page 13

291 30 2
                                    

RAYUWAR BAHIJJA.

*13*

"Kayan Saraki!! Kayan Saraki!! Wake up."  Sumy ke fad'an haka tare da bubbuga kafadan Bahijja. Ta bud'e ido tare da motsa baki ahankali "Me nene Sumy?." Jin muryanta irin ta marasa lafiya yasa Sumy janye blanket d'in data rufa tare da hawa gadon tana taba jikinta "Adda B bakya da lafiya ne?" Takan kirata da adda intanajin nushadi, kamar yadda su khady ke kiranta.

K'an-k'ame hannun Sumayya ta yi muryanta na rawa "Sis rufeni don Allah, sanyi nakeji, rufeni na ce." Da sauri Sumy ta maida blanket d'in ta rufeta, jansa ta k'arayi ta rufa har saman kanta ta cure wuri d'aya jikinta na kar-karwa.

"Me ke daminki?" Sumy ta ambata tana tab'a jikinta.

"Sis ai komima ciwo yakemin kai, mara da cinyana ta dama kamar zasu bar jikina." Ta k'arasa maganar cikin rawar murya hak'oranta sai haduwa da juna sukeyi.

Fita Sumy tayi da sauri bata ga umma a parlour ba sai tayi part din mummy ko gama fad'awa mummy batayi ba ta wuce da sauri zuwa part d'in umma, nanma kobi takan umman batayi ba  wacce ke shirya break fast akan dinning tashige d'akin Bahijja Sumy ta rufa mata baya. Umma akidime ita ma tabi bayansu tana cewa "Lafiya? me ke faruwa?" Ganin Bahijja ya bata amsar tambayar ta.

A can part d'in Mumy Mujaheed na zaune yana shan tea a dinning yanajin ance Bahijja ba lafiya ya ture cup din tea gefe ya dafe kai ya yi shiru zuwa can kuma ya mik'e ya fice parlourn, d'akinsa ya shiga ya fito d'auke da fist aid box. Babu kowa a parlourn sai ya doshi d'akin da yakejin alamar mutane ciki, sabida shi baisan d'akin Bahijja ba cikin dakunan dake parlourn. Tsaye ya yi a bakin k'ofar yana kallon yadda mummy ke rarrashinta tana share mata hawaye ita kuma sai dafe ciki takeyi tana kuka mara sauti a sannu ya k'arasa shiga d'auke da sallama.

"Yawwa Mujaheed dubamin ita ko da taimakon dazaka iya bata." Bai ce komi ba ya sunkuya yana kallon fuskanta wanda ke rufe sai ruwan hawaye ke zubowa. A 'yan mintoci yagano tana d'auke da zazzabi mai zafi wanda ya haddasa mata jin sanyi sannan time d'in period nata ya yi shiyasa takejin ciwon mara. Ya kamo hannunta ya tsirawa ido, ya yi umurni da tasha tea tukunna, bayan ta sha kad'an ya yi mata Allura yabata magani ta sha bata jima ba barci ya d'auketa.

Bayan sallar azuhur ya shigo parlourn Bashir yasamu yana cin abinci ya k'arasa wurinsa, cikin murmushi Bashir ya ce "Bokan turai yau baka lek'a asibitin ba ne?." Yamutsa fuska ya yi sannan ya amsa "Ban fita ba."

"Ok to bismillah." Ya tura masa plate girgiza kai yayi "Am ok brother."

 Hira sukeyi amma hankalinsa na kan d'akin Bahijja, zuwacan yamik'e yana duban Bashir "Bari in dubo jikin yarinyan can."  Bai jira amsarsa ba ya doshi d'akin. Bashir murmushi ya yi cikin girgiza kai ya mik'e yafice daga parlourn.
 
Barci takeyi har zuwa lokacin, cinyoyinta duk awaje sakamakon  rigan dake jikinta ta tattare tayi sama,  ya ja baya cikin fad'uwar gaba ya tsira mata ido yana k'arewa suranta kallo wani harbawa yaji k'irjinsa ya yi ya ware ido cike da tsoro, ta yi motsa tare da bud'e hannayenta bottoms din rigar ya bude rabin breast dinta suka bayyana har yana hango kan daya da sauri ya sunkuyar da kai k'asa yana jan istiggifari tare da furta "Ya salam!" Sai ya juya da sauri yabar gakin batare da ya kuma kallonta ba.

 Sai daf da la'asar Bahijja ta farka, taji ta saka yau ba inda kemata ciwo sai mara itama kad'an kad'an. Toilet ta shiga sai da tayi brush sannan ta watsa ruwa tagyara jikinta sabida taga period din yazo. Tana fitowa ta sami Sumy zaune a bakin gado tana waya ganin fito warta yasa ta katse wayar ta dubeta cikin kulawa "Adda B ya jikin?."

"Yayi normal sis."

"Haka akeso, Allah ya k'ara lafiya."

"Amin." Ta amsa tana gyara zama a stool dake gaban mirror. Simple makeup tayi amma ta yi kyau na ban mamaki ta feshe jikinta da perfumes masu k'amshi ta dubi Sumayya "Mummy tana nan kuwa?."

"A'a ta fita yanzu amma nasan  kafin magrib zata dawo."

"Ok Allah dawo da ita lafiya."

"Amin."

Umma ce ta shigo rik'e da plate, ta mik'a ma Bahijja. "Ki cinyesa yanzu."

"To Ummana."

Murmushi Umman ta yi ta fice. Suna hira har ta cinye, suka fito parlor suka zauna suna taya Umma kallon program d'in larabawa.

Haka nan Bahijja tasoma jin kunyar had'uwa da Mujaheed gudun kada ya tsokaneta na kukan allura da ta yi, shi kam farbagan da ke shiga ne in sun had'u yasa shi janyewa had'uwar na su.

*
Kwanci tashi ba wuya gashi har su Bahijja sun shiga S.S 3 suna shirin jana jarabawar fita. Cikin nasara suka kammla exams dinsu duka sai adduar samun saka mako mai kyau.

 Tsakani sati biyu dagama exams nasu akasa lokacin yayensu na haddar alqur'ani da suka yi dan haka dik suka kasa zaune sukasa tsaye, shiri sukeyi sosai, ba sa da lokacin kansu dan kullum in sun fita sai yamma suke dawowa sabida karatu da suke badawa domin ana son dikan d'alibi ya karanta alqur'ani sau sittin ko rabinsa kafin lokaci yayen yazo.

Ana gobe taron da yamma Bahijja da Sumy sun dawo daga retouching suka sami yaya Bashir tare da Bilal a harabar gidan zaune suna hira cike da mamaki Bahijja ke kallonshi domin basu jima dayin waya ba amma bai fadamata yana nan ba.  Ko kallon inda suke Sumy batayiba zata wuce Bahijja ta fizgo kafad'arta ta dawo da baya ba shiri.

"Wai Sis me kike nufi?"

"Na me fa?"

Harara ta dalla mata tare da janyo hannunta suka nufo inda su Bashir ke zaune.

"Wallahi ki kiyayeni da son wulaj'antamin Saraki." Ta ambata cikin rad'a.

"In ank'i fa?"

"Zan baki mamaki."

"A kan bare zaki b'atamin?"

"Yaya Bilal ba bare ba ne nasha sanar miki da hakan Sumy."

"To nak'i aminta sai ya ya kenan?"

Wani kallo mai cike da takaici ta cillo mata, zatayi magana ta yi saurin janyota da k'arfi suka k'arasa wurin su.
   

RAYUWAR BAHIJJA.Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang