page 45

163 19 3
                                    

RAYUWAR BAHIJJA.

*45*

Batasan iya adadin da ta d'auka zaune a wurin ba tasan dai ta jima dubi da yarda ta ke jin zaman ya ishe, jikinta tamkar anyi mata duka, ta gyara zama tare da bud'e data ko zai debe mata kewa, messages din suna gama shigowa ta soma bi tana dubawa yawanci daga kawayenta ne don ita bata shiga group a ganinta rashin aikin yi ne. Sumayya ta kan ce mata yana d'ebe kewa amma sam bai taba burgeta ba dik kuwa daga tana ganin ana adding d'inta a groups wanda ta san aikin Sumayya ce sai dai bata dubawa ta ke ficewa, ta ja tsaki tare da cewa "Ai ko garanarta nan yazo da ace yanzu ina ciki wata kila  da na sami nutsuwar ruji koda da irin su funny stories din nan ne.

Haka dai ta cigaba da bin sakon nin wanda taga dama tayi reply wasu kuma ta dokawa harara ta wuce. Tana shirin sauka taga wani sako da ya ja hankalinta ta bud'e tana kallo baki bud'e sai kuma taja tsaki ta ce " Yar wahala kawai, munafuka da alama ke kikamana k'ullin da ya kaimu ga rabuwa da juna, shi ne dan rainin hankali za ki yimin tambayar rainin wayo to ban sani." Tana gama fadar haka ta mike fuw! ta fice daga garden d'in tana ta zabga tsaki.

 Bakowa ta ke yiwa wannan bala'in ba sai Munirat, wacce tasa alamar firgici a sakon sanna ta jefo mata tambayar 'Aunty Bahijja wai da gaske hamma Bilal ya sake ki?'

Har tashiga bedroom din umma tsaki ta ke ja, ta sami Sumayya na kyalliya bisa lamau bata dad'e da fitowa wanka ba.
 
"Ke da Bilal d'in kunci gidanku ko anyamuku ina da lokacinku ne? aikin banza da wofi kawai." Ta kuma ambata cike da fushi. Ita dai Sumayya sukuti tayi tana sauraren abin kamar almara, wai yau Bahijja ce ke fadan zancen banza akan sarakinta. 'Uhm to ko me ya yi zafi?' Sumayya ta ambata cikin zucci.

Ko kallo inda Sumayya ta ke bata yi ba ta shige toilet wanka ta yi tare da dauro alwalla. Tana zaune saman sallaya lazimi ta keyi kiran Mujaheed yashigo wayarta Sumayya ce ta d'auka ta sanar masa da cewa tana lazimi, ta yi jim da alama sako yake bata zuwa can ta amsa da "To zanfad'a mata insha Allah." Ta ajiye matawayar a gefenta ta zuba mata ido tana son gano damuