Episode ~ 11

283 108 0
                                    

*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
_{Novel series}_
*_[♠️SEASON.2 ♠️]_*

*WATTPAD @Smart_Feenert ...✔️*
*_[🥀Be ~ Smart 🥀]_*

*_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_*

*_🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*

*_Episode ~ 11_*

Sai a cikin jakar Hajiya Munira, gaba dayansu suka dauke da salati mai hade da ban mamaki. tare da finciko jakar da k'arfin Allah sai da hannu guda na jakar ya sance, sannan suka tinkaro waje da ita, inda suka same mutane a tsatstsaye sunyi carko-carko suna jiran ganin sakamako.

Gwaggo Uwani ce ke rik'e da jakar a hanunta, ta riga sauran fitowa waje sabida zanzana, inda tana isowa ta cira jakar sama tana fadin "jama'atul wajen nan, kunga jakar barauniyar da ta sace mana wayayuwa, domin a cikinta muka samesu gabadai."

Ko ida rufe bakinta bata yi ba kamar daga sama ta ji ance "wallahi k'aryarki ta sha k'arya Uwani! wannan ba shirin kowa ba ne illa na ku, kuma wlhy sai kun warwareshi a fito da gaskiyar waje kowa ya ji ta, dan mu munfi k'arfin mu dauki kayan wani balantana naki! Wai ma me kike tak'ama da shi ne wanda mu ma ba ma da shi? me kika tara ne a duniya da har zai tsone mana ido a kanshi?, abinda kika aikata yanzu kuma me ya tabukar maki da shi ne in banda kunya da tab'ewa? Me ya k'ara bayyana a gareki in banda saunanci da rashin sanin darajar kanki? sannan dande baqin wulak'anci makircinki na ki na yau bai tashi akan kowa ba sai akan mahaifiyarmu? wlhy an dai ji kunya idan ansanta."

Kafin Gwaggo Uwani tayi wani yunkurin maida mata martani tini wata mai bakin raiza ta sharbe zancen da cewa "Ok! idan na fahimceki, borin kunyar ne kike son ki barar mana da shi a wajen nan ko? to ki k'ara gaba da shi, wata k'il a can zai iya yi maki amfani amma ba a nan ba, dan babu wajen zamanshi! gaskiyar dai ce kuma ta fito fili buru-buru kowa ya gani ya tabbatar! to meye ne kuma amfanin tada jiyo jin wuya anan? tin kafin mu kai ga fara tada namu?"

A zafafe Gwaggo Uwani ta ce "Ki barni da bak'ar munafuka Zara! Ni ce daidai da marar tarbiya irinta, dama ai an dade anayi sai yanzu ne Allah ya toni assirinsu dama ance rana dubu ta barawo ce rana d'aya tak kuma ta mai kaya ce, dan haka wlhy tin wuri ku naima ma kanku mafita dan yau mai hana mu dank'ara maku shegen dukan tsiya a gidannan wallahi shi ne Allah, domin mu ba'a mana sata a take lafiya, sai mun yi ma mutum hukunci daidai da abin da ya aikata."

Hajiya munira ta ce "Hmmm wlhy Uwani kin ban mamaki, sannan kin cuce rayuwata ba ki man adalci ba, ban taba tinanin qiyayyarki a gareni hartakai hakan ba kinyi man k'azafin abinda ban san nayi ba! wlhy ko a mafalki ban taba tinanin zaki man irin wannan mummunan k'azafin ba! habaa mana Uwani, wannan wanne irin abu ne haka? me namaki? ko kuma me na kashe maki? ki gayaman Uwani! Hmm Amma kin ban kunya wlhy kuma kin bani mamaki, dik ina kika baro yawan shekarunki da hankalinki da tunaninki da wayonki? Ina kika baro su Uwani? amma ki sani wata shari'a sai a lahira ki je ke ma zaki gani in dai duniya ce gaki gata."

