Episode ~19

284 104 0
                                    

*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
                  _{Novel series}_
           *_[♠️SEASON.2 ♠️]_*

  *WATTPAD  @Smart_Feenert  ...✔️*
            *_[🥀Be ~ Smart 🥀]_*

*_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_*

*_🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

         *_Episode ~19_*

     "Hhhhh Haba my milkers! me ku ke ci na baka na fita a waje? ai dik yanda kuka ce haka za a yi! Ko yanzu ma idan kuna bukace a shirye nak.........."

"A'a rufa mana na yau jarababbiya! Ba mu kai nan ba, so kike mu ziyarce gidan yari ba mu shirya ba" a cewar Hansa'u da ta yi saurin katseta.

Gabadayansu suka fece da dariya, a daidai wannan lokacin d'ay daga cikin 'yan matan Amaryar wadda ke palour ta shigo dakin da hanzari tana gaya masu ga angaye nan zuwa suyi sauri su k'ara shirya Amarya tin kan su ida k'rasowa ciki.
                           
A hanzarce Memu ta tashi ta shiga k'ra gyara mata kwalliyarta,  tana idawa har ta yafa mata gyalenta ta sake rabketa da wani mahaukacin turare mai bala'in kamshin tsiya.

            kamar daga sama suka jiyo sautin fitar wata zazzak'ar murya tana fadin Amarya "Ba kya laifi ko kin kashe angonki."

Cikin wata murya mai kama da ta k'ramar mage, Hansa'u ta ce "Aiko da babu batu! Amarya ta kashe ango sai dai tarihi."

Gabadayansu dariya suka saka, tare da ce wa "Wannan gaskiya ne."

                Sannan d'ay daga cikin abokanan Angon ya buda masu taron da addu'o'i tare da fatan Alkhairi ga Amarya da Angon, da fatan su ma Allah ya nuna masu na su.

         Aka amsa da "Amin" tare da shafa addu'ar a fuska, sannan Muhsin sarkin son wasa ya ce ma "'yan matan Amaryar to kuma me kuke jira 'yan ganin kwam? sai ku tashi mudan taimaka mu saukeku gida mu futa su ma ku barsu su huta." wanda ya yi maganar ne cikin zolaya.

Aiko kamar daman su ma a jiraye suke, cikin dan jan aji irin na mu na mata, suka yi mashi caaaa da cewar "Babu inda za su tafi, sai an saye baki."

Muhsin yace "bakin wa😳?"

Suka ce "Bakin Amarya."

Ya ce "ai su ma sun saye na ango."

nan dai rigima ta kacame tsakanin Abokanan ango da na Amarya        sai da d'ai daga cikin abokanan angon ya fiddo bandir din dubu'dubu ko canji babu ya miqa ma 'yan matan Amaryar sannan aka zauna lafiya.

Bayan an gama sayen baki, Abokanayen su gaba dai suka yi masu sallama akan zasu wuce su barsu suci Amarcin'su lafiya.

    Cikin farin ciki Uncle Mukhtar ya rakasu har, Sannan ya dawo gidan tare da hudubar Ustaz Muhsin akan ya gudanar da wannan harkar cikin hankali karya kashe diyar mutane.

      Bayan ya iso cikin dakunan su ma ya saka masu key ya kulle.

  Lokacin da ya iso cikin bedroom ya sameta a wajen da ya barta lullebi da mayafi kamar wadda ke jin dari.......
Follow me on wattpad and vote.

WAHALA DA GATA season2 Where stories live. Discover now