sai yanzu na san nayi dace da sarakkuwar ta gari domin waɗancan dik sheguna ne matsiyata." "Sosai ma Hajiya! ai Aunty Balkisu kam, ta wuce kowa a cikinsu, sannan ta......" Sa...