page 25 to 26

216 18 1
                                    

*26*

Bahijja ce tsaye a tsakiyar parlour tana kurban tea, tanayi tana kallon agogo, ganin tea din yaki hucewa sai k'onamata harshe yakeyi yasa ta kaishi dining ta ajiye ta koma fice da hanzari  tana kallon a gogon da ke daure a tsintsiyar hannunta na hagu. A cikin  mota ta tadda Sumayya zaune tana jiranta fuska a hade alamun ta jima a zaune. Bude driver seat ta yi ta zauna batare da ta kalli Sumayya ba tayiwa motar key suka fice gate.

Tana kallon titi ta ce "Yau su ooo anyi abinkai, har jirana akayi, ba sa ban ba."

Harara Sumayya ta watsa mata cikin cewa "Kya ce haka mana 'yar rainin hankali, kin kwana soyayya da zuqalallen sarakinki kintashi amakare zakizo kinamin wani borin kunya don latsin hammata."

Dariya Bahijja ta sanya sosai sannan ta amsa "Wallahi sis Sumy komi zaki kira saraki bazan damuba yanzu sabida kema kina tare da abin tsoro kuma fad'i harma ki kara da ihu duniya su jiyoki yes munraba dare jiya muna shan hiran soyayya da habibina shi yasa natashi amakaren sai me?"

"Sai in jibgeki yanzu baruwa na." Ta furta cikin sigar wasa, itama cikin wasan ta ce "To bissillah kayan katon mutum mai taton tumbi."

Dariya Sumy tasa sosai cikin dariyan ta ce "Allah Adda B kina son k'aton mutum mai tumbi sabida akullum inbakiyi zancensaba bakayajin dad'i, to yarinya ina baki shawara da ki bar wani d'an waken zagaye ki fito fili kifad'amin gaskiyan zuciyarki, ni kuwa in mara miki baya ki sami cikar burin ki."

B'arin iska Bahijja ta yi da ita Dan ta gano Mujaheed ta ke nufi, ganin haka Sumayya ta dafa kafadarta cikin son tunzurata ta ta ce "Ok nagane kada kidamu yau zan sami yaya Mujaheed infad'a masa kince yadawo kan dutynsa sabida kingane gaskiya,
zuciyarki shi take muradi sabida ako da yaushe tana cikin begensa sannan gayawan mufarkinsa da kikeyi kullum dare a matsayin miji."

Agigice Bahijja ambaci "A'uzubillahi minal shaid'anin rajin!! Allahumma ajirni da wannan bakak'en zantuntukan naki wallahi
bakinki ya sari bed din barcinki kikoma gida kin gansa yayi rugurugu ba shi da mamora."

Dariya Sumayya ke yi har da dafe ciki, Bahijja taja tsaki cikin k'uluwa ta furta "Muguwa mai fatan alkaba'i."

Sumayya ta tsagaita da dariyan ta ce "Aikomi zakice sai dai kice amma tuni nagnoki da duk wani kwane kwane naki Ba kowa kike burin aura ba sai Yaya mujaheed dan haka kisanima daga yanzu nabar kiranki kayan saraki kin koma sirrin Jaheed d'an duma-duma, sardidi mai 'yammata lodi-lodi amma duk cikinsu Bahee d'insa ke haskawa a birnin ruhinsa."

Tsabar haushin kalaman Bahijja komi takasa ce mata. A haka suka karasa cikin makaranta, Sumayya nata tsokananar ta,ita kuwa tayi mata banza amma jin zuciyarta ta keyi kamar wuta domin sosai maganganun Sumayya yabata mata rai kuma ta kudurta tana komawa gida zata turawa Bilal message akan ta amince ya turo magabatansa, a tsaida lokacin bikinsu tafasa yin degree fin
aurenta zatayi, dama shine darajan duk wata d'iya mace.

*
Mama Yalwa ce zaune a gaban sabon malaminta ta tankwashe kafafu kamar mai d'aukan darasin Allah da manzonsa domin idan kaganta bata da maraba da mai d'aukan karatun addini.

"Malam so ni ke kabimin shi da jininsa ka k'onamin zuciyarsa a allon k'arfe ta yadda zaiji inbai auri Munirat ba bazai iya rayuwa ba."

Malamin yayi 'yan dube dubensa awani bak'in kasa mai kama da toka zuwa can ya d'ago kai yace "Hajiya kiyi haquri ayi auren sabida na gani dole sai sun auri juna amma zan baki wani garin magani ki ajiye ahannunki har sai ana gobe ko ranar d'aurin auren sai ki juba mishi a inda zai taka kuma kizuba mishi awani abinda zaici ko sha, bayan gama bikin kizo inga miza ayi a gaba domin asiri zaiyi wuyar kamasu, sabida dukkansu suna da rikon addini sannan basa wasa dayin addu'ar neman tsari ga kuma iyayensu natsaye akansu dayi musu addu'ar kariya daga abin k'i."

RAYUWAR BAHIJJA.Where stories live. Discover now