60

180 14 0
                                    

RAYUWAR BAHIJJA.

*60.*

Sai da ta d'auki lokaci tana kallonsa sannan ta yi gyaran murya ta ce "Koma katayata shirya kayanta ka d'auketa kutafi can ku karata da rashin kunyarku."

 Kara sunkuyar da kai kasa ya yi yak'i yin motsin kirki ganin haka sai ta mike ta nufi kitchen tana mai cewa "Kunyar gulma."

Yana ganin ta bar wurin da sauri ya koma room d'in. Ta gama shiryawa zata fito sukaci karo ta yi baya zata fad'i ya yi gaggawan tarota ya rungume tsan tsan yana dariya tasaki 'yar kara sakamakon matsan dataji yayi mata. Sakinta ya yi tare da janyo trolley d'inta yasoma zuba duk abinda yasan mallakinta ne. Tsaye tayi tana kallon ikon Allah har yagama had'awa ya rufe ya d'ago yana kallonta fuskansa kamar gonar audiga ya ce "Sanyo hijab mutafi gidanmu."

  A yatsine tace "Wani gida? Nan ma gida ne ko daji kamaida shi?"

  Jan hannunta yayi yana cewa "Bana da lokacin fad'a yanzu sabida nid'in ango ne kinga dole in lallaba kona sha romon cikin natsuwa."

 Harara ta dallawa kyeyarsa kamar idonta zai fad'o, shi kam ko sanin tanayi baiyiba, zumud'i yakeyi tamkar wata tsuntsuwa maisuna marai mai rawan jiki, lol.

Suna fitowa parlourn ya saketa ya karasa gaban Abba wanda yake zaune kan Cushing gefensa na hagu mummy ce zaune d'ayan gefen na dama kuma umma suna magana da alama tattauna wani abun ne su ke.

Cikin fara'a Abba yadubeshi ya ce "Likita bokan turai kuma da alama kazama bokan Momynku sabida katsaya yi mata laku laku to da zatayi ta rike maka mata ne har sai ta yaye abinda zata haifa."

Yana dariya kasa kasa cikin jin nauyi ya ce "Ina yini Abba?"

"Lafiya lau likintan marasa kunya, fafin mummynku."

Ji yayi kamar ya nutsu awurin don kunya barinma da yaga umma na dariya domin yanajin kunyarta tun fil'azal. Can ya tsinkayi muryanta tana fad'in "Rabu da su kaji maza d'au matarka kutafi, ai dama ana shin maidamaka da ita ne kazo kuma maganar gaskiya kayi kokari kusan watanni biyu tana gida jinyar da zata iya yinsa a d'akinta dan kawai sangarta ta taho gida, to Allah ya kara lafiya tare da albarka."

"Amin." Su Abba suka amsa.

Mujaheed ya yi musu sallama ya fice janye da trolley d'inta ya yin da take rakube gefe kunyar ganin su Abba a falon dik ya isheta.

Hawaye tasomayi mummy ce tazo ta janyota jikinta tasoma rarrashinta.
Gaban Abba ta duka ya dafa kanta "Ayi ta hakuri da rayuwa kinji Bahijja?"

Ta d'aga kai sama alamr amsawa.

  "Dafatan ba inda keyi miki ciwo yanzu?"

"Eh alhamdulillah."

"Madallah Allah ya raba lafiya."

Ta yi shiru batare da ta amsa ba.

"Amin." mummy ta amsa.

  Gefen umma ta kalla taga tana murmushi hakama mummy murmushin ta keyi sai ta sauke kai kasa cike da jin kunya. Haka ta taso tana sharan kwalla sabida sosai takejin zatayi kewarsu musanman Momy.

Sun d'auki hanya Mujaheed ya dubeta yasa dariya ta tura baki tana hararansa ya kuma kwashewa da dariya ya buga steering yaso yiwa kansa kirari "Sai ni dodon matana, sai ni mai basu dad'i a tsakiyar dare, sai ni jarumi mai nuna bajinta, sai ni maisa wata yarinya 'yar fara sol kukan dad'i musanman intajita saman k'irjin habibinta."

Kauda fuska tayi tana kallon gefen titi dik da abinda keyi na bata dariya amma ta k'i yi. Haka ya yi ta tsokanarta amma tayi masa shiru harbya gaji ya yi shiru shima.

RAYUWAR BAHIJJA.Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang