*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*
*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
*_{Novel series}_*
*_[♠️SEASON.2♠️]_** WATTPAD @Smart_Feenert ...✔*
*_[🥀BE ~ SMART🥀]_**_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**Episode ~47*
_Saida aka fara wucewa da ita ta bangaren'su Papa suma suka saka tasu albarka sannan aka nufi part dinta da ita ( da yake dik cikin gida gudane)_
_Kai tsaye wani mahaukacin palour naga annufa da ita nikaina da naga wannan hadadden palourn sai da nace aljannar duniya kenan domin dukiya'ce tasha iyo sosai a ciki har ta gaji Komai dake cikin dakin dark and light blue ne iya tsaruwa dakin yayi daga cikin palour na hango dakuna wajen guda ukku ko wanne cike yake da kaya, gefe guda kuma wajen dinning table ne hade yake da store a bangare na daban kuma wajen kayan kallone masha Allah👌🏻,_
_Kai tsaye aka nufi daya daga cikin bedroom din da ita, masha Allah gaskiya ba kananan kudi bane Alhaji'Muhammad ya kashema ƴarsa'ba dan ganin ya faranta mata rai, abin kan ba'acewa komai saidai hamdala ga Ubangiji_
_Suna zaunar da ita a tsakiyyar gado sukayi mata huduba mai ratsa zuciya sannan sukayo tafiyarsu, suka barta ita kadai cikin dakin kamar mayya tana ta famar rabe-raben idanuwa kamar bakuru (Kuli-Kuli),_
_Sai wajajen karfe10:00pm Mohan ya shigo tare da abokananshi su ukku Abbakar da Khaleed da khaleel, a gaggauce sukayi abin da suke suka gama Mohan yayi masu rakkiya har izuwa get sannan ya dawo part dinsa tare da garkame ko ina da key,__Bayan ya shigo dakin da take, suka tashi suka gudanar da dik wani abin da ya halatta ga sabbin ma'aurata suyi,_
_Sannan suka danyi ciye-ciyen'su na kayan motsawa a baki suka gama, suka halarce bathroom sukayi wanka bayan sun gama sukayi shirin bacci,_
_Nan take ta bude wardrobe dinta ta zago wata makekiyar rigar bacci wadda zaka iya kiranta da net domin komai na jikinka sai ta fidda waje ba tare da ta rufamai assiri'ba,__Koda Moda ya fito daga palour ya dawo bedroom tin a bakin kofar shiga bedroom ya dasa ayar tsayuwa anan yana kallon irin halittar da Allah ya a zurtata da ita cikin wani shauki na fita a cikin hayyaci,_
_Kwata–kwata bata lura da shiba dan ta matsu'ma bata kare shirirnta'ba taje ta kwanta tin bai kaiga shigowa'ba, ta samu tayi koda baccin karya'ne,_
_Nan ta nufi wajen mirror dauke da takon'ta na daukar hankali kamar wadda ke tausaya'ma kasa,_
_Wasu mahaukwatan turarukka'ne da humrori masu bala'in kamshin tsiya naga ta dinga balbala'ma jikinta kamar mai watsa ruwan wanka,__Mohan dake tsaye a bakin kofa dik ya rikice hankalinsa gaba dai ya fita a jikinsa baisan lokacin'da ya tako ta wajen da take'ba,_
_Kai tsaye taji anriko kugunta ta baya, cikin mugun tsoro ta shiga kokarin kwace kanta, da hanzari ta juyo jikinta baya da niyyar ganin ko wanene amma sai akayi rashin sa'a ta ɓangale ƙasa zata faɗi, saijin tayi an riƙo hannunta tare da riƙe kugunta ta baya da hannu guda,_
YOU ARE READING
WAHALA DA GATA season2
FantasySeason 2. "Hhh ai gaskiya ne Rukayya ni wlhy kin san Allah sai yanzu na san nayi dace da sarakkuwar ta gari domin waɗancan dik sheguna ne matsiyata." "Sosai ma Hajiya! ai Aunty Balkisu kam, ta wuce kowa a cikinsu, sannan ta......" Sa...