61 to 62

375 22 0
                                    

RAYUWAR BAHIJJA.

*61 to 62*

Tafiya yayi mai nisa dan har ta gaji da shirun ta soma tambayarshi inda zai kaita, ya yi banza ganin haka itama sai ta shareshi ta maida kanta gefe tana kallon tsarin gine ginen garin Bauchi.

Hotel ya danna hanci motars, sai da ya gyara parking sannan ya juyo dubeta "Fito muje."

"Ina?"

Bai bata amsa ba  ya bud'e kofar ya zagayo gefenta ya bud'e mata tare da janyo hannunta tayi saurin fizgewa ta ce "Sabida baka kishina shi ne zaka fito dani cikin mutane ba mayafi a jikina?"

  Ya mika hannunsa kujeran baya ya d'auko hijab ya mika mata yana cewa "Dama nasan wata kila in taho dake babu shi yasa nayo guzurin wannan.

  Sanyawa tayi tare da fitowa ya kule motar suka jera harzuwa d'akin daya kama sadda ya iso garin.

  Wanka ya shiga bayan ya tabbatar da ya murzawa kofar key tare da zarewa ya boye sabida gudun ka da ta wuce.

Bai jimaba ya fito ya iso gabanta ya tsaya ta d'ago tana dubansa ya had'erai ya ce "Shiga kiyi wanka."

Itama fuska a had'e ta amsa "Bazanyi wanka a hotel ba."

"Ok tam yayi miki kyau ai, dama nafahimci ni ban isa dakeba shiyasa na ke baki umurni kinakin aikatawa kamar yadda kika sa kafa kika yo tafiya mai nisa tare dayin kwanaki batare da sanina ba in matsayin mijinki, abin iko da ke sama da kowa a duniya."

  Shiru tayi kanta sunkuye haka ya yi ta fad'ansa ya gaji, taki ce masa kanzil.
Abinda ya kuma kona masa rai, ya fizgota daga inda take zaune ya jefata sama bed ya bita ya danne ta yi kara tasoma magana tana haki "Dan Allah yaya jaheed kayi hakuri nasan banyi daidaiba, natuba bazan sakeba kuma wallahi naso in sanar sakai sai mummy ta hanani."

Ya d'agata yana yimata wani kallo wanda yasa tayi saurin kauda fuskanta gefe sakamako ganin tarin fitina acikin idanunsa.

"Mummy take aurenki kenan?."

"A'a ba ita bace amma naga ta isa tayi iko da matar d'anta koda ace bani ba ce danake matsayin d'iyarta."

"Uhmm to yayi miki kyau, amma kisani wannan abinda kika aikata kinjama kanki dan yau sai kinyi kuka a hannuna, shine hukuncin dazanyi miki, in kinso gobe ki kara ni kuma incigaba d'aukan mataki ta hanyoyi kal-kala."
 
Idanunta yaciko da hawaye cikin rawar murya ta ce "Yaya jaheed kayi hauuri dan Allah kabari mukoma gida sannan kuma kaga nabaro Sultan agida kada yayi kuka  a nemeni bana kusa."

"Kinsan Allah Bahijja yau sai naji dad'ina dake, sultan kuma wacce taja mishi sai tayi rainonsa amma tabbas sai na fanshe wulakancin da kika yimin.

Tanaji dana gani yayi ta yamutsata, tayi kokarin jurewa kada tayi kukan da ta fahimci shi yakeson ganin amma ina ta kasa sabida da mugunta keyi mata kuma ga gyaran da tasha wurin mummy ta matse sosai jitayi tamkar ranar yasoma saninsa sabida muguntar da yakeyi mata, tun tanajin  dad'in abin har ta daina, tagaji sosai shi kuma yaki saurara mata. Ganin inta kyalesa zai yi mata illah yasa tasoma had'ashi da Allah da Annabi tana kukamai sauti.

 Janje jikinsa yayi yana maida numfashi don shima yagaji tsaban mugunta ne yasa shi kin d'agata.

  Bayan ya tsarkake jikinsa ya sakai ya fice ko kallon inda take kwance tana kuka bai yiba balle tasaran zai taimaka mat.

Yana fita yasa key ya kulle kofar ta baya yana jin rashin dadin abinda ya yi mata amma in ya tuno hukunta ta ya yi sai ya kauda tausayin gefe.

Wani kukan ta sa ke fashewa da shi cike da matsancin jin haushinsa.
 
Bayan tayi kukanta tagaji ta mike tashiga toilet ta gasa jikinsa sosai sannan tayi wankan tsarki, tafito ta maida kayanta ta gyara gadon tsaf sannan ta kwanta tanajin alamun zazzabi nason kamata. Sultan kawai take tunawa tana share hawaye, ahankali ta furta "Kayi haquri Abbana, Ubanka baida kunya sam bai son kawaici ba sai mugun son kansa ya sani kawai."

RAYUWAR BAHIJJA.Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin