59

176 11 0
                                    

RAYUWAR BAHIJJA.

*59*

Bahijjace kwance saman doguwar Cushing parlorn Mummy sai hawaye ta ke yi mummy ta sanyata a gaba tana yimata magana a hankali da alama rarrashinta ta ke yi.

Cikin muryan kuka ta ce "Mummy a fitar da shi kawai in huta tunda bai riga yazama halitta ba."

  Cikin taushin murya mummy ta ce "A'a kibar fad'an haka kada mijinki yajiki, kindai san halinsa wata rana hutsune na gaske sannan kuma bakinsan baiwar da Allah ya yi masa ba sannan kila shi ne kad'ai rabonki dan haka kibar tunanin fiddashi, kiyi ta addu'a Allah zai baki lafiya wata rana kiji kamar baki taba shiga cikin laluran ciwo ba."

"Ta mummy nabari Allah yakawo min sauki indawo kamar ko wani mai lafiya."

"Amin." Momy ta amsa cikin shafo fuskanta.

Sumayya ce ta shigo ta zauna kan hannun kujeran da Bahijja ke kwance, ta dubeta cikin gintse dariya ta ce "Mummy Allah kirage shagwabata haka, ace kawai dan yarinya ya yi ciki sai tak'i zama d'akin mijinta inda zata sami lada ninki ba ninki sai ta dawo ta yi ta lankwashewa wai ciwo-ciwo, alhalin kowa ma haka ya yi jarunta ne kawai akafi ta."

 "Kinci gidanku na ce." Mummy ta ambata tare da watso mata dakuwa.

Tana dariya ta kuma cewa "Allah gaskiya na ke fad'a ace tayi ta zama a gida kamar wata mai jego wannan inaga intazo jego sai ta yi yaye kenan."

"Sai ta yi uwaki ne, mara kunyar banza kinzo kin isheta da surutu kamar aku salon ki sanya mata ciwon kai."

  Sumayya ta kwashe da dariya tare da ja baya ta ce "Almuna fun-fun ce ai diyar naki mummy domin ta kosa ta koma gidanta dan d'azun tacemin ta sami sauki kawai langabewa ta ke yi wai bata son komawa bautan aure."

"La'ila ha'illallahu! Mummy wallahi sharri ta ke min bamuyi haka da ita ba Allah." Bahijja ta ambata cikin muryan kuka.

"Nasani bazaki aika ba, kyaleta ta yi rashin kunyarta tagama ba inda za ki koma sai kin kara samun sauk'i."

"Aikuwa dai mummy hakan baida ce ba wallahi a maidawa Yaya da matarsa kawai yau, tunda shi d'in likitane zai iya  kula da ita fiye da ku."

 Dundu Momy ta sakar mata mai kyau wanda saida ta gantsere tare da mikewa tana cewa "Daga fad'ar gaskiya za a illa tani to na yi nan, Allah ya kara lafiya yasa baza kiyi raki yayin labour ba don naga alama baki da juriya ace daga d'an laulayi amma duk kinbi kin langabe kamar wata kagwani."

"Mummy kin jita ko?"

"Kyaleta lokacin tane za ki rama bada jimawa ba.'

Dariya sumyya ta yi tare da yiwa Bahijja gwalo ta fice tana cewa "Yarinya sai dai ki rame in dai Sumayya ce."

"Allah ya shirya ki." Momy ta furta tare da gyarawa Bahijja kwanciya.

"Mummy barci na ke sonyi amma parlourn ya yi min haske."

"Tashi muje ciki ki kwanta."

Ta mik'e mummy ta kamata ganin tana tangad'i kamar zata fad'i. Barci tamu sosai fuye da kullum dan bata tashi ba sai misalin hud'u da kwata na yamma. Wanka ta yi da ruwa mai zafi, taji dad'in jikinta ainun, ta d'auro alwallah ta fito ta zura jallabiyarta na sallah tare ma tsakaicin hijab ta zauna ta gabatar da sallar a zuhur da la'asar bayan ta idar ta yi addu'a sosai tare da rokon Allah yaraya masu abinda ta ke d'auke dashi.

Shafa lotion ta yi da farar powder ta sanya atamfa mai ruwan kwai da digon baqi tayi kyau sosai duk da bawani kwalliya ta yi ba, fuskanta ya yi danye-danye irin dai na masu yaron ciki.

Parlour ta fito inda ta tadda Badi'a da kanwarta Atika tare da yayarta mabruka sunzo duba jikinta.

Da murmushi ta isa inda suke tasa hannun ta amshi little B ahannun Atika ta manna mata kiss akumatu tana cewa "My dear namesy na yi kewarki, ina kiri niya?"

RAYUWAR BAHIJJA.Where stories live. Discover now