page 7

213 26 0
                                    

*07*
Rungumeta yayi sosai hawaye na bin fuskan shi cikin sark'ewar murya yasoma magana "Bazan barki ba K'anwata, k'afata-k'afarki insha Allah."

Zamewa ta yi ta dago tana kallonsa fuskanta dauke da murmushi kuma ga hawaye yana zubowa. Hannu yasa yana share mata hawayen yana kuma mata magana ahankali "Kibar zubda hawayenki haka nan domin yau zakibar k'auyennan, yau a jikin umma zaki kwana da yardan Allah."

Cikin murna ta sa ki dariya ta kamo hannunsa ta k'an-k'ame.

Bayan an natsu Malam ya dubi Bahijja d'auke da murmushi  "Nagodewa Allah S.W.A daya nufeni da cika miki alk'awarin dana d'auka naganin na sadaki da Ummanki, fatana yanxu shine inkin koma kada kisa wasa akaratunki ki maida hankali sosai yadda nan bada jumawaba ace nazo taron bikin yayen haddarki kamar yadda akayi na saukanku."

"Insha Allah zakazo Malam nan bada jumawa ba." Ta ambata cikin matsanancin farin ciki.

"To Allah ya nufa hakan d'iyata."

"Amin." Gwg. Bintu ta amsa.

Nana ta b'ata rai, idanunta suka ciko kamar zatayi kuka dik sabida bata son tafiyar Bahijja.

Bashir yabawa Malam kyutar kudi masu yawa da kyar ya amsa sannan yayiwa sauran mutanen gidan kyautar kudad'e, Gwg. Bintu kam nata na daban ne sannan ya k'ara da yi mata godiya na jajircewar da ta yi akan kula da Bahijja alhali wacce alhakin hakan yarataya awuyarta tagaza yi.

Gwg. Bintu tayi ta samishi albarka tana sharan kwallar rabuwa da Bahijja. Malam yaso yajira dawowar Gwg. Lanti su gaisa amma ya ce sam bazai tsaya ba domin had'uwarsu ba zaiyi kyauta dan ta nemi yi masa hauka zai takata baruwanshi da shirme. "Kaga Malam da in tsaya abu mara d'adi ya afku gara na wuce sai dai ga sak'o a sanar mata in ta dawo tajira dawowata na biyu domin amsar gadon da ta matsa aka bata na Bahijja dan kula da lamarinta mai makon hakan sai ta maidata baiwa mara gata, ta yi ta azabtar da ita, to ta shirya biyansa."

Ganin ransa ya b'aci yasa Malam ya yi ta tausansa har ya sakko. Bahijja da Nana sai kuka sukeyi da kyar aka rabasu da juna. Bashir ya yi musu sallama suna tayi masa adduar sauka lafiya.

Daf da zasu fita garin sai ga Maryam da Bilal akan mashin, Bahijja ta kwaltawa maryam kira amma batajiba ta koma ta lafe cikin seat tana cigaba da zubar hawaye sabida ganin Maryam da yayanta ya k'ara jefa zuciyrta cikin kewa.

Bashir bai hanata ba har sai tayi mai isarta ta hak'ura sai jan zuciya takeyi zuwa can barci ya kwasheta.

Har suka iso birnin Zazzau bata farkaba. A habar Shagalinku guest in ya yi parkin, har yagama abinda zaiyi akabashi room key Bahijja bata motsa ba. Dafa kafad'arta ya yi tare da girgizawa kad'an ta bude idanu wanda har suntasa don kuka. Murmushi yasakar mata "Oya fito muje budurwan k'auye mai barci amota."

Salati ta yi gami da mik'a ta dubeshi "Wai har mun iso?'

"A'a tukunna dai. Come out." Ya ja baya tare da had'e rai sabida baison ta kuma jefo masa wani tambayar. Murmushi ta yi ta fito tana bin wurin da kallo cikin k'auyanci. Yana gaba tana biye da shi suka shiga wani babban parlour.

"Zauna anan 'yar k'anwata." Ya ambata cikin murmushi. Kai ta gyada tana k'arewa parlourn kallo. Fita ya yi bai jima ba ya dawo dauke da kedoji manya biyu, ya zubesu agabanta yana kallonta cikin kulawa ya ce "Tashi kiyi wanka, ga kayanan ki sanja sai kizo muci abinci."

  "To Yaya." Ta amsa a hankali.

Fes tafito cikin riga da wando na Pakistan pink da ratsin black ta yi rolling da voile nasa, sai tafito  kamar 'yan Hindustan *Lol*

K'amshi perfume ke fita a jikinta gaba d'aya ta sanza kamar ba ita ba, hatta Bashir yasha mamakin ganinta domin gani ya yi ta k'ara haske, sai ta saje da 'yan birni kamar ba dazun nan take 'yar k'auye ba. 'Lallai tsafta da kyalliya na gyara mutum cikin k'an-k'anin lokaci. Suna cin abinci nata tsokanarta ita kuma tana zuba masa shagwab'a damar da ta rasa a wurin Gwg. Lanti.

Suna gama cin abinci suka fita basu zame ko inaba sai *Mom Aysar beauty saloon* Dake gefen masaukisu.

Ba bata lokaci a kawanke mata sumarta sai kyalli keyi dama gashi da tsawo tare da cika sannan aka wanke mata k'afa tare da yanke mata farce, ai tuni Bahijja ta k'ara sanjawa sosai ta koma 'yar gayu hatta da ita kanta sai kallon kanta takeyi a mirror. A hanyarsu na dawowa masaukin su take tambayar Bashir nan kuma wani gari ne?

"Birnin ilimi kenan k'anwata wato Zaria."

Ta kama baki cike da mamaki ta ce "Ikon Allah dama nanne Zaria? Lallai tacika birni."

Bashir yasa dariya ganin yadda take maganar tare da kama haba "Ai bakiga komi ba k'anwata sai mun isa Kanon dabo sannan kiga birni tare da cikowar muta ne."

Kai ta motsa tare da cewa "To yaya yi sauri mu isa Kanon dan dik nak'osa inga Ummata da yaran dakace ta haifa."

Dariya sosai yasa sannan "Sai zuwa gobe in Allah yakaimu zakiga Umma."

Cikin hanzari ta tareshi "Why Yaya?"

Munyi dare domin da tafiya kafin mu isa kuma ban son tuk'in dare."

"Ok yaya na fahimta."

"Good."

Misalin 10:00pm suna zaune, kallo sukeyi Bahijja ta ce "Yaya kiramin Umman mugaisa."

"To k'anwata 'yan matan k'auye. Ta ke ta batata rai tana tura baki yasa dariya.

"Ga Umman." ya ce da ita sanda yaji alamar an dauka cikin zumudi ta mak'ala akunni tasoma  sallama sannan ta dan russuna kamar tana kallonta ta gaisheta. Mamaki ne ya kama Bashir ganin dik da ta rayu a k'auye amma tana da natsuwar da 'yan birnin basu da shi.

Sosai suka sha hira kamar ba kudi suke ciba domin har Abba da abokiyan zamanta sai da suka gaisa da ita. A k'arshe tamik'a ma Bashir wayan shima sun dade suna magana sanan sukayi sallama.

"Yaya wai me yasa Umma bata tab'a zuwa ganina acan ba?."

Ya yi jim sannan zuwa can ya ce "Tacemin tana tunoki amma watarana kuma sai ta manta dake sannan tana son zuwa wurinki sai wani uzuri yazo ya dauke mata hankali ta manta hatta da Abba mijinta shima yayi k'ok'arin suzo ganinki sai duk su shafa'a sai bayan wani lokaci su tuna. Sun sha sa rana zasu zo amma Allah bai basu damar zuwa ba."

Cikin hawaye take ce wa "Wallahi duk sharrin gwg Lanti ce dama tasha fad'a min wai ni da ganin uwata sai a darul salam inmuna darabon haduwa."

"To ai ba ita ce Allah ba, muguwar banza kawai ai ina shirin zuwa daukoki na hadu da malam akasuwar kwari yana tambayar shagon Alhaji Suleiman mai fata inaji nazo wurin ganin kamar yagaji gashi mutum k'auyene sannan wadanda ke tambaya sai shirme suke mishi, najashi gefe ina mishi tambayoyi yana kallona naji yasaki hailala yana cikin tafa hannaye sai jinayi yana fad'in Kai jinin Bahijja ce tabbas, shin ko kai ne Bashir? Cike da mamaki na amsa eh. Sai ya damk'e hannunta yana murna.

Gida nakaishi bayan ya huta ya sanarmin tun jiya yake yawon neman gidanmu nace ba wanda zaigane kwatancenka dan masu kak'abin fata suna da yasa kuma ba Abba ne kad'ai Alhaji Suleiman ba. Ranar tare muka kwana da shi sun sha hira da su Umma sosai Abba ya sa ke masa.

Kwanarsa biyu muka zo dama yazo menan gida ne sai ya koma ya zo dake a burinsa na ganin kin tsir daga izayar Gwg. Lanti."

"Allah sarki Malam, Allah ya biyasa da Aljanna."

"Amin."

Washe gari k'arfe 7:30am suka dauki hanyar Kano, dik garin dasuka wuce sai Bahijja ta tambayi sunarsa wani yafada mata sunarsa wani kuma ya ce baisani ba.

RAYUWAR BAHIJJA.Donde viven las historias. Descúbrelo ahora