*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*
*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
*_{Novel series}_*
*_[♠️SEASON.2♠️]_** WATTPAD @Smart_Feenert ...✔️*
*_[🥀BE ~ SMART🥀]_**_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_**_🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*
*_Episode ~25_*Sai misalin ƙarfe 1:30pm, ya farfaɗo.
Inda Buɗe idanuwanshi kaɗai ke da wuya ya fara yin tozali da ƴan ɗakinsu harda ma waɗanda suke uba ɗaya da su tare da iyayensu da kowa ma, gabaɗai sun yi carko-carko a zaune suna kallonshi, ko wane fuskarshi ɗauke da wani uban tagumi, sannan gurin yayi tsit kamar wajen da aka yi rasuwa.
"Me ya faru Baba? na ganku gaba dai zazzau ne! ina aunty balkisu."
Da mamaki dik wanda ke wajen ya ƙara maida dubanshi gareshi cikin yanayi na ban tausayi, suka shiga yi mashi sannu da jiki.
Amma ko ta kansu bai bi ba, sai famar ce masu yake "Aunty Balkisu tana ina?."
Cikin wani matsanancin mamaki suke kallon junansu tare da tambayar shi "kuma wacece Aunty Balkisu?"
Nan take yace masu "Hajiya fa shi yake nufi."
Da hanzari Hajiya kaka ta ƙara matsowa kusa da shi cikin fuskar ban tausayi, ta ce "Gani nan kusa ɗana kana ji na kuwa?"
Da karfi ya ce "A'a wlhy ni ba ke nake nufi ba! dan Allah karku maidani mahaukaci, wanda baisan abinda yake yi ba."
"Innadillahi wa'inna ilaihim raju'un! yau na shiga ukku wai me na tare maki ne Saudatu? me na tare maki ne kike son ganin bayana da na ɗiyana? me muka yi maki.....uhum'uhum'hihhihhiiiiii." Ta fashe da wani hatsabibin kuka mai ban ta kaici.
Baba ne ya yi hanzarin katse ta, wajen ce wa "kinga Lauratu karki kuskure ki d'ora ma kowa alhakin wannan, dan babu wanda ya san abin da ya sameshi har takai shi ga faɗuwa, kuma a iya gwajin da na mashi kwakwalwar shi lafiya lau take ba abinda ya same ta, koma mene ne ina saka ran nan da zuwa anjima komai zai daidai ta."
"Hmm Allah yasa da gaske ne." A cewar Hajiya Kaka.
Baba ya ce "to shikenan, tin da baki yarda ba"
"a'a nifa ba haka nake nufi ba, kar a canza man magana."
"Ko ma dai ya kike nufi, Allah ya sauwaƙa kawai! ni zan koma ciki."
"Hmm ai ba wanda ya riƙe maka ƙafafun tafiya."
Ko uffan bai kara ce mata ba, ya wucewarshi nasu ɓangaren.
Haka dai kowa ya tashi ya rufa ma Baba baya, aka bar Hajiya kaka kadai zaune a cikin dakin kamar na ubanta, ita ala dole nan zata zauna, ita mai ɗa.Bayan kamar minti 20, Balkisu ta fito daga cikin wani ɗakin dan tin lokacin da su Hajiya kaka suka shigo gidan ta koma can tayi zamanta akan haushin ganinsu.
ko da ta'iso cikin dakin da Uncle Mukhtar yake ta same Hajiya kaka kwance tayi nashe-nashe a saman gado tare da Uncle Mukhtar sunata famar sharɓar baccinsu gabansu gaɗi ba wani shakku ko tsoro a tattare da su.
"Kai kai kai kai wai babbar kazat'uba! ai wannan shi ake ce ma samun sakati tusar a suba! to dan ubanki Hajiya sai kin tashi kin bar gadon nan wlhy, ba mahaifiyarshi ba kuwa ko ke kika haife mahaifiyar shi wlhy sai kin sauko ƙasa tin da bada shi kika zo ba! cabdi, to uban wanda ya fara hauka a duniya, haka kawai dan samun waje daga zuwa na jiya-jiya har an fara nunaman harkar mulkin mallaka? Uhmm to bara na zo na sake samunki anan kwance wlhy kiga aiki da gamawa, Hajiyar banza da ta wofi, sai nayi maganin ki wlhy........*—•«»•—*
A ɓangaren su Ammie kuwa, gwaggo uwani tin da subahin misalin ƙarfe biyar ta farfaɗo, amma dan mugunta Ammie bata bari aka sanarwa da kowa ba ko daddy bata sanar ma ba dan kar ya faɗawa police halin da ake ciki, sabida tafi son a yi ta ganawa maƙiyanta azaba har sai sun manta da cikin duniya suke, dan ita dik a tunanin ta kamar suna cikin matsi ne.
♥♥
Ƙarfe 12pm police suka bayyana a kofar gidan Alhaji Usman dan duba halin da Gwaggo Uwani take ciki idan ta farfaɗo.
A nan bakin get sauran suka tsaya aka tura macce guda ta shiga ciki don ta bincika.
Wanda tin a bakin ƙofar shiga cikin main palour'n take jin kyakkyewar dariyarsu na tashi a cikin palour'n, har ta kai ga isa cikin palourn inda suke da ko sallamar ta basu ji ba...........
Follow me on wattpad and vote.
YOU ARE READING
WAHALA DA GATA season2
FantasySeason 2. "Hhh ai gaskiya ne Rukayya ni wlhy kin san Allah sai yanzu na san nayi dace da sarakkuwar ta gari domin waɗancan dik sheguna ne matsiyata." "Sosai ma Hajiya! ai Aunty Balkisu kam, ta wuce kowa a cikinsu, sannan ta......" Sa...