"Babbar malafar ubannan! ni kike gayawa wad'annan banzayen maganganun? wato kina nufin k'azafi na maki? Ni wlhy nafi gabannan kuma nafi k'arfinki nafi k'arfin dik wani wayonki! kuma na fi k'arfin dik wanda kike tak'ama da shi a doron k'asar nan, sannan na fi k'arfin na maki k'azafi! Kuma billahillazi yau sai kun yabawa aya zaqinta dan ba wanda zai fita a gidan nan yau a cikinku da hannu guda wlhy sai mun debeshi munyi maku hukunci daidai da abinda kuka aikata domin ya zama izina ga 'yan baya! sannan wai dan ma babbar bu...uba! a dake mutum a hana shi kuka! yau ninaga cin zarafi."

HAJIYA ta ce "Uwani ba hannu kadai zaki cire mana ba dan Allah idan kin isa karku barmu da rayuwa a cikin gidannan."

Cikin mugun jin zafin wadannan tafasasshen zafafan kalaman da Hajiya tayi mata, Gwaggo Uwani ta hiranyanyo sama a guje ta wazgo kamar wata zakanya ta nufato wajen Hajiya Munira tana fadin

"wallahi na fiki zama 'yar tasha! kai ku bani waje in nuna mata cewa ruwa ba sa'ar kwando ba ne! wuihuhu billahillazi na rantse yau sai na ci bu..ubanki Munira, sai kin gaya man ubanda ke maki k'azafi a wajen nan! kai ku banwaje nace da kazat uba! wayyo Allah Aljannuna sun tashi" ta ce da k'arfi.

Cikin wani mugun tsoron aljannun Uwani da suka ji ta ambata kamar da gaske, kowa ya kauce ya bata waje tare da shirin taya ta damben idan ta kama.

Cikin wani gurnanin zaki ta isa wajen Hajiya Munira ta daga hannunta sama da yunk'urin wazge ta da wani mugun mari.

Sai jin tayi ita ma an here hannu sama da k'arfin Allah an tarbeta da wani irin mahaukacin bugu a tumbi sai da yayi sanadiyyar faduwar ta qasa kwance sumammiya, akan azabar wannan naushin.

Aiko nan hankalin mutanen da ke wajen ya yi wani mahaukacin tashi ganin uwar gayya k'asa a baje ko motsin kirki babu a tattare da ita.

a gurguje wasu suka tin karo wajen da take da hanzari cikin tashin hankali, inda wasu kuma suka haramma Fatie wadda suka ga hannunta ya sauka daga saman cikin Gwaggo Uwani, wanda ganin abin ya fara wuce gona da irinta ya sa Amratu antaya ma fadan domin taimakon k'anwarta da ta ga anyi wa taron dangi.

Tsaye Hajiya Munira ta yi a gefe tana kallon ikon Allah tare da wata irin ajujuwa da take jin tana neman rabketa k'asa, wanda hakan ya saka ta damb'are masukkanta a saman wani d'an dakali dake kusa da ita.

Iyakar k'arfin hali wajen nuna harkar jarumta su Fatie sun nuna a wajen fadan, domin mutanen da suka haran masu sun fi k'arfin mutum hamsin, amma dik da hakan babu wanda ya iya da su, sai cira k'attan banza suke sama suna rabkewa qasa.

A bangaren Gwaggo Uwani kuwa, an wankadeta da ruwa sun kai galan goma manya, amma ko nishi babu balantana samatar tashi, inda wasu suka soma ce wa "ta mutu" wasu kuma na ce wa "tana raye, buguwar da ta sha ce, ta dibe'ta da yawa har hakan, shi yasa ta kasa farfad'owa da wuri."

Haka dai aka tattaleta kamar ragga, aka kai dakin Ammie aka jibgeta kamar kayan wanki a saman gado sannan kowa ya kama hanyar gabanshi, inda Atika ce kadai aka bari a tare da ita domin kulawa da ita, da ita ma tin lokacin da ta ga an bawa Gwaggo Uwani tsarabar wannan irin mahaukacin dukan, ta ajiye makaman yak'inta k'asa dan tsiratar da lafiyar jikinta....
Follow me on wattpad and vote.

WAHALA DA GATA season2 Where stories live. Discover now