*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*
*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
_{Novel series}_
*_[♠️SEASON.2 ♠️]_**WATTPAD @Smart_Feenert ...✔️*
*_[🥀Be ~ Smart 🥀]_**_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_**_🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**_Episode ~ 10_*
Ita ma a sace ta dan gyada mata kai alamar ta fahimta, sannan Atika ta zauna suka ci gaba da sha'aninsu, na tsince da tsegumin da daman shine musabbabin zamansu a wajen.
Bayan kamar minti goma haka, hankalin kowa ya dauku izuwa harkokin gabanshi.
Gwaggo Uwani ta sake wata k'ak'k'arfar kalima wadda sai da tayi sanadiyyar dawo da hankalin mutanen dake wajen a wajenta, kowa sai famar tambayar abinda ke faruwa yake, inda cikin mugun sababi ta ce "Inaaaaa wallahi ba zata sa6u ba wai bindiga a ruwa! ai ba irina ake yiwa sata ba."
Muutanen dake wajen suka ce "Sata shin? Innalillahi wa'inna ilaihim raju'un! me aka daukar maki Uwani?"
A rikice ta ce "Waayayuwana wajen guda biyu aka sace a nan wajen da nake zaune."
Cikin al'ajabi suka ce "lallai harka ta b'ace"
Ta ce "Ai harkar bata gama b'acewa ba wlhy, tukunna dai har sai sanda aka fito man da wayayuwana dan wlhy bazan dauki hasara ba."
D'ai daga cikin 'yan bikin ne ta ce "Anya kuwa Uwani kin bincika da kyau a inda kika ajiye? wata k'ila ma fa a wani wajen na daban kika jefasu kin dai manta ne."
A fad'ace Gwaggo Uwani ta ce "Ya kike man irin wannan maganar? Wanne irin dai a wani wajen na jefasu Hajara? tin d'azu fa nake tare da su a wajen nan, kuma a cikin jikina amma yanzu ace nazo daukar abina, na nemesu na rasa ko k'asa ko bisa? wlhy tallahi ba mai fita a gidannan yau sai an bincike cikinshi da wajenshi."
Cikin mugun tashin hankali gabadayansu suka kwashe da kalima suna fadin "yau sun shiga ukku da ransu da lafiyarsu ace a maidasu tsirara akan abinda bai kai ya kawo ba? Ai ko ko kudi ne sai dai suyi tarbace a biyata da dai kan a mai da su tsirara suna ji suna gani."
Hajara tace "ai ba ma za a kai ga yin hakan ba, a dai sake dubawa da kyau ko za'a dace da ganinsu"
Ba tare da Gwaggo Uwani ta ce da ita ko uffan ba, ta sake lulawa wajen nemansu cikin mugun tashin hankali, ta duba nan ta duba can amma shiru babu su babu samatarsu a nan, sai d'ud'd'ungura wa mutanen biki zagi take tare da alfasha harda su Allah ya'isa."
Hankalin kowa dake wajen idan ya kai dubu sai da ya tashi kowa sai wasi-wasi yake a cikin zuciyarshi.
Atika ta mik'e tsaye daga duk'en da take wajen taya gwaggo Uwani neman wayayuwan, ta ce "Wai Babbar kazat ubannan! wallahi nima an zare man tawa."
Aiko nan jikin kowa ya sake dask'alewa a wajen kamar kitse.
cikin rashin kwarin jiki suka sake daukar wani salati cikin k'arfin hali cike da zargin junansu da alhakin daukar wayayowan a wajensu inda rikici ya ida gaurayewa ta ko ina wasu na shirin yin dambe wasu kuma har sun fara.
Da k'yar dai da wala'haula aka samu abin ya dan lafa ta hanyar fitowa waje gabadai aka halarce cikin harabar gidan inda filin yake, kowa ya ajiye jakarshi gefe ana bincike tare da kiran numbobin wayar kuma dik suna shiga saidai har a wannan lokacin an kasa gano inda suke.
Nan dai wata mata ta bada shawarar "mutum biyar su shiga cikin dakuna su bincika wata k'il barawon da ya sace wayayuwan ya boyesu ne aciki ya manta bai kashe ba." Sosai aka yi na'am da shawarar da ta bada, aka za6e wadanda zasu antaya cikin dakunan su bincika a cikinsu kuwa har da Gwaggo Uwani.
nan take suka fada ciki, suka shiga binciken tako wani bangare tare da kiran numbobin wayar, ba tare da bata lokaci ba suka nufe wani daki inda suke jin alamun sautin k'arar wayayuwan na tashi.
Inda suna isa dakin suka sake kiran wayar, saidai kuma wani abin mamaki, basu sake jin k'arar wayar a ko ina ba sai a cikin jakar.......
Follow me on wattpad and vote.
YOU ARE READING
WAHALA DA GATA season2
FantasySeason 2. "Hhh ai gaskiya ne Rukayya ni wlhy kin san Allah sai yanzu na san nayi dace da sarakkuwar ta gari domin waɗancan dik sheguna ne matsiyata." "Sosai ma Hajiya! ai Aunty Balkisu kam, ta wuce kowa a cikinsu, sannan ta......" Sa...