Episode ~32

147 92 0
                                    

*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
*_{Novel series}_*
*_[♠️SEASON.2♠️]_*

* WATTPAD @Smart_Feenert ...✔*
*_[🥀BE ~ SMART🥀]_*

*_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*_Episode ~32_*

Bayan sun isa Police-Station, aka yi rubuce-rubucen da za'ayi aka bada belinsu Hajiya Munira ita da yaranta.

Kasancewar sun baro kayansu gidan Alhaji Usman, yasa DPO ya had'asu da Police mata guda biyu su rakasu su dauko kayansu, sabida gudun kar wata matsala ta sake afkuwa.

Tare suka dawo da Gwaggo Uwani da sai wata fankama take a cikin motar 'yan sanda tun da taga su Hajiya Munira dan ta nuna masu ce wa "Ita mai galihu ce a wajen."

Suna isa gidan suka yi parking daga wajen get! sannan suka ida karasawa ciki tare da Police din.

Ammie na ganin su Hajiya Munira ta taso cikin munafurci ta nai masu sannu kamar wadda aka ce ma "sun fito daga gidan maza ne" inda cikin siyasar makirci ta dinga nuna harkar damuwarta akansu dande su zauna ta samu damar kara afka masu wani makircin da yafi wannan.

Su kuma dik sun riga sun fahimta da komai shi ya sa dik abinda ta ce "sai dai su jefeta da murmushi mai wuyar fassarawa." wanda da taga uwar bari taga da gaske tafiya zasu yi kuma ba zata so hakan da wuri ba! ta ce masu "Gashi kuma zaku tafi ko Alhaji baku hadu da shi ba."

Cikin kawaici Hajiya Munira ta ce "Ai babu komai wlhy idan de ya dawo a gaishe mana da shi." a daidai lokacin da suke kokarin fitowa daga cikin palour'n.

A hanzarce Ammie ta yi yunkurin biyosu waje dan ganin take wannan ita ce dama ta karshe dake son kubce mata ta hanyar wulakantar dasu Hajiya Munira, Gwaggo Uwani dake tsaye a bakin kofar da ta gama fahimtar komai, da yake ita ma makirar karshe ce, tayi hanzarin dakatar da Ammie ta ce "Ki barsu kawai, ai zasu sake dawowa nan gaba kuma Makircin da zamu sake hada masu sai yafi wannan da muka masu muni! Uhum-Uhum" ta yi murmushin mugunta wanda ya yi gaggawar zuwo mata cikin yanayi mai kama da na daukar fansa, ta ce "wallahi sai sun gane kurensu."

*****

*WA CECE GWAGGO'UWANI?*

Gwaggo Uwani diya ce ga mahaifiyar wadda ta haifi Ammie wato kakar Ammie Hajaru, Amma suna kiranta da Hajara, tin Gwaggo-Uwani bata zo duniya ba Allah yayi wa mahaifinsu Malam Isma'ila rasuwa ba tare da wani ciwo ba ko kuma jinya, kawai dai lokacinsa ne ya yi kuma ba wanda ya'isa ya wuce lokacinsa.

Malam Isma'il ba wani babban attajiri ba ne, amma yana da rufin assirinsa daidai gwargwado.

LYana da Mata guda Hajara inda Shekararsu biyu da Aure Allah ya azurtasu da samun karuwar diya Macce wato Suwaiba mahaifiyar Ammie, ita kadai Allah ya basu a wannan lokacin kuma basu tada hankalinsu akan hakan ba domin sun san komai mukaddari ne daga Allah! Kuma hakan bai sa sunyi wasa ta tarbiyar Suwaiba ba ta hanyar shagwabar da ita wajen yi mata dik abinda takeso wanda ba daidai ba, inda ya sakata makarantar Arbic data boko

A arbic school tayi wajen sauka 3 ta alkur'ani sannan ta san wasu hadissai da littattafan addini, Haka ma a makarantar boko tana da kokarinta iya gwargwado iko, tana yar shekara 13, ta gama Jenior Level sannan ta shiga Senior Level
_Tana da 16years ta gama Secondary School, a lokacin har an tsayar mata da miji aka yi mata aure, Shekararta3 da aure Allah ya azurtata da samun ciki, Hakama Mahaifiyarta Hajara har sunde'be rai da tsammanin samun wani cikin Allah ya nuna masu ikonsa.

_Ko da cikakkansu suka kai wata7 dik Malam Isma'il ya rasu, Haka suka yi ta jimamin mutuwarsa tare da laukayin cikakkansu har Allah ya saukesu Laifiya, Inda Suwaiba ta haife santaleliyar diyarta mace, Bayan kwana biyu ita ma Hajara ta haifo tata ita ma Macce, sai na dai cikin radadin haihuwar Allah ya amshe abarshi, diyar ce kadai Allah ya kaddara da zata tafo da rai........
Follow me on wattpad and vote.

WAHALA DA GATA season2 Where stories live. Discover now