Episode ~34

127 65 0
                                    

*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
*_{Novel series}_*
*_[♠️SEASON.2♠️]_*

* WATTPAD @Smart_Feenert ...✔*
*_[🥀BE ~ SMART🥀]_*

*_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*_Episode ~34_*

Bayan sati biyu da aurensu Balkisu.

Uncle Mukhtar ya zama kamar almajiri a wajenta, idan yana gidan haka yake kamar wani nakkasasshen bawa! amm da zarar ya bar gidan ya fita wani wajen saiya dawo dai-dai kamar ba shi ba.

Mutane da dama sun fara fahimtar hakan musamman waɗanda ke yawan zirga-zirga a gidan, sai dai kowa bakinshi a riƙe yake sabida gudun kar ace daga wajenshi aka ji.

A yau kuma Gwaggo Uwani ce da Zuhra tare da Nadiya suka iso cikin gidan direban su Ammie ya yi parking ya jibgesu, inda yana ajiyesu ya juya ya yi tafiyarsa.

Cikin murna mai cike da tsantsar farin ciki suka an taya cikin gidan da sallamarsu ta natsatstsin 'yan bariki.

Kamar a mafarki ta jiyo muryoyinsu cikin mugun farinciki ta wazgo a guje kamar wata mahaukacciya ta nufato wajen da suke gabaɗai ta rurrungumesu cike da kewar 'yan uwanta ta shiga yi masu "oyoyooo" inda su ma cikin farincikin suka rurrungumeta a ciki kuwa harda Madam Gwaggo Uwani.

Bayan sun dan futa ne sun sha ruwa sun jika makoshinsu dik da dai ba wata gajiya mai girma ce atattare dasu ba, sannan suka shiga labartawar tsintse da tsegumin Hajiya Kaka, inda a nan kuma Gwaggo Uwani ta shiga kara daurata a hanya.

Inda ta zage damtsenta sama ta jejjefa Balkisu a cikin wutar da take tunanin ita ce ruwan sanyi a gareta tare da kara bada kwarin gwiwarta dari-bisa-dari akan karta kuskura ta sabsabtawa Hajiya Kaka daga yau ta fara dandana mata ruwan Madaci a baki, idan ma da kwai abinda yafi shi ɗwaci ta zuba dik su gauraye, ta nuna mata ainahin ko wacece ita! Saboda Hajiya'Kaka ita ma tin yanzu ta fara dandana gudarta kafin a dawo wajen sauran 'ya'yanta, inda kafin ta dasa ayarta saida ta tufeta da Albarkar "Allah ya'isa idan har ta raga masu."

Sosai Balkisu ta yi Na'am da shawarar da Gwaggo Uwani ta bata domin ita ma kudurinta kenan a cikin zuciyarta an dai rigata faɗa ne a fili.
*Follow me on wattpad and vote.

WAHALA DA GATA season2 Where stories live. Discover now