Episode ~30

182 100 0
                                    

*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
*_{Novel series}_*
*_[♠️SEASON.2♠️]_*

* WATTPAD @Smart_Feenert ...✔*
*_[🥀BE ~ SMART🥀]_*

*_(🕵🏻‍♀️Crouches prefect of 🌈KAINUWA WRITERS✍🏻)_*

*_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*_Episode ~30_*

inda ita kuma har a cikin ranta, jin Balkisu take a cikin ƙoƙon zuciyarta domin ji take dik cikin sarakkunnenta ba wadda hankalinta ya fi kwantawa da ita sama da Balkisu.

Sai da suka kawo dafda bakin get d'in fita gidan, cikin sanyin jiki Hajiya kaka ta ce "ta barta kawai, nan ma ya isa zata iya idawa har gida."

Cikin nuna damuwa da rashin Jin dadin hakan Balkisu ta dawo cikin gidan tare da rarrashin da Hajiya kaka ta yi mata, inda kuma bayan ta iso cikin palourn ta zauna saman daya kujerar dake cikin jerin kujerun dake cikinshi, sannan ta shiga sakin dariyarta ta mugunta mai cike da tunanin abinda zata sake aikatawa Hajiya Kaka nan gaba.

_Uncle Mukhtar ne durƙushe a gabanta yana kallonta cikin mamaki yanda take sakin dariyarta cikin wani salo mai wuyar fassarawa, a raunane ya ce "Aunty dama cewa nayi yanzu me za'a yi maki ne?
Kamar daga sama ta jiyo sautin muryarshi, kasancewar bata lura da shi a wajen ba, inda zai sake yin wata magana ta daka mashi tsawa ta hanyar ɗaga mashi hannunta guda ta ce "Dakata man! baƙin munafuki dama ina cike da haushin ka yau, wato dan tsabar iya munafurci da kilin-bibi a gaban bainan-nasi kake kirana da sunan Aunty ko?, wato so kake a dinga bararani a duniya ana ce wa "da zuwana jiya-jiya har na mallake mijina ko? sabida dama burinka kenan kaji ana zagina! To wallahi daga yau karna kara jin Aunty Balkisu a bakinka da sunan wai ni kake kira kaji na gaya maka, ko baka ji ba ne?"

Cikin rawar murya kamar barawon da aka kama cikin masallaci yana sata, ya ce "In sha Allah na daina daga yau."

Ta ce "karma ka daina dan ubanka."

_Ya yi shiru yana saurarenta bai ce da ita ko kala ba, sai da ta gama zuba yana kwashewa, yaga alamar ta gaji, sannan ya ce "Amma Aunty da wanne suna zan dinga kiranki da shi?"

_Cikin mugun bacin rai ta ce, "Ka kirani da sunan UBANKA!!!"

****

"Subhannallahi bayin Allah, dik me ya kawo wadannan maganganun haka? Haba Ammie dan Allah kuyi hakuri ku bawa zuciyarku ruwan sanyi! Ni daice aka zo dubawa ko? to gani na tashi ba shikenan ba?"

Police din tace, "Eh! shikenan! Yanzu zaki biyomu tare muje Police station"

"Me zatayi a Polistation bacin gata kun ganta?"

"Hajiya dan Allah ki kama girmanki!" Police din na fadin haka ta fice daganan tayi waje ta shigo da sauran Police din da suka zo tare! dan taga alamar Ammie na son bata matsala wajen aiwatar da aikinta.

_A bakin kofar shiga palourn sauran suka tsaya, sauran kuma suka ida shiga cikin parlour'n..........
Follow me on wattpad and vote.

WAHALA DA GATA season2 Where stories live. Discover now