*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*
*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
_{Novel series}_
*_[♠️SEASON.2 ♠️]_**WATTPAD @Smart_Feenert ...✔️*
*_[🥀Be ~ Smart 🥀]_**_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_**_🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**_Episode ~12_*
A can waje kuwa fad'an ne ake ta famar zabga babu k'ak'k'autawa domin arzikin bana dai ya ci uban na dah, inda masu lalurar aljannu tini sun gama tashi har sun samu nasarar mai da wasu daga cikin mafadatan tsirara, wasu kuma anji masu mummunar rauni, kowa dai sai da aka yi k'ok'arin bashi tashi gudunmawar.
Ammie ce zaune a bedroom d'in Daddy ita da yaranta ta saka key ta kulle kansu a ciki, gudun kar a kawo masu hari dan tin lokacin da aka fara fadan tsoro ya hanata fita, haka ma diyanta dan ko wani kyakkyawan motsi bata yarda su yi ba, jiran suke fadan ya k'are su samu damar fitowa waje amma abin ya cutura domin har yanzu an kasa shawo k'arshen matsalar.
Nan dai ta yanke shawarar kiran Daddy ta sanar da shi abinda ke faruwa, dan tin shekaran jiya marabinshi da gida, yana can sabon gidanshi tare da sauran abokananshi da manya-manyan bak'inshi wadanda suka zo tun jiya daga k'asashensu dan gudanar da shirye-shiryen lalurar daurin auren tare dasu, kasancewar kuma a masallacin Shehu za'a daura auren.
Kira guda daddy ya dauka, ba tare da sun tsaya gaisawa ba, ta shiga kora mashi k'arya da gaskiya, tin daga inda fadan ya samu isali har izuwa yanzu da yak'ara armashi, ta kwashe ta sanar mashi harda kukan munafurci domin k'arama harkar tested wajen daukar kwakkwaran mataki akan 'yan uwanshi, tare da k'ara bashi kwarin gwiwa dari-bisa-dari wajen turo yan sanda a tafi dasu Hajiya Munira a kaisu magark'ama a kulle, kuma sossai shi ma ya yi amanna da hakan domin iyakar harzuk'a ya yi har hayaki tafasa ke fita a cikin kwanyar kanshi.
Bayan sun gama wayar, a gurguje ya kira nmber ACP ya shaida mashi abinda ke faruwa a gidan shi, inda cikin kulawa ACP ya ce "in shaa Allah yanzu zai tura yaranshi gidan su je gabadai su kwasosu azo dasu office." Daddy ya yi mashi godiya sannan suka yi sallama da junansu cikin kulawa.
Ko 10mins da ayi ba da gama wayar ta su ACP ya turo Hillocks wajen guda biyar a gidan, inda da taimakon Baba mai gadi suka samu damar isa cikin gidan har wajen da ake gudanar da wannan tab'argazar.
Har suka iso cikin gidan tsunbulbul, mafadatan ba su san miyar da ake sha ba a wajen ba, dan sosai suka maida harmarsu wajen fadan, dan yanzu danbe ya dawo wasu-wasu a tsakaninsu, dik wanda aka samu rabka ake.
police din da suka ga haukar da ake bugawa a wajen tayi bala'in yin yawa, kuka akasarin mafadatan mafi yawancinsu dik matan aure ne, kuma basu zo tare da police macce ko guda ba balantana ta shiga ta farma rabon fadan.
Nan dai wani ASP ya ciro waya daga cikin Aljilhun wandonshi ya kira number ACP, ya shaida mai abinda ke wakana a wajen, dan su kansu basu san ta inda zasu bullowa al'amari ba, nan ACP ya bashi izinin harba bindigar sama domin dawo da hankalin mafadatan a wajensu.
Cikin zafin nama ya halba bindigar sama ta ce "twaaaaaaaa." wanda jin k'arar bindigar ya sa gabadayansu kwantawa k'asa a rigingi ne, suna ihun neman agaji.
Ba tare da bata lokaci ba, polices din suka gewaye su kamar yan boko haram, aka dinga murmurk'aasu cikin motocin ana jefawa, sannan aka dauki hanya police station dasu, sai famar ihu suke..
Follow me on wattpad and vote.
YOU ARE READING
WAHALA DA GATA season2
FantasySeason 2. "Hhh ai gaskiya ne Rukayya ni wlhy kin san Allah sai yanzu na san nayi dace da sarakkuwar ta gari domin waɗancan dik sheguna ne matsiyata." "Sosai ma Hajiya! ai Aunty Balkisu kam, ta wuce kowa a cikinsu, sannan ta......" Sa...