page 6

247 28 0
                                    


 *RAYUWAR BAHIJJA.*

*06*

Yauma zaune suke k'asar bishiyar d'orawa suna cin abin break da suka siyo irin dangin gyad'a, aya, k'osan rogo and so on.

Bahijja ta dubi maryam kad'an ta ce "Dan Allah zanbaki littafan yaya Bilal ki kai mishi, kice mishi na gode ya kuma baki wasu ki kawomin islamiyya anjima."

"Tam kawo insa cikin bag kada in manta."

Ta mik'a mata, maryam tayi k'uri tana kallon books din sannn ta ce "Lallai yaya Bilal naji dake."

"Lamar na me fa?"

Tana tura littafan a bag ta amsa "Da ya baki aron books dinsa dayakeji dasu domin akansu sai da ya doki Munirat don kawai ta d'auka ta karanta batare da ta tambayeshi ba, dalilin dayasa tak'i zuwa hutu kenan wannan term d'in."

Baki Bahijja ta tab'e tare da kauda fuska gefe. "To ai can tamatse mata."

Dariyan zolaya maryam ta sa Ki "Uhmm kedai k'awata kodai kishin ya motsane?"

Tab'e baki ta kuma yi cikin ko in kula ta ce "Kishin wa kuma?"

"Na Yaya Bilal man, sabida naga abu daya kuke aikatawa ke da Munirat, aduk sanda na ambaci sunar daya a gabanku sai kun b'ata rai."

"Ke ni nafada miki bazanyi aure agarinan ba, inkuma yayanki nasona sai ya jira in gama karatuna ya biyoni gaban Ummata cikin gata na."

"To ai shima karatun yakeyi kuma maimartaba yasa mishi gida kusa da makaranta a nan ya ke zaune, gidan mai kyau sanda muka kai masa ziyara na yi ta santin gidan."

"Ah! lallai anaji da yaya Bilal kam."

"Sosai kuwa domin shi kad'ai ne babba namiji a gidanmu, manyan dik mata ne."

"Masha Allah Yaya Bilal magajin sarki."

"Ai kam gashi bai son sarauta."

"Ni ma bai burge ni."

"A she hali yazo d'aya kenan."

Murmushi Bahijja ta yi cikin sosa hanci.

"In mun sami hutu zantafi gidan k'anwar Abbanmu, mahaifiyar Munirat."

"Kai haba?"

"Allah kuwa."

"To Allah yakaimu amma zakibamu kewa kam."

"Nima zanji naku ai."

"Wani gari za ki?" Sai lokacin Nana ta tsoma musu baki cikin hira .

"Zaria."

"Ayya ai ma ba nisa."

"Eh babu, in naje zancewa Munirat Bahijja na gaishe ta."

Murmushi Bahijja ta yi ta mik'e tana cewa "Ban aikeki ba wallahi."

"Sai ko na fad'a dan banga dalilin yin gaba ba."

"Ke ce ke kira muna gaba amma ni sam bata gabana." Tana gama fad'a ta wuce tabarsu.

*
Sun hanyar dawowa gida Nana ta ke cewa "Wallahi inaso inje birni inga irinta, dama ni ce ke Maryam na ke da dangi acan da innatafi bazan dawo ba saina zama doctor Nana yusuf Imam."

Bahijja tasa dariya har tana duk'awa, Maryam ta kaimata duka. "Allah Bahijja ke muguwace bakya dariya sai kinga mugunta kuma abinda baki sani ba dariyan tafi yi miki kyau sabida inkinayi kumatunki duka na lotsaya ciki ga wushiryanki ya bayyana ya k'ara fito da kyawunki, dama zaki tayin dariya fa."

"Tunda gani shafan almatsutsai ba, dole kice inyi ta yin dariya." ta furta cikin waroswa Maryam harara."

Nana ta sanya dariya tana mai maita kalmar almatsutsai.

RAYUWAR BAHIJJA.Donde viven las historias. Descúbrelo ahora