Episode ~14

278 101 0
                                    

*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
                  _{Novel series}_
           *_[♠️SEASON.2 ♠️]_*

  *WATTPAD  @Smart_Feenert  ...✔️*
            *_[🥀Be ~ Smart 🥀]_*

*_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_*

*_🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

     *_Episode ~14_*

   Uncle Aminu ne tafe shi da Uncle Mu'azzam da Uncle Mu'saddiq, sanye  cikin wata tsadaddiyar shadda kalar Orange tare da wata hadaddiyar babbar riga baqa wadda taji aikin da zare orange, wanda dabbisa takalumma har izuwa hulla agogo dik orange ne, komai na jikinsu  irin daya ne abin gwanin birgewa da ban sha'awa, kuma da ganinsu kaga k'annen ango, domin kamarsu da kwarjininsu gabadai sun bayyana  a tattare da su, sannan wannan shigar tayi masifar d'obosu sai ka ce wasu hanshak'an larabawa.

A gefe guda kuma iyayen angon ne maza, tsaye a waje guda tare da ta su tawagar  suna jiran isowar ango wajensu su tayas, wato Alhaji Kabiru da Alhaji Ibrahim, da suka ci adon cikin wani tsadadden boyel Milk wanda yaji aikin baqin zare harna fitar arzik'i, sai kuma yannen shi su ukku Uncle Mustapha da Uncle Huzaifa da Uncle Muhammad tare da abokanan arziki kowa yana cikin shigarshi ta alfarma, ba wanda ke cikin k'aramar shiga ta ya ku bayi, inda iyakar haduwa kowa yayi gwargwadon tashi Masha Allah.

           Suna fitowa daga cikin gida kowa ya bude motarsa ya shiga aka tayas inda basu zarce ko ina ba sai a cikin babban masallacin dake cikin garin sokoto.   Wato Masallacin SHEHU USMAN BIN FODIYO,  inda basu wani jima da zuwa ba, su Alhaji Usman shi da tashi tawagar suka k'araso a wannan wajen. 

Wa'iyazu billah iya haduwa suma sunyi musamman ma Baban Amaryar dake cikin wani tartsatstsen yadi fari wanda yaji akin zare Ashcolor.

Sosai a ka taru a wannan wajen na daurin aure har sai da jama'ar  unguwar suka shaida, kai da ganin wannan auren kasan bana k'ananan mutane ba ne, domin manya-manyan mutane masu fada aji a cikin garin sokoto, har da na wasu k'asashe da dama sun halarci wannan wajen, kama daga manya-manyan "yan siyasa, Sarakuna, manyan 'Yan kasuwa masu fada'aji da dai sauran wadanda ban ambata ba, suma sun halarci wannan  daurin auren.  

An cika tank'il a masallacin kamar tabkin ruwa. sannan ta ko ina zagaye yake da security lungu da sako, dik wanda yazo wucewa sai dai ya tsaya jira ko kuma ya canza hanya dan ko titin dake wajen saida ya shaida da wannan daurin auren.

           Ba tare da bata lokaci ba aka fara gudanar da addu'ar daurin Aure Inda Alhaji Ibrahim shi ya zama wakilin Ango ita kuma Amarya Babanta ya zama wakilinta, sannan kowa ya shaida daurin auren Mukhtar ALHAJI KABIRU (K.I). da Amaryarsa Balkisu ALHAJI USMAN (MAI DALA) akan sadaki naira dubu dari biyar. tare da fatan alkhairi ga ma'auratan da kuma mutanen da suka halarci wannan wajen hadi da fatan Allah ya maida kowa gidansa lafiya,    daganan liman ya dasa aya tare da addu'ar watsewar taro lafiya.

Nan kowa ya ja tawagarsa suka bar wajen cikin farinciki da annashuwa.

        _inda su kuma su uncle mukhtar direct suka wuce Ibro hotel shi da abokananshi domin gudanar da  dinner shi a can, su uncle Aminu kuma suka wuce gida domin dauko liyafar sauran kayan abincin da aka manta da su a gida.

    *—•«»•–«»«»–•«»•—*

     A bangaren su Ammie kuwa har  5:00pm tayi Gwaggo Uwani bata farfado ba inda hankalin Ammie Idan yayi dubu wajen tashi sai da ya k'ara da dari biyar.

Nan take ta lalabo nmber daddy takira ,yana dagawa, ta shiga  neman shawara a wajenshi domin barin kai Amaryar yau har aga yanda hali yayi, ya ce bai Aminta da wannan shawarar tata ba  domin shi ya fi son lokacinda aka daura aure lokacin Amarya ta tare a gidanta, Haka dai tayi haquri ta dangana amma badan taso hakan ba.

Ta bangaren wadan da ke police station kuwa.
Follow me on wattpad and vote.

WAHALA DA GATA season2 Where stories live. Discover now