Episode ~ 4

278 98 0
                                    

*_🌈KAINUWA WRITERS ✍🏻ASSOCIATION🤝_*
'''{United we stand and succeed, Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_*

*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
_{Novel series}_
*_[♠️SEASON.2 ♠️]_*

*WATTPAD @Smart_Feenert ...✔*
*_[🥀Be ~ Smart 🥀]_*

*_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*

*_🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂_*
—•—•—•«»«»«»«»•—•—•—

*_Episode~4_*

Wasa-wasa lokacin bikin nata k'arasowa kwanaki na ja gaba.

Yau ta kasance ranar Alhamis daren bikin Balkisu da Uncle Mukhtar

'yan-uwan Alhaji Usman ne su Ukku mai napep ya sauke a daidai get din gidan.

Hajiya munira wadda suke kira da Hajiya, d'iya ce a gurin k'anen Mahaifin Daddy, Malam Abdul, wanda Allah ya yi ma cikawa tinda dad'ewa, sai fatima da Amratu wadanda suke diya ne a wajen Hajiya Munirat.

dauke suke da jikunkunan kayansu na biki nik'i-nik'i a hanunsu, domin anan suke da tabbacin zasu sauke farali sai bayan biki zasu koma gida.

A hankali suka kwankwasa get Baba Mai-gadi ya taso da hanzari ya walgale masu shi sannan suka kurd'e ciki, wanda tin kafin su ida isa cikin harabar gidan suka tsinkanyo 'yan-uwan Ammie gurguzu guda a waje kamar 'yan gudun hijira, sai sharbar labarinsu suke suna kwasar dariya kamar wasu dungura-dunguran mahaukata.

Da sallamarsu suka k'arasa wajensu tare da gaisuwa cikin sakin fuska.

kamar Majalisar Arna suka yi kunnen uwar shegu da su, babu wani wanda ya ko kalle gurin da su ke balantana su ga damar amsa masu, sai 'yan k'alilan daga cikinsu da suka d'an amsasu cikin rashin dad'in rai tamkar wadanda aka saka dole sai sun amsa sallamar. tare da tarbarsu da ruwan harare-hararensu na banza had'i da ji fansu da tsakin rainin wayo

Gabansu gad'i su Hajiya suka ida k'arasawa ciki, ba tare da sun tsaya bi ta kansu ba, suka nufe sashen da suke tunanin su Ammie na can.

ko da suka isa cikin parlourn suka sameta ita da yaranta tare da wata mata wadda kusan zasu kai sa'a (Shekaru) daya da ita, suna dan tattauna batu.

Da sallama suka shigo dakin a takure kamar wasu bayi, ba tare da sun jira an amsa masu ba dan sun san ansawar a wajensu ba dole ba ce, a yanda suke kallon kansu.

suka neme waje a saman kujerun dake dakin suka maka mula-mulayensu sama, sai da suka zauna dasss bayan sun gama sauke nannauyar ajiyar zuciya, sannan su Ammie suka ga damar amsa masu sallamar ciki-ciki tare da kauda fuskarsu gefe suna ci gaba da labarin da suke.

Su ma din dai hali guda suka nuna masu da wadanda ke waje domin gabadayansu ba wanda ya yi masu kyakkyawar tarba da ita har diyanta, dik da su d'in dama haka halinsu yake shi ya sa basu wani damar da kansu akai ba.

Wannan matar ce dake fira da Ammie ta kira sunan Nadiya cikin muryar k'asaita, ta amsa da "na'am gwaggo Uwani"

Gwaggo Uwani ta ce " Ki je store ki dauko masu uniforms su saka tinda aikin ne ya kawosu yanzu sabida ba wanda bai san biki sai gobe ba."

Cikin mamaki irin wannan bak'in wulak'ancin da aka fara tarbasu da shi, ko waccensu ta kalle 'yar-uwarta tare da wata zankadediyar magana Abakinta......
Follow me on wattpad and vote.

WAHALA DA GATA season2 Where stories live. Discover now