page 4

282 30 0
                                    

*04*

*BUKAR LAMI'DO LGEA PRIMARY AND SECONDARY SCHOOL*
  Makarantace daya tilo dake hanyar shigowa garin kwara-kwara, k'auyen dake cikin Egabi local government a cikin garin kaduna state.

Ankafa makarantar da dadewa amma mutanen garin sunk'i habbakata ta dalilin k'in kawo yaransu makarantar sabida da rashin wayewa akan ilimin boko. Yaran sarkin garin da liman sukad'ai suka soma karatu a makarantar sabida iyayen sun aminta da ilimin sannan sune masu fad'a aji, sai daga baya kuma 'yan tsirarun mutane suka soma sanya 'ya'yansu, gaba-gaba har yazamanto fulanin dajukan da ke kewaye da garin suma sun sako nasu ciki, ganin ta bunk'asa sosai sai aka gina musu secondary d'an gaba da primary d'in.

*
A k'asar bishiyar d'orawar dake harabar makarantar yarane mata su uku zaune akan wata sallaya mai fad'i duk sun duk'ufa suna rubutu bisa ga alamu assignment sukeyi.

Zuwa can dayansu ta rufe littafinta tare da furta "Alhamdulillah."  Wacce ke gefenta ta d'ago tana kallonta "Badai har kingamaba?"

"Gashinan idonki yabaki amsa."

"Uhmm lallai Bahijja kinji dad'i,  komi baya miki wuya  musamman darasin turanci da lissafi."

Murmushi tasaki tare da matse hannayenta wuri d'aya sukayi 'yar k'ara sannan ta amsa "Kema wasa kikasa aranki maryam amma ai da komi baya miki wuya, sabida haka kima kanki fad'a kikoma kamar da yadda nasanki da maida hankali akan karatu."

"To k'awata zan dage insha Allahu ."

"To Allah ya yarda."

"Amin."

Ta matsa kusa da dayan wacce take ta tsaki tana tura baki, kunnen ta Bahijja taja da k'arfi wanda sai da ta sa ki ihu, tasoma liliya kunnin.

"Wallahi Adda Bahijja nakasa samo amsa ne shine abin yabani haushi har nayi tsuki amma kiyi hak'uri namanta kintsani tsaki."

"To naji iya surutu."

Tana dariya ta motso jikin ta "To Adda taimakamin insamo amsa ko na tsira daga bulalan Mr. Joshua."

Cikin tak'ai taccen lokci ta yimata bayi ta ke ta samo amsar, cikin jin dad'in ta  ce "Allah yabiyaki da aljanna Adda mai sona"

"Amin." Maryam ta amsa wacce itama ta kammala aikinta.

Nana ta cigaba da cewa "Wallahi Mr. Joshua  baya da imani kuma bai wani iya kayarwaba sai uban cewa kungane? Inba a amsaba yabi kowa da bulala akan dole ake cewa angane alhalin ba agane komiba."

"Wallahi kam maganarki haka ne Nana, dawani k'aton muryansa kamar ana buga duro." Fad'in Maryam.

Ai kam suka bushe da dariya, ita dai Bahijja murmushi tayi domin bata fiye yin dariya ba.

"Shiyasa ba ku gane koyarwansa sabida kun rainashi."

"Uhm Adda Bahijja kenan, kedai kinji dad'i kina ganewa amma Allah kowa yasan baya bayani mai kyau ko ya ya Musa naji yana maganar baya fahimtar komi."

"Wani Musan?" Maryam ta tambayeta.

"Na gidanmu mana."

Dariya ta kwashe dashi har da rik'e ciki, cikin fushi Nana falla mata duka "Mi ye haka wai?" Maryam ta tsagaita da dariyan tana mai cewa "Gani nayi yaushe yazo makaranta da zaisan malamin dake koyarwa da kyau da mara kyau."

"Uhmm kumafa maganarki haka ne Maryam, Yaya Musa baison karatu sam daga boko har addinin, inaga k'ila wurin abokansa yaji suna fada."

"To saidai haka kam."

 Bahijja dai ta yi shiru tana sauraransu zuwacan taja ajiyar zuciya duk suka kalleta idanunta lumshe tana murmushi.

Maryam ta dafata "Ya akayi kuma haskenmu kuma matar Yaya Bilal."

Ido ta ta bude sai kuma tak'ara kullewa, cikin sanyin muryanta tasoma magana "Kewar Umma ta da Yaya Bashir ya dameni sosai akwana kinnan, ina jin lokaci yayi da zan nemi ganinsu koda gwagwgo bata sani ba, zan tsere intafi wurinsu, in koma cikin gata na ko na yi ban kwana da tijarar Gwg. Lanti."

Cikin jimami Nana ta dafata "Adda Bahijja kinsan garin dasu ke ne?" Kuma zaki iya ga ne hanya?"

Hawaye ya zubo mata ta share da bayan hannunta sannan ta amsa "Ban san hanyaba Nana amma nasan sunar garin."

"To kik'a hak'uri Adda wata rana zakigansu yanxu kada ki gudu wani abu yasameki na cutarwa ahanya."

Maryam ta amshe "Eh Bahijja kiyi  hak'uri inkinyi aure sai mijinki ya kaiki, na san Yaya Bilal ba zai k'i ba."

Cikin jan ido muryanta na rawa ta ce "Wallahi bazan bari sai nayi aure ba, har shekaru nawa nan gaba? Tab bazan iya jira ba. To wai angaya muku ni zanyi aure a k'auyen nan ne?"

Dik suka zaro ido Maryam ta ce "Garin namune k'auye kuma?"

Bata amsaba ta mik'e ta nufi hanyar ajinsu inda aka rubuta js 2A. Da kallo suka bita cike da jin haushin ta kira garinsu k'auye.

RAYUWAR BAHIJJA.Where stories live. Discover now