page 14

236 22 0
                                    

RAYUWAR BAHIJJA.

*14*

"Oh kaga k'afafun yawo ba, kuntafi kun shantake kamar baza kudawo ba kunbar bak'i nata jiranku."

Sumayya ce cikin murmushi ta amsa "Wallahi yaya Bashir munsami cikowar mutane ne awurin Amare da k'awayensu sabida bikukuwa yayi yawa cikin wannan satin."

Sai da ya harare ta cikin wasa ya ce "A duba bakin ta." Da sauri ta kai hannunta ta rufe bakin tana dariya k'asa-k'asa. Ya mik'e tsaye tare da dungure mata kai ya sauke dubansa kan Bahijja "K'anwata sai kinshigo inkingama soyayyar."  Ta ja baya tana kare fuska wai taji kunya. Bilal yasa dariya. Tab'e baki Sumayya ta yi batare da tayiwa Bilal magana ba ta bi bayan Bashir da gudu ta kamo hannunsa tana fadamishi wani magana ya kama mata kunni tasoma tsalle bai saketaba har suka bacewa ganin su Bahijja.

 A jiyar zuciya ta sa ki a hankali tana tunanin abin da Sumayya ke nufi da ita naqin kula Bilal alhalin sarai taganshi tare da yaya Bashir.

Hannunta ya jawo yazaunar da ita a inda Bashir ya tashi ya zube hannayensa bisa cinyarta ta bi hannun da kallo tana tura baki da sauri ya janye yana murmushi ta d'ago ta kalleshi ya kanne mata ido d'aya tare da cewa "Princess kin rame kad'an ko baki da lafiya ne?"

Bata amsa ba ta gyara zama  "A she tunsanda maukayi waya kana nan amma kakasa sanar dani." Yatsunsa ya tura cikin sumarsa ta tsareshi da dara-daran idanunta yasaki murmushi mai sauti sannan ya ce "Surprise nayi niyyar baki."

"Surprise kuma? ta me?"

Mik'ewa ya yi yasoma tafiya zuwa inda yayi parking ta biyoshi suka jingina jikin motar yana kallon idanunta "Shiga ciki idanunki ya gane miki."

Ta mak'e kafad'a cikin shagwaba ta ce "A'a nidai fara sanar dani tukunna kafin in shiga."

"No ni dai kitafi kigani da idanunki." Ya ce yana kwaikwayon muryanta cikin rangwad'a kamar mace, dariya tasa shima dariyan yayi.

"Queen wallahi kina da bak'i aciki tun bayan azuhur sukazo don haka tafi kigansu, nasan suma sunk'a-gara su ganki."

Gyad'a kai ta yi "To sai anjuma Saraki." Murmushi ya sakar mata mai burgewa sannan yashiga motarsa, sai dataga ficewarsa sannan ta nufi ciki mai makon ta ahiga part din Umma sai tashige part din mummy don kawai tasami Sumayya taji dalilinta na wulak'anta mata Hubby.

Murza idanunta tasomayi hango Gwg. Bintu zaune da Momy suna hira.

"Taho mana Bahijjan Malam."

Da gudu ta isa ta rungume ta tana kyalkyale dariya.

"Bahijja an girma kai masha Allah."

"Gwaggo wa ya kawo ku?"

"Bilal."

Ido ta ware.

"Bahijja Bilal na k'aunarki da gaskiya bakiga abin arzikin dake aikoma Nana da shi ba dik sabida ke, haka Malam na alfahari da wannan tarayya naku."

Sunne kai ta yi tana kallon Momy ta gefen ido.

"D'iyata ta girma har ansoma zancen aurenta." Momy ta fad'a sadda ta kamata tana kallon ta.

Da gudu ta bar wurin, ta shige d'akin Sumayya. Nam ma Hindu, Nana tare da Maryam ta samu suna hira ya yin da Sumayya ke zaune saman stool tana shafa lotion.

Shiru ta yi a bakin k'ofa tana binsu da kallo.

"Oh wannan shi ne tarban da zakiyi mana." Cewar Maryam.

"Kuyi mata uziri kinsan in tana cikin mayen soyayya bata gane komi sai bayan wani lokaci."

A zabure ta yo kam Sumayya, ta tashi suka soma zagaye d'akin sun Hindu na yi musu dariya, shigowar Momy yasa suka tsaya cirko-cirko.

"Au har ganin bak'in baisa kun natsu ba? To kuzo ku gaisa da Malam, gashi can tare da Abbanku zasu fita."

Hijab dogo Sumayya ta zira suka biyo bayan Momy.

"Alhamdulillah, masha Allah Bahijja ta cikamin burina na ganin kinzamo hafiza, to Allah ya inganta yabama 'yan baya ya kuma fito da miji nagari."

"Amin." Sumayya ta amsa tana mintsilin cinyar Bahijja ganin tana sharan hawaye.

"Nagode Malam domin dik abinda na zama kai ne sila, Allah yasaka maka da alkhairi."

"Amin." Suka amsa a tare da Abba.

Malam ya yi mu su tanbihi akan darajojin Alqur'a tare da falala ga me yawan karantata, musanman su mahaddata wanda nauyin kula da ita ya rataya a wuyarsu ta hanyar yin aiki da ita tare da yin tilawarta.

Sun baro part d'in Abba suna sha kwana Bahijja ta cukume Sumayya idanu waje ta ke dubanta.

"Adda B me na yi kuma?"

"Bansani ba."

"Nashiga uku da mata, wai kuwa bakya da shafan shed'anu?"

"Sai dai na ifritai gareni wanda muka samesu tare da ke."

Dariya ta kubcewa Sumayya.

"Na zama mahaukaciya ko?"

"No Adda B but dan Allah ki sa ke ni wallahi bazan iya da ke ba dan kinsan kinfini k'arfi neman magana ta ce kawai yasa na ke tsokano ki."

Murmushi Bahijja ta sa ki dan ta gano dad'in baki Sumayya ke yi mata kamar yarda ta saba.

"Allah ki kiyaye wulak'antamin Saraki."

"To Adda B nabari Allah ya bar k'auna."

"Amin." Ta ambata tare da sakar mata hijab. Ta yi gaba da sauri ta juyo ta ce "Akan mai kama da carrot kike cukumata to yanzu nasoma adawa da shi domin baku da ce da juna ba."

A zabure ta yo kanta ta kwasa da gudu, dariya Bahijja tasoma 'Sumy kenan ga tsoro ga menan fad'a.' Ta furta cikin ranta.

*
Adda Hindu, Nana, Maryam sannun ku da zuwa."

"Yawwa da fatan mun sameku lafiya." Suka amsa a tare.

"Lafiya lau, ya mutanen garin kwara-kwara?"

"Dik suna gaisheki."

"Ina amsawa."

Daga nan suka b'alle da hiran, inda Hindu ke bata labarin zuwarsu Gwg. Lanti bata sani ba sabida Malam ya ce kada su fad'a mata gudun fitinarta.

"Oh ya rabbi wai har yanzu Gwaggo bata daina jaraba ba?"

"Ai sai abinda ya k'ara, wallahi lamarin na k'anamin zuciya ta yi ta zubda min da mutunci matan gidanmu su yi ta min habaice wai uwata ta zamo matar jaraba annoba wacce tasan darajar aure ba. Ba yarda na iya illa na shiga d'aki na yi ta kuka Baban Amir yana rarrashina.

"Kiyi hak'uri Adda watarana sai labari, insha Allah zai zamo kamar ba'ayi ba."

"To Allah yasa."

"Amin." Suka amsa.

"Bari in watsa ruwa inzo mu d'ora daga inda muka tsaya, abani labarin wanda sukayi aure."

"Ai kam dik sa'anninmu sunyi aure ni da Nana kad'ai ne bamuyi ba."

"Kai haba?" Ta ambata tare da gyara zama.

"Ke dai tafi kiyo wankan sai kisha labarai ba ma labari ba."

"To."

Tana shiga bathroom Hindu ya yi gyaran murya "Amma Bahijja ta yi girma."

"Adda nima tun dazun na ke bjnta da kallo, tazama babban budurwa."

"Kai Nana dan dai bakiga manyan 'yan mata ba ne amma Bahijja bata gama cika ba ta dai soma tasowa." Maryam ta ce tana dariya dan ita bataga girman Bahijja kamar yarda suke magana.

"Ikon Allah gaskiya birni mata suna batsewa kafin akaisu d'aki."

Dariya suka sanya jin abinda Hindu ta ce.

RAYUWAR BAHIJJA.Where stories live. Discover now