page 28 to 29

165 20 1
                                    

RAYUWAR BAHIJJA.

*28*

A naso ana kaiwa kasuwa. A naso ana kaiwa ka... fass aka taska mata duka abaya wanda yasa ta tsaya cak daga rawa tare da wakar dakeyiwa Bahijja na tsokana.

Mummy ta harareta tare da kamo kunninta ta murda ta ce "Shin intambayeki wai Bahijja kakarki ce ko me? Da kike sanyata gaba da tsokana."

Cikin jin zafi ta amsa "A'a mummy, wayyo zafi mummy nabar tsokanarta daga yau Allah nabari."

Ta sakaketa tare da dankwashe mata kai tasaki 'yar qara "Wayyo mummy zata maidani dak'i-k'iya." Ta ambata cikin sosa kai tare da liliya kunni duk alokaci d'aya.

Bahijja tana gefe tana kwasan dariya har da riqe ciki, ita ma mummy dariyar ta yi a takaice.

"Oya kubiyoni zuwa kitchen yau muna da bak'i."

Suka amsa "To."

Mummy nafita Sumayya ta yo kan Bahijja ita kuwa ta kwasa da gudu batai auneba tajita ta bugu da mutum tayo baya zata fad'i yayi saurin tareta ya maidata qirjinsa yayi mata kyaky-kyawan masauki a k'irjinsa. Kamshin turarensa tagano ko waye, da qarfi ta fincike jikinta tana zabga masa harara, nata shirin magana ta tsinkayi muryan mummy tana cewa "Wai ina ku ka makale ne? sarakan son jiki."

Da sauri taraba gefenshi ta wuce ya rakata da idanu cikin wani yanayi.

 Mummy tana nuna mata aikinta da zatayi Sumayya ta shigo tana kyalkyala dariya "Ke!! lafiyanki kalau kuwa daza kishigo mana kina wannan irin dariya kamar wata kwancen hauka."

Bahijja ta kwashe dariya jin karshen magamar mummy.

Sai mummy tayi shiru tana kallon ikon Allah ta dubesu ta ce "Ina ganin sai annemo muku tai mako, kila kuna da shafan junnu."

A zabure dukkansu suka ce "Wallahi mummy lafiyanmu lau."

"To inkuna lafiya me ke sanya ku dariya kamar bugun almatsutsan saman tsauni?"

 Caf Bahijja ta ce "Mummy dariyan Sumayya ce ya sanyani darawa nima."

"Naji dalilinki, kefa?." Ta nuno Sumayya.

"Ni kam Mummy ganin  Bahijja rungume jikin Yaya Mujaheed shine abin ya sanyani dariya."

Shiru Mummy tayi batare da ta kara cewa komi ba, ta nunawa Sumayya aikinta.

Suna aiki Bahijja na hararan Sumayya ita kuwa sai murmushi takeyi, mummy duk tana hankalce da motsinsu tana murmushi domin yadda suke gudanar da rayuwarsu cikin tsokanan juna na burgeta. A gefe d'aya kuma cikin zuciyarta tana addu'ar Allah yasa Bahijja tazamo rabon d'anta Mujaheed dik da kuwa tana hasko da kamaar wuya faruwar hakan.

Sun fito cikin shirin fita unguwa suna ta muhawara na wanda zai ja motar Bahijja tace "Kibari in kaimu sai ki dawo damu."

"A'a wallahi adda B, naqi wayon salon inzamu dawo kibarni da wahala, alhalin time d'in nagaji."

"OK to mutafi a napep kawai dan ba zan kaimu na dawo da mu ba kina  hakince na zama drivern ki."

"To muje a hakan."

 Suna fitowa bakin gate Mujaheed yana zaune bisa motarsa yana amsa waya, ya dubesu ya kirasu da hannu suka qarasa daidai ya gama wayan.

"Ina zakuje haka?" Ya furta cikin kallon Bahijja yana sauke mata murmushi, tura baki ta yi tare da kauda fuska gefe.

Sumayya ce ta amsa "Kasuwa zamu, kasan next week bikin Nana."

"Wace ce Nana kuma?."

"Ta garin su Bilal, diyar Malam mijin goggo Lanti."

RAYUWAR BAHIJJA.Where stories live. Discover now