51

186 17 1
                                    


*51*

Ita ma idanun ta zuba mata kamar a ranar tasoma ganinta, janye nata Bahijja ta yi tare da mikewa zata fice.

"Bahijja!." Badi'a ta kira sunarta cikin  tsawa.

Juyowa ta yi amma takasa d'aga idanu ta dubeta balle ta amsa kiran, sai kawai ta kai dubanta shashin da Sumayya ke zaune tana shayar da babynta nono hankali kwance, jamaa'an d'akin kuwa suka baza kunne da idanu dan sauraren yarda zata kare.

 Kafad'anta Badi'a ta dafa tasoma magana muryanta na rawa "Dole kikasa kallona dama mana Bahijja, sabida kinsan kinci amanata kin gama cutata, kinriga da kingama sanin sirrina a inda nasaki baki ina fad'amiki dan nad'aukeki tamkar 'yar uwarsa Sumayya wanda aure bazai taba shiga tsakanin su ba a she kallona kikeyi ad'age kinacan kina fafutikan auremin miji sannan kuma dan rainin hankali bawanda ya sanar dani sai kawai naji d'aurin auren a sama, to wallahi ba ki isa ba inyi kishi dake ba kuma kisani ni d'aya ce tilo mallakin mijina, ni ce uwar 'ya'yansa kaf don haka basu da 'yan uba, sai kinemawa kanki mafita tun lokaci bai kure miki ba domin mijina ya fi k'arfin ki." Tana kaiwa nan ta tura Bahijja baya ta koma ta zauna tana sauke numfashi da sauri da sauri kamar wacce ta ta yi gudu.

'Dakin yayi tsit kamar bakowa ciki, zuciyar Bahijja inyayi dubu ya b'aci amma kuma takasa yunkurin kare kanta domin tana auna zantuka a ma'auni tare da dora kanta a matsayin Badi'a.

Zuwa can Zarah d'iyar yayan Umma ta mik'e ta nuna Badi'a da yatsa tana mai cewa "Ke!! Matar rashin wata, yi maza ki saita kalaman harshenki akan Bahijja sannan abinda bakisani ba to bude kunnuwarki yau zan sanar dake Bahijja itace matar da mijinki yaso tun talintali amma Allah bai nufa shi zata fara aura ba sai yanzu Allah ya yi ikonsa kinga kenan tsohuwar soyayya ce ta had'a kanta, kuma da kike fad'an ta gama sanin sirrinki yo wani ya ce kifad'ama ko dole ta sa ka ki sai kin fad'a mata? ke kika fad'a mata don ra'ayin kanki ba ita ta nema ta ji ba dan haka can tamatse miki amatse-matsin matsalarki." Ta ja numfashi ta d'ora "kuma ki karaji da kyau a rashin Adda B, Yaya Mujaheed ya aureki sabida mun san komi duka duka watanku uku ana hud'u da had'uwa akayi bikinku kinga tun nan zakigane auren rashin wata akayi dake don haka kisaita kalamanki nacewa bazakiyi zaman kishi da ita ba, dan wannan kam ya zame miki wajibi ki zauna da ita ko kinki ko kinso sai dai inzaki hakura dashi ne ki bar mata kayanta, haka 'ya'ya dole su sami 'yan uba tunda ubanso yaji yagani, ya kasa dauke idonsa akan tauraruwa Bahijja, idan kina da ja tafi ki tambashe ga hanya nan da fatar za ki ju... da sauri Bahijja ta rufe mata baki tana girgiza mata kai "Zarah ya isa haka ko bakya ganin yanayin datake ciki ne dazaki sata a gaba kina fad'amata maganganun masu d'aci haka? Rashin kyautawa dai anriga da anyi mata dan haka ki barta tafad'i duk abinda ke ranta ko hakan zai sata sami sauki."

"Saukin me zan samu Bahijja bayan kin auremin farin cikina to wallahi bazan taba yafe miki ba."

"Ka da kiyafen mana banza kawai." Zarah ta ambata cikin fada.

Bahijja ta tura Zarah waje ta dawo ta tadda Badi'a na kuka Sumayya na bata baki, kuri Bahijja tayi musu da idanu ranta a dagule, taga cikin jikin Badi'a sai motsawa yakeyi sakamakon doguwar rigan da ta sanya na wani material ne mara kauri yabi jikinta ya lafe cikin ya fito sosai kamar watan haihuwarsa ya tsaya nan kuwa watansa na bakwai yashiga, lumshe ido ta yi tana haskowa da yanzu ita ke dauke da cikin.

K'aran da Badi'a ta sa ki shi ya dawo da Bahijja cikin natsuwanta. Tana dafe da cikinta tana kiran sunar Mujaheed ga jini yana bin kafafunta,, a gigice mutanen d'akin sukayo kanta suna kiran "Subbahanallahi."

 Bahijja ce ta kira Mujaheed aiko cikin yan mintoci sai gashi a tsakiyar dakin, d'aukanta ya yi cak ya nufi mota, Umma tabi bayansu a rud'e sabida tasami labarin rigimar abakin Zarah shi ne tazo domin yin masalaha, ta ci karo da su.

 Bahijja ta zube saman gadon mai jego tana sharan kwalla, Sumayya ta dafata tana rarrashinta ta dubi Sumayya idanu cike da hawaye ta ce "Kingani ko sis inta mutu nice sila."

"Baza ta mutu ba Adda B kiyi mata addu'a kawai ba kuka ba."

Kai ta gyad'a ta zame ta kwanta tana mai fatan samun waraka ga Badi'a amma a gefen zuciyarta magan-ganun da Bidi'a ta fad'amata sun tsaya mata a rai sai ta k'ara jin tsanar auren mijin wata a ranta ainun.

Suna isa hospitan d'in dake aiki ma'aikatan suka amsheta da gaggawa sukayi labour room da ita nanma ganin sunkasa tsaida jinin dake zuba mata kuma gashi bata da kuzarin da zata iya haihuwa da kanta yasa suka d'auketa zuwa d'akin theater dan yi mata operation.

Tare da Mujaheed a kayi nasaran fidda Baby girl sai dai ta yi karama sakamakon rashin cika watannin haihuwarta da batayi ba. An killaceta cikin kyalba domin samun dumi zuwa wani d'an lokaci dazata kara kwari.
Maman Baby kuwa an kaita d'akin hutu sai barci takeyi sakamakon alluran da akayi mata bai riga da ya sa ke ta ba.

Umma ce ta ke zaune da ita har zuwa sadda ummanta da Mabaruka yayarta tare da kanwarta mai suna Atika suka iso.
 
Ummansu ce kawai ta gaishe da Umma amma su Atika kuwa iyayen rashin kunya ko kallo Umma bata ishesu domin labari ya je musu na komi a bakin magulmata. Sai harara suke watsa ma umma sannan umman nasu tana kallonsu ta kasa yi musu magana su bari hasalima sai wayancewa ta yi ta hanyar jan Umma da hira wai ita ga 'yar bariki.

*mrs j moon*

RAYUWAR BAHIJJA.Donde viven las historias. Descúbrelo ahora