Episode ~45

100 20 0
                                    

*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
*_{Novel series}_*
*_[♠️SEASON.2♠️]_*

* WATTPAD @Smart_Feenert ...✔*
*_[🥀BE ~ SMART🥀]_*

*_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂*

*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*Episode ~45*

_Me kuke nema anan_

_Kai tsaye su kace sunzo ganin watane,_

_A inah_

_A cikin gidannan, suna mai nuna mashi gidan_

_Wacece a ciki,_

_Wlhy bamu rike sunan'ba,_

_Kuban misalin yanda take_

_Doguwa'ce fara,_

_Kai ni bazan gane wannan dabirtaccen misalin naku'ba ai dik gidan babu baki a ciki, ku bari na turo maku wata idan ita kuke nema! idan kuma ba ita bace dan Allah kuja machine dinku ku kara gaba,_

_Ba tare da yaji amsar maganar suba yaja motarsa ya ida kara sawa ciki, ""Uncle'Mustapha kenan da dawowarshi wajen kasuwancinsa kenan ya tsaya yana subur budo masu tanbayoyi kamar dan jarida,_

_Yana fitowa daga cikin motar kaitsaye ya nufi bangaren Hajiya'Kaka, tin a bakin kofar shiga cikin palour ko sallama bai tsaya yiba ya shiga kwalawa marainiyarsa kira wato Fatima,_
_Tin yanda taji Uncle'Mustapha na mata irin wannan kiran kamar wadda tayi wani babban laifi nan take ta ajiye Morphin dinda take cikin hanzari tayo wajen da yake da sauri,_

_Saida ta durkusar da gwiwowin'ta har kasa cikin ladabi da biyayya sannan tace Uncle gani,_

_Nan take ya ɗauke'ta da wani raki'in shuri har saida ta wintsile kasa ta sake tashi zaune sannan yace ƴar'iskar banza tambaɗaɗɗiyar yarinya maza kije waje anason ganinki kuma wlhy ki tabbatar kin basu hadinkai dan ko yau ta kama aurar dake zanyi cikin buga tsawa yace "Ko bakiji bane dan ubanki",_
_Cikin rawar murya tace naji Uncle,_

_A hanzarce ta mike tsaye ta fita daga cikin dakin. ta nufi hanyar fita get hartayi kusan Isa tajiyo murya Hajiya'Kaka na fadin to annamimiya gidan ubanwa zakije, Kafin takaiga bada amsa har Uncle'Mustapha ya zabce tambayar ya maida wajenshi yace ni na turata waje akwai wasu ƴan'iskan matsiyata dake nemanta idan sun sasanta junan'su ko bata sonshi sai andaura auren gobe,_

_Da kyau ai hakan shine dai-dai wlhy gwanda da kayi hakan tana mai maida dubanta ga Fatima dake tsaye har yanzu ta kasa fita bakin get, Tace to tantiriyar munafuka ai tinda kinjiya sai ki ida fita ko! bakar shegiya,_

_Ba tare da tace da ita ko kala'ba cikin mutuwar jiki ta dinga takonta sut-sut-sutt kamar wata babbar ɓarauniya, har tabar cikin gidan_

_A cikin napep ta hangosu zazzaune kamar wasu tumakai, kai tsaye ta ida karasawa wajen koda suka hangota gabadai suka fiffito daga cikin napep suka nufato inda tadan labe cikin sallamar'su,_

_Ta amsa masu kai tsaye tare da gaishe dasu cikin sakin fuska,_

_Bayan sun gama gaisawa'ne suka shiga fada mata abinda ke tafe dasu, ko ida rufe bakinsu ba suyiba suka jiyo muryar Uncle'Mustapha wanda shi ya katse masu hanzari wajen idawa,_

WAHALA DA GATA season2 Where stories live. Discover now