*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*
*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
*_{Novel series}_*
*_[♠️SEASON.2♠️]_** WATTPAD @Smart_Feenert ...✔*
*_[🥀BE ~ SMART🥀]_**_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**I wish u a Happy new year 2020*
*Episode ~37*
_Faɗa dai kan ya yi ƙamari domin su Aunty Ruƙayya kan andarje kukan wahala.
A can gefe kuma Gwaggo Uwani ce maƙure da wuyan Hajiya Kaka shedarta na biɗar ɗaukewa, inda daga bisani kuma aka maka kanta ga bangon gina saida ta sake tusar ƙarfin hali.
_Uncle Mukhtar ne ya shigo dakin cikin hanzari dan tinda ya shigo cikin gidan yake jin hayaniya sama-sama na tashi, bai ida tabbatarsuwa ba saida ya kawo daf da kofar shiga cikin Palour.
Inda Kai tsaye wajen matar shi ya nufa ya samu nasarar ɓaɓɓaketa daga saman jikin Aunty Rukayya, sannan ya je su Nadiya gefe ya tayar da Aunty Rukayya dake kwance kasa malalaaa-kamar kayan wanki, ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, dan tin lokacin da ta samu aka dauke mata Balkisu daga saman jikinta taji kamar an dauke mata wani katoton dutsi a saman cikinta ne.
Tana cikin tunaninta na jin dadi matakin da take tunanin Uncle Mukhtar zaya zautar wa matarsa da kuma yan uwanta taji an dade da dubin fuskarta an kwasheta da wani irin wawan mari wanda sai da ta kasa daukar kanta tsaye ta fadi kasa kwance ta sake k'ara wanda jin wannan k'arar ne ya dawo da hankalin Gwaggo Uwani dake saman Hajiya Kaka ta makure mata wuya.
Cikin wani mugun karfin hali Hajiya Kaka ta ce "Kam babban bu...uba! yanzu kai dan baka da hankali su gama jibgarmu kamar tumaki kana kallo, har dai ita Rukayya da suka ma taron dangi amma ka rasa abinda zaka saka mata da shi sai wannan wawan marin na mugunta? ina ce wadannan dik kannen ita matar kace ko? amma ka duba kaga yanda suk........." cikin d'aga murya ya ce "ya isa dan Allah Hajiya, idan bata kawo kanta ba dik wannan abin zai faru da ita? ubanwa ya tayar da dik wannan rigimar ne idan ba ita ba?"
"Awww! harka ma kiyasta hakan? wawa bakin sauna wanda bai san darajar mahaifiyarshi ba da kuma kanwarsa." nan take ta fashe da kukan da ya jima cikin mak'oshinta, tana fadin "Wlhy idan de harni na haifeka yau-yau dinnan sai ka sake wannan bakar shegiyar abin da kaje ka kwaso muna."
Cikin hargowa gabadayan'su harda Gwaggo Uwani suka ce "Shegiya dik ta wuce ki? bakar yar tasha wadda tayi gadon tashanci."
Cikin matsanancin Kuka Hajiya Kaka tace "Yanzu Mukhtar kana jin suna zagina amma ko kayi wani abu akai?"
"Haba Hajiya! to ni meye nawa a cikin fadanku? ke kika kawo kanki kuma tin farko ke kika jawa kanki, yarinyar ga dai tana iyakacin bakin kokarinta wajen ganin ta faranta maki amma dik bakya gani! gaskiya ni na fara gajiya da wannan k'iayyar da kike nuna mata, kawai zamu tashi mu baku waje tinda haka kuke so, amma ya zaku sakata gaba ita da yan uwanta kunacin zarafinsu?"
"Mukhtar yanzu ni kake gayawa haka? nice fa mahaifiyarka."
"To danke ce mahaifiyarsa kin isa ki saka shi yin abinda bai ga dama ba?" a cewar Balkisu, inda ta k'ara da ce wa "Ai gaskiya ya fada, kuma wlhy in dai dan ni ce, nan gani nan bari dukiyar uban wani ehee."
YOU ARE READING
WAHALA DA GATA season2
FantasySeason 2. "Hhh ai gaskiya ne Rukayya ni wlhy kin san Allah sai yanzu na san nayi dace da sarakkuwar ta gari domin waɗancan dik sheguna ne matsiyata." "Sosai ma Hajiya! ai Aunty Balkisu kam, ta wuce kowa a cikinsu, sannan ta......" Sa...