page 19

227 19 2
                                    

RAYUWAR BAHUJJA.

*19*

Wurin wata k'aramar motar fara sol sai daukan ido takeyi ta nufa ta bude tayi bismillah sannan ta zauna ta juya back seat ta zube littafan hannunta kusa da laptop d'inta. Horn ta danna zuwa can ta k'ara latsawa tak'i cire hannu dan haka k'aran ya yi ta fita bak'au-k'autawa a guje Sumayya ta fito gyale a hannu tana goge baki da tissue, har ta iso Bahijja bata saki horn dinba, saida ta zauna gefenta sannan ta saki, harara Sumayya ta maka mata "Ai kin kyau tunda kin dimautani da k'ara." Bata tanka mata ba sai da tayi reverse tana shirin fita gate ta ce "Allah daga yau kingama batamin lokaci da shiririntanki, mutum kamar mai nak'udar d'iya mace."

Duka Sumayya ta taska mata acinya tana dariya "Ke fa 'yar buhu ce wato mai nak'udar  d'iya mace ce tafiye shiririta ko me?"

"A'a dalla Malama ba shirita na ke nufi ba dad'ewa, kinsan ance nak'udar mace wai yafi jimawa."

"inji wani d'an ka iyan? "

"Ke ni kam ban sani ba, 'yar jaridan banza kawai da ahegen iya tambaya."

"Aiko you sai kinfadamin a inda kiaji."

"in ank'i fa?"

"Kici na Baki yanzu."

Sai da ta yi dariya sannan ta ce "Bissimillah Hajuya Momu."

Wuyanta takawoma shak'a cikin wasa, ido ta zare  "Ke bar wasan nan kada tsautsayi ya afku kijawa Saraki a Sara."

Tana dariya ta kwanta cikin seat ta ce "Allah yatse afkuwan komi sai Alkhairi kayan Sarakinta."

"Amin my Sumy ta gargajiya."

"Baki da kyau Bahijja ko da kinyi wanka, wato ni ce ta gargajiya."

"To ta turai shi kenan."

"A'a kin manta ta Chinese."

"Kinsan kuwa kuna kama da su wurin k'ananun ido da gajeran hanci."

"Allah ya sakamin."

"Ya dai saka mana."

"Kamar Darling Bash ya ji wukak'ancin da kikayimin."

"K'awalliya, aminiyar, masoyita Sumy affuwan wasa ne fa."

"Ai kin makaro dik dad'in bakinki ba zaimin komi ba."

Dariya ta sanya tare da manna mata mintsili. A haka dai suka isa school cike da shirirta wanda a kullum cikinsa su ke.

Suna zaune k'asar bishiya hira sukeyi bayan fitowarsu lecture.

"Adda B wai ya kukayi da sarakinki akan kiranshi da kikayi Munirat ta d'auka?"

Lumshe ido ta yi san nam ta amsa "Ya kasa yimin gamshesh-shiyar bayani sai kame kame dan haka tun jiya nakashe my phone, nasan yanzu na can yana nemata bai samu ba."

K'uri Sumy tayi mata da idanu batare da ta furta kalma ba.

"Kuma nayanke shawara zan tambayi Maryam inji abinda ke faruwa sabida tun wuri insan matakin d'auka."

"Uhm to Allah yasa kiji Alkhairi"

"Amin."
 
"Amma da zakijj shawarata da kinyi k'o-k'arin cire son Bilal aranki ki kama dahir wanda kika tabbatar da baki da 'yan hamayya ciki kuma...

"A k'ufule ta d'aga mata hannu " Ya isheki haka Sumy, ki rik'e shawarnki dan bata samu karbuwa ba a nan."

"Wallahi Adda B komi zakiyi sai nafada miki gaskiya indai akan Bilal ne, haba ace mutum kamar tsinke dan siranta, amma kiyi ta nacinsa alhalin ga d'an duma duma son kowa k'in wanda yarasa, kin kau da kai a gareshi sabida da rashin tunani." Taja numfashi dik Bahijja na kallonta baki bud'e ta kuma cigaba da cewa "Haba Adda B dan Allah kisanja tunani mai kyau gaskiya domin sam ba ku dace da juna ba."

Tagumi ta yi tana sauraronta har tasa aya.

"Har kingama campaign d'in?"

"Dalla ni bawa ni campaign sai gaskiya kuma daga k'inta hausawa sunce sai b'ata."

"Bakinki ya biki Sumy bazanga b'ata ba a taraiyata da Yaya Bilal, sai dai naga Akhairi insha Allah, kuma kisani konarashi bazan auri Yaya Mujaheed ba sabida bana son... saikuma tayi shiru kana kallon Sumy cike da jin kunya."

"Cigaba da zancenki Bahijja ko kunyar fad'ar kalmar ki kaji? To kibar jin kunya feel free damarki ce." Sumayya ta firta cikin tsare Bahijja da ido.

 Kau da fuska ta yi ranta a b'ace. Sumayya ta mik'e "Bari insamo mana abu mai sanyi." Ta yi gaba abinta batare datajira amsawar Bahijja ba, amma da alama itama ranta ya b'aci.

Ta dawo ta ajiye gwan-gwanin deaw mai sanyi, ta zauna a inda ta tashi tare da bude nata tasoma tsotsa a hankali. Bahijja tayi tsam da ranta cikin tunani sai kuma ta matso jikin Sumayyata ta ce "Sis Sumy kiyi hakuri, rai na ne ya b'aci da zantukanki amma wallahi inason Yaya Mujaheed, so ba irinta ta aure ba  ta 'yan uwantaka."

Murmushi Sumy ta yi "Allah na fahimceki kada kidamu kanki share kawai, dik abinda ya faru ina tayaki murna."

Rungumeta ta yi "Nagode sis da fahimta, Allah bar zumunci."

"Amin Adda B abin dad'in Sarakin ta."

Duka ta kai mata "Baki da kunya Sumy."

"Yo ai kece malamata ko kin manta in tuna miki?"

Murmushi ta yi kawai bata k'ara cewa komi ba sabida ta fahimci hauka take son manna mata.

RAYUWAR BAHIJJA.Where stories live. Discover now