*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*
*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
_{Novel series}_
*_[♠️SEASON.2 ♠️]_**WATTPAD @Smart_Feenert ...✔️*
*_[🥀Be ~ Smart 🥀]_**_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_**_DEDICATE TO KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION_*
*_🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂_*
—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*_Episode ~ 5_*
Tin kafin su kai ga fad'in albarkacin bakinsu, Gwaggo Uwani ta sake tarbarsu da wata banzar magana, ta ce "Ya naga dik kunyi shiru kuna kallon junanku, ko zaman ne ya kawo ku ba aikin ba? I dan ko har haka ne gaskiya kun bani kunya."
Wani irin kayataccen murmushi mai saurin k'unar zuciyar wanda aka jefa da shi, Hajiya Munira ta ce "Uhum Uwani kenan! I dan ba aiki ne ya kawomu ba, to mezai kawo mu anan kuwa? amma kafin nan..." ta kalli wajen da Nadiya take da har ta kusa kurd'ewa cikin store, ta ce "Nadiya kina iya dawowa kici gaba da abinda ya shafeki, dan ina ga hakan zaifi maki amfani sabida mu ba ma buk'atar canza wasu tifafin akan zamu yi aikin! na jikinmu ma sun isa."
Cikin takaici Gwaggo Uwani ta ce "hmm lallai fa, amma fa kun matuk'ar burgeni, wanda hakan ya sa na shiga cikin wani mawuyacin yanayi na tunanin muhummancin wannan auren a gareku ya ma wuce lissafina."
"Allah sarki! ai ba wani fa'idar canza tufafi a bikin 'yarka, yana da kyau a gareni daukar wannan auren da matuk'ar muhimmanci fiye da yanda kike tunani, domin mu ke da diyar kuma mu muke da ikon bada ita ga dik wanda rainmu yake so!, kinga ko mununa bajintarmu da gwanintarmu tare da bada kwarin gwiwa dari-bisa-dari ga wannan gagarumar harkar da Allah yaqaddara da rabon ganinmu a ciki, bai zama gazawa ba! gashi kuma bikin ya fado mana cikin irin wannan lokacin da ya zamana muna da rai da lafiya ba tare da tsufa ko kuma kunji wanda zai iya hanamu taka rawar gaban hantsinmu ba! dan haka kinga ko ba komai dole ne mu mik'a godiyar mu ga Allah [S.W.A] da har ya k'addaremu da ganin irin wannan lokacin."
Cike da bakin-cikin wadannan zafafan kalaman da take jin su tamkar an tsoma gangar jikinta a cikin tafasasshen ruwan zafi an saka mucciya ana juyata da ita, gwaggo Uwani ta ce "Babbar bu...uban nan! wlhy k'aryarki ta sha k'arya Hajiya Munira! mu ne k'irjin biki kuma d'iya mu ke da ita, mu muke da hurumin yi mata Aure ga dik namijin da rainmu yake so, dan hakan wannan batun ma da kike kina b'ata yawun bakinki ne a banza, a wajen da basu da amfani.!"
A hankali Hajiya Munira ta ce "Hmm! lallai fa kina da gaskiya Uwani, amma ki sani dik Uwayen kirki da mutunci ba sa yadda su aura ma diyansu yarinyar da bata da dangin Uba domin sune komai na rayuwarta, amma tunda har kince k'arya ne Alarahma Uwani zan so ki dan ja mana aya ko hadisi inda Addini ya aminta da hakan ba tare da wani kwakkwaran dalili ba wanda Allah da manzansa suka aminta da shi."
A harzuke gwaggo Uwani ta mike tsaye ta ce "ke na fiki zama 'yar babbar bu...uba fa a wajen nan wlhy, ko dan kin ga....." bata ida kai k'arshen zancenta ba, Fatima ta sharbe zancen da cewa "Dakata a nan Gwaggo Uwani! wlhy karki soma ki zage mahaifiyarmu a gabanmu, dan zamu iya jure komai amma banda zagi da cin zarafin mahaifiyar mu! dan haka yana da kyau dik wani abu dake damunku a kanmu ku fito fili ku sanar mana ba sai kun tsaya wani boye-boyen da ba shi da amfani b......."
Cikin d'aga murya da sun yab'a ma Fatimar magana Gwaggo Uwani ta katse ta da ce wa "ke kuma as wa? dan-wake a hotel, idan kika ce zaki man rashin kunya, sai na yi wa shegen k'ololon kan nan na ki mugun bugu a bangon dakin nan sai ya watse, dan ni kin yi min kad'an na tsaya sa'insa da ke! Uwarki ga ta nan zaune ita ce sa'ata! ina fatan kin fahimta?"
Ammie da taga abin ya fara wuce gona da iri ta ce "Haba Gwaggo! dan Allah ki saka masu ido ki kyalesu tinda jidalin ne ya kawosu nan, mu farinciki muke yi ba bak'in ciki ba, tin da har haka suke so dan Allah ki saka masu na mujiya..!" Ana cikin hakan, sai ga 'yan'uwan Ammie rutu'tutu sun fado cikin dakin da hanzari.....
Follow me on wattpad and vote.
YOU ARE READING
WAHALA DA GATA season2
FantasySeason 2. "Hhh ai gaskiya ne Rukayya ni wlhy kin san Allah sai yanzu na san nayi dace da sarakkuwar ta gari domin waɗancan dik sheguna ne matsiyata." "Sosai ma Hajiya! ai Aunty Balkisu kam, ta wuce kowa a cikinsu, sannan ta......" Sa...