49 to 50

215 19 0
                                    

RAYUWAR BAHIJJA

*49 to 50*

Kowa yayi farin ciki dajin zancen auren musanman uban gayyan Mujaheed. Abba ya ce abari sai bayan Sumayya da matarsa sun haihu sai a tsaida ranar d'aurin aure da tarewa lokaci d'aya, kowa ya amince saidai hakan baiyuwa  Mujaheed dad'i ba dan shi a son ransa ayi komi a gama a cikin sati biyu, yaso yiwa Abba k'orafi Momy ta tsawatar masa.

Bahijja kuwa wasan buya suka somayi da Mujaheed domin duk inda tasan zasu had'u tana kaucewa zuwa wurin inkuma ya ritsata a lungu da gudu take barin wurin tazamar dashi kamar wani dodo. Shikam dariya take bashi tare da hango yarintarta tsan-tsa.

Badi'a bata san da labarin  Auren ba kuma dan ba wanda yayi mata zancen hatta da shi Mujaheed d'in bai sanar da ita ba sabida gudun halin da zata shiga gata da ciki, su kuwa mutanen gida zatonsu mijinta ya sanar mata.

Bahijja ce kwance a cikin d'akinta waya ta ke amsawa tana kwasan dariya har tana rik'e ciki, Mujaheed ya turo k'ofarfar ya shigo ya tsoge hannayensa rungume a chest nasa yana kallonta cike da sha'awa, ta yi hanzarin cewa "Nana ina zuwa don Allah." Ta sauke wayar tare da mik'ewa tana kallonsa ta gefen ido batare da ta yi masa magana ba, zata shiga toilet yayi saurin kamota ya maidata tsakiyar gadon shima ya hayo ya zauna ya kama kafad'anta  yana matsawa a hankali ta tura baki tana hararansa yatsarsa yasa ya make bakin nata tayi saurin dafe wurin cikin zare idanu, ya motsa kai alamun bata tabbaci ya ce "In kina min tsiwa sai na rika dukanki da gaske ba wasa ba dan yau kin soma ganin zahiri."

Ta had'e rai idanunta suka kawo ruwa cikin k'aramar murya ta ce "Ai kuwa da ka daki auren ka don bazan zauna da maduki ba kuma ka tashi kaficemin a d'aki, ni ban iya rashin kunya ba."

"In anki fa?"

"Sai inyima ihun kato ya shigomin d'aki batare da neman izini ba."

Yq fizgota ta fad'o kansa yasa hannu ya ja zip d'in dake gaban best d'in dake jikinta Allah yasa ta saka bra amma dik da haka sai da kusan rabin na shanunta suka bayyana, ta yi saurin jan blanket ta rufe k'irjinta, cikin matukar fushi ta dubeshi amma dai ta samu kanta da sunkuyar da kai ya yin da idanuwarsu suka had'u cikin sanyin murya ta ce "Kasan Allah Yaya Jaheed inba kadaimin irin haka ba zan had'aka da Mummy."

Shima fuska a daure amsa "Yi maza ki had'anin da ita kuma bazan bar duba lafiyar kayana ba sai dai kiyi duk abinda zakiyi." Ya k'arasa cikin mik'o hannu kamar zai janye bargon ta buge hannunsa tare da nuns masa k'ofa " Malam nidai kafice min a d'aki ko na samu in sarara."

"Ba zan fita ba sai na yi... idanu waje ta tari numfashinsa "Me ka ke nufi?"

Ya matso yana kallon cikin idanunta ya soma jan blanket d'in data rufe kirjinta da shi yana cewa "Bari in nuna miki ki ga zahiri."

Ganin da gaske ya keyi sai ta kalli kara ya yi saurin rufe mata baki da hannunsa, d'ayan kuma yana kokarin janye bargon cizo ta manna mishi a gefen wuya mai zafi amma yaki ko gezau sai dai yabar son janye bargon, hannunsa ya kai yana rufe  bakinta ya soma magana "Kika cije ni ko? to ki rubuta ki ajiye lokaci yana nan zuwa da zan rama kuma kinjama kanki don yau zan bukaci Abba da ya d'auramana aure wani sati, bayan haihuwar su Sumayya sai ki tare, dama haka bikin zarawa yake a d'aura aure bikin tarewa sai wani lokaci to kema haka za ayi ko kya kara samun daman yin gyara da kyau yadda zanji komi yayimin zam-zam." Ya karasa maganar tare da ka kashe mata ido d'aya.

Kallonsa kawai takeyi takasa ce mishi komi ganin haka yasa ya d'ora da cewa "Kuma kisani ni jarumin namiji ne mai matukar kwazo ta ko ina dan haka sai ki zage dantse kizamo jaruma mara lalaci sabida ni d'in ina da bambanci tsakanina da gantalallen tsohon mijinki."

Ita dai shiru tayi mishi zuciyarta na kai komo akan batun auren da ya ambata zaisa a d'aura a wani sati da kuma kalmar bazawara da ya kirata kai tsaye, tunanin abinda zatayi mishi na bacin rai takeyi ko zata sami saukin ci mata fuskan da ya yi amma ta kasa .

RAYUWAR BAHIJJA.Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang