15

240 28 0
                                    

RAYUWAR BAHIJJA.

*15*

Washe gari misalin k'arfe 9:30am akasoma gabatar da taron a harabar makarantar ta *Madinatul Ahabab Rasul* wurin yacika mak'il da mutane Sarakuna da tare 'yan siyasa, hamshak'an 'yan kasuwa da sauran al'umman Annabi sai kuma jigajigan masu masaukin bak'i taron wata malaman makarantar. Wuri fa ya yi masha Allah bakajin komi sai hayaniyar al'umma.

 Taron yayi taro, manyan bak'i sunyi ta gabatar da addu'o,i tare da yabawa dalibai ta nuna tsantsar farin cikin gami da yi musu addu'a tare da makarantar.

'Dalibai sittin da uku aka yaye, arba'in da biyu mahaddata ne yayin da ashirin da d'aya wanda sukayi saka ne.

Bayan gama yawabai na shugabanni da manyan bak'i sai aka soma kiran dalibai suna fitowa d'aya bayan d'aya suna gabatar da karatun Alqur'ani mai girma cikin kwarewa. An fitar da dalibai guda biyar masu hazak'a cikin masu mahaddar hukumar makarantar tabasu kyauta, cikinsu har da Bahijja wacce tazo ta biyu, wani namiji ke gabanta, Sumayya ita kuma ta hud'u tazo.

Su Abba sai murna sukeyi ganin 'ya'yanshi sun zamo abin alfahari burin dikkan iyaye Na gari.

Sai daf da sallar la'asar sannan taron ya tashi kowa ya watse tare da tarin farin ciki musamman ga wad'anda 'ya'yansu ke cikin d'aliban.

A gida kuma Abba ya had'a musu wata kwarya kwaryan walima wacce za'agabatar da ita aranar bayan sallar la'asar.

4:00pm compound din gidan yasoma cika da 'yan uwa tare da abokan arziki. Hud'u da rabi dai dai su Bahijja suka baiyan awurin, sanye suke cikin wani had'add'en material white, d'inkin riga da sket sai suka d'ora bak'ar abaya asamar kayan, faces nasu tasha makeup, dik da Bahijja batason irin kyalliyar amma Adda Asma'u tadage sai anyima mata bayarda ta iya hakanan ta tsaya akayi mata, sai kuma gashi yayi matuk'ar yi mata kyau.

Walima ta k'ayatar sosai, anci ansha an gyatse cikin walwala sai fatan Alkhairi akeyi musu. Sun sami gifts awurin Bashir, Bilal, Mujaheed tare da wasu daga cikin 'yan uwa da k'awayensu. A na kiran magrib akayi yin addu'ar tashi daga walimar don haka wasu dik cikin gidan suka shigo domin gabatar da sallah.

Bahijja ta fito wanka tana shafa lotion Sumy tashigo "Adda B kizo Abba nakiranmu yana parlourn shi."

"To jirani mutafi kawai."

Sun sami Abba tare dasu umma su Mujaheed da Adda Asma'u. Suka sami wuri suka zauna tare da gaishe da kowa d'aya bayan d'aya.

Abba ya umurci Mujaheed yayi addu'a. Addu'a yaja mai tsayi sannan ya cike da fatiha aka shafa. Bahijja baki tasaki tana kallonn sa ganin yadda yake feso addua kamar wani balarabe, har aka shafa adduar bata sani ba dan hankalinta na can wurin kallon Mujaheed, suna had'a ido ya harareta tare da motsa baki ahankaki ya ce "Kallonfa?"

Ta fahimci me ya ce don ka sai ta murgud'a mishi baki itama ahankali ta ce "Shafa kaji."

Ido ya zare yana nuna k'irjinsa ma'ana ni ta gyad'a kai tana mishi kallon uku saura ya hade rai tare da kauda fuska itama kauda fuska ta yi tana murmushi domin taji dad'in ganin tabata mishi rai.

Sumy dake kallon abinda ke faruwa ta lalibi cinyar Bahijja ta manna mata mintsili tayi fuska kamar ba ita tayiba. Ihu Bahijja tasaki tare da mik'ewa tana karkad'e doguwar rigan jikinta tana fadin "Wayyo cinnaka ya cijeni!."

Tsawa Umma ta daka mata "Ke! Natsu bansan sokanci ko intashi yanzu na sab'a miki." Ta ja baya tana matsan kwalla, "Umma wallahi da zafi, diba  kigani har ya tashi wurin." Tana k'ok'arin yaye rigar sama, hannunta umma ta make cikin furta "Kifita idanuna Bahijja ko ranki ya b'aci, inbanda iskanci ina kika taba ganin cinnaka agidannan da zakice ya cijeki? To Allah inbaki shiga hankalinki ba zan makeki tam."

Komawa ta yi ta zauna suna had'a ido da Sumayya ta somayi mata dariya, kauda kai ta yi dan zuwa lokacin ta gano ita ce cinnakan.

RAYUWAR BAHIJJA.Where stories live. Discover now