*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*
*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
*_{Novel series}_*
*_[♠️SEASON.2♠️]_** WATTPAD @Smart_Feenert ...✔*
*_[🥀BE ~ SMART🥀]_**_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**_Episode ~33_*
Suwaiba ta dauke yarinyar ta hadesu da diyarta ta rike, tare da gudunmawar mijinta.
ranar sunan aka yi shi tare, inda diyar Suwaiba ta ci sunanta da Zainab, wato Ammie, diyar mahaifiyar Suwaiba, Hajara taci sunanta da sunan mahaifiyarsu Hajara shi ya sa suke kiranta da Uwani.
Haka dai rayuwa tayi ta juyawa da dadi da babu dadin, har suka girma suka kai munzilin karatu, inda suka yi karatunsu daidai gawargwado, suna gama Secondary School shekara17 akayi masu aure, Inda Ammie ta aure Alhaji Usman, Gwaggo Uwani kuma ta aure wani Malamin Islamiyyarsu mai suna Yusuf,_
Shekarar'su Hudu da aure Ammie ta Haife Balkisu, inda ita kuma Gwaggo Uwani wani iftila'i ya afkawa mai gidanta a hanyarshi ta dawowa daga wajen aiki yana saman machine dinshi Suzuki! cikin motocin dangote na siminti guda tabi ta kanshi Allah ya amshi anbinsa, sati guda da mutuwar mijinta sai auntynta Suwaiba, wato mahaifiyar Ammie ita kuma ciwon ciki tsakar dare ya zama sanadiyyar ajalinta.
Tashin hankali ba irin wanda basu shiga ba a wannan ranar, musamman ma Gwaggo Uwani dake cikin jimamin mutuwar mijinta.
Haka dai rayuwa ta ci gaba da tafiya 'yan uwansu dik suka juya masu baya 'yan kalilan ne kadai ke tare dasu.
Bayan shekara biyu Gwaggo'Uwani ta sake samun wani mijin mai suna Abdul Kadir, dan Siyasa, gaba da baya, kuma gashi hamshakin mai kudi ku san zance kudinshi sun ninka na Alhaji Mangal.
Cikin dan kankanen lokaci aka yi aurensu suka tare a Abuja da yake a can yake da gurin zama shida 'yan uwansa.
Yana da kanwa guda Atika sai mahaifiyarshi Lubabatu! kasancewar mahaifinsa ya dade da rasuwa sai kuma sauran 'yan uwansa wadanda ke zaune tare da su.
Atika ce ke zama wajenta tana debe mata kewar mijin, idan bayanan sabida sauran 'yan'uwan mijin dik sun tsaneta bata da ikon shiga cikin gidansu mijin ta gaishesu! tana shiga zasu rufeta da bakaken maganganu shi yasa take zamanta bangarenta sai idan da lurar bikin aure ko kuma na suna take dan regawa jin kadan kuma ta dawo kofarta.
Kiyayyar ta samo asali ne tin lokacin da aka so hadashi aure da wata yar uwarshi, ya kyakyashe idanunshi ya ce "baya so, ala'dole shi Uwani yake so." wannan shi ne musabbabin kiyayyar, da farko ita ma Atika ta so ta kamu amma tin yanda ya bude mata wuta tayi sanyi har ta dinga sakin jikinta da ita domin ta san halin yayansu sarai ba sai an gaya mata ba.
Haka dai ta dinga zuwa tana dan tayata fira akai-akai har suka fara sabo da Gwaggo Uwani.
Daga karshe dai har suka yi mugunyar shakuwa irin wadda i dan ma baka san Atika kanwar mijinta ba ce zaka ce ciki daya suka fito, shi yasa komai zasu yi tare suke yinsa ba mai kaunar ya batawa wani a cikinsu.
Bayan wasu 'yan watanni Gwaggo Uwani ta fara ganin tashin hankali ga yan uwan mijin domin azaba babu irin wadda bata sha agurinsu! tin tana shigewa daki ta darje kukanta sun ranta! har abin ya fara isarta ta dinga maida masu kadan-kadan tare da gudunmawar mijinta dan kusan ma shi ya fara finjirar da ita, tin yanda suka ga ita ma ta fara finjire masu suka ga nasu ya fara zama wasa, daganan suka shiga biyar malamai da bokaye a turo mata wannan a tura mata wancen.
_Kwana biyu ta fara shan azabar assiri, mijinta ya dinga nema mata taimako a dik inda ya samu labarin wani shahartaccen malami yana iyakacin kokarinsa dan ganin ya samu ya kawo mata, gashi lokacin siyasa ya fara karatowa, da yaga ta fara samun sauki sai ya dinga turata ita da Atika inda yake anso mata taimako, suna zuwa dik sati daya k'are su amso, anan ne labari ya fara canza salo inda ta hadu da wata mata 'yar duniya mai suna lubabatu amma anfi saninta da Lubancy har suka dan fara sabo da ita na tsawon wasu yan lokutta.
Anan ne Lubancy ta samu nasarar canza ma Gwaggo Uwani ra'ayi daga bidar taimako ta koma biyar bokaye, wanda tare da Atika ake zuwa dan ta zamar mata kamar 'yar uwa ta jini, daganan itama Ammie suka fara saitata a layi tin lokacinda ta haife Nadiya wadda ita ce ta karshe a cikin diyanta.
Lokacin da ta haife Nadiya a lokacin taji labarin kara auren mijinta Alhaji Usman, hankalinta bai kara tashi ba sai a lokacin da taga wata mata a cikin gidanta a matsayin kishiyarta, tin daga lokacin ta daure damarar yaki da dik wani mai son rabar mijinta tare da taimakon Gwaggo Uwani da kuma Lubancy.
Tin lokacin da mijin Gwaggo Uwani ya gano kulla-kullar da suke shiryawa ya shata mata layi ta hanyar yi mata saki ukku gangame, ta dawo sokoto da zama a cikin tsohon gidansu, amma ko da haka nan basu rabu da Atika ba kasancewa suma asalinsu daga sokoto ne takan taho gidan kakanninta ta kawo masu ziyara ta koma.
_Bata wani jima da dawowa gida ba Mahaifin Ammie ya rasu, komai ya kara dabircewa dama shine ke yi masu nasiha suna ji idan sun aikata wani abun da ba daidai ba tsakaninsu da mazansu, idan na tsawatarwa ne ya tsawatar masu domin gyarawa, yanzu kuma ya bar duniyar iskanci sai wanda suka zaba!
KARSHEN LABARIN GWAGGO UWANI KENAN, Idan baku manta ba tin a season1 na baku labarin Ammie da kuma yanda ta haukata kishiyarta ta farko sauran kuma ta dinga kashe su da assiri DA DAI SAURAN LABARAN..........
Follow me on wattpad and vote.
ESTÁS LEYENDO
WAHALA DA GATA season2
FantasíaSeason 2. "Hhh ai gaskiya ne Rukayya ni wlhy kin san Allah sai yanzu na san nayi dace da sarakkuwar ta gari domin waɗancan dik sheguna ne matsiyata." "Sosai ma Hajiya! ai Aunty Balkisu kam, ta wuce kowa a cikinsu, sannan ta......" Sa...