Episode ~24

255 97 0
                                    

*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
_{Novel series}_
*_[♠️SEASON.2♠️]_*

* WATTPAD @Smart_Feenert ...✔️*
*_[🥀Be ~ Smart 🥀]_*

*_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_*

*_🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*_Episode ~24_*

Nan take komai nata ya sauya izuwa wata halitta mai ban tsoro da ban firgici, inda cikin wata ƙaƙƙaurar murya marar daɗin ji, ta fara kiran sunan Koka Mintsinkyu, har wajen sau ukku kafin ta sake ta hud'u, tini ta tsintsi kanta tsunbulbul a cikin fadar shi tsaye a gaban shi.

Da wata mahaukacciyar dariya ya fara tarbarta da ita, inda da daga bisani kuma ya turmiƙe fuskar nan mai kama da kashin jaki, ya soma yi mata magana cikin wata murya mai kama da ta mutane bila'adadin, a taƙaice ya ce, "I...na...jin......ki"

_Ba tare da ɓata lokaci ba ta shiga kora mashi bayani, ta yanda take son a tafiyar mata da rayuwar Uncle Mukhtar, ya zama tamkar bawa a wajenta. ta zamar mashi tamkar dafin maciji a cikin rayuwar shi., maganganunta su zama tamkar tafasasshen ruwan zafi a cikin kunnen shi, sai a binda ta ce ya yi sannan zaiyi ko yana so ko baya so ya zama dole ne a gare shi, kafin ta kai ga ƙarƙare maganganun nata gabadai, kamar ance ta buɗe tafin hannunta, ta ji faɗowar wata ƙaramar kwalba a saman shi.

kan ta yi wani yunƙirin yin wata maganar, ta ji Boka Mintsinkyu ya soma yi mata bayani da irin muryar dazu yana ce mata "ta haɗa wannan turaren da fitsarinta waje guda, sannan ta gauraye su tare sai ta fesa shi ta ko ina dake cikin dakinta bayan ta ƙarƙare gaba dai ta ajiye kwalbar a bakin kofar shiga toilet." Yana gama fadin haka komai ya ɓace mata, ta tsintsi kanta tsaye a cikin dakinta a wajen da take dazu, ta sake wata irin mahaukacciyar dariya marar dadin ji wadda sautinta kadai ya isa ya firgitar da masu karatun wannan page, sannan ta kama hanyarta ta aiwatar da bak'ar aniyarta. ta shiga bathroom ta yi fitsari, bayan ta gama, ta haɗeshi da turaren da boka ya bata waje guda ta gaurayesu, sannan ta shiga fesa ma dakin ta koo ina lungu da saƙo.

Bayan komai ya kammala gabad'ai sannan ta je ta ajiye kwalbar a daidai inda Boka ya ce ta ajeyeta idan ta gama, wanda ko 1second ba ayi ba wannan kwalbar ta bace.

_Cikin wani irin mugun farin ciki da take jin dik duniya ba wanda ya fita sa'a da nasarar samun Boka Mintsinkyu, ta sake sakin wata mugunyar dariya irin ta ɗazu saidai ta wannan karon ko kisa zata iya yi domin zuciyar mutum na iya bugawa akan bala'in kaifin tsiyarta kamar raiza.
A hanzarce ta cire wannan rigar daga jikinta, a daidai lokacin kuma komai nata ya dawo daidai, idanuwanta da jikin da komai ya dawo yanda yake, sannan ta nadiye rigar ta maidata inda ta ɗauko ta tare da ƙara yi mata tanadi na musamman, sannan ta maida kayan dake jikinta wad'anda ta ɗebe dazu ta haye saman gado ta zauna, zuciyarta cike da farin ciki marar misiltuwa, lokaci guda kuma tasha omo ta ce

"Hmm! Mukhtar taka ta k'are Yau! ba dai ka ce da ni zaka ja ba? Aiko zaka tsintsi talatarka a laraba! sanadiyyar bak'ar zuciyarka ya sa na ɗauki kwakkwarar mataki a kanka yau dik da banyi niyar yin hakan ba, amma ka tilastani, ka nuna tsanar gareni tsagwaronta a fili, ka sa ranar farin ciki ta zame muna tamkar ranar baƙin ciki! Kai ne sanadiyyar wannan ƙwaƙƙwaran matakin da na d'auka yanzu, domin alamar da ka nuna a kwai shaƙiyanci make a cikin kwanyar kan nan naka mai cike da taurin kan tsiya! Gaskiya na tausaya maka matuk'a, domin wannan matakin da ka d'auka ba zai yi wani amfani ba a yanzu! Ka yi asarar lokacinka tare da wargajewar lissafi dan da ka sani yau baka fita wajen sallar subahin ba, domin dik lokacin da nayi yunƙirin tashi na fara aiki na sai na ganka a falke, dan dole na koma kwanciya ta! hhhhhhh. ka yiwa kanka dan daga yau taka ta ƙare, wlhy saidai wani amma ba kai ba ko wanin ma nafi ƙarfinshi Koda a kwai shi kuwa a cikin faɗin duniyar nan wlhy nayi alƙawarin sai naga bayan shi koma wanene! hahahaaaa dani kake zancen." ta ƙara gyara kwanciyar ta cikin jin daɗi da annashuwa ta koma bacci.

*—•••«»•••—*

Zaune yake a cikin masallaci ya na lazimi, amma zuciyar shi sai wasi-wasi take mai akan al'amarin duniya, ya rasa a binda ke mashi daɗi tun a wannan lokacin, Jin kanshi yake wani iri kamar ba shi ba, har aka kai ga tada sallar asuba bai daina jin ƙunar da zuciyar shi ke mashi ba.

Bayan sun gama sallar, a gaggauce ya taso ya fito daga cikin masallaci ya nufato hanyar komawa gidan zuciyarshi cike da zullumin abinda ya sha mashi kai..

Ko 3mins ba ayi ba daga fitar shi cikin masallacin ya ji alamun jiri na son rafkeshi ƙasa, ya dinga ƙwiƙwita wa, wajen ci gaba da tafiyarshi cikin ƙarfin hali da rashin kuzari, inda yana cikin tafiyar ne kai tsaye ya ji kanshi ya kauri wani ƙaƙƙarfan abu kamar dutse sai da ya duƙe ƙasa, inda kafin ya yi wani yunk'urin tashi tsaye ya ga koma mene ne, ya ji wani abu kamar mashi yabi ta tsakkiyar kwanyar kanshi ya wuce, nan take ya faɗi ƙasa kwance, tun daga nan bai sake sanin inda kanshi yake ba........
Follow me on wattpad and vote.

WAHALA DA GATA season2 Where stories live. Discover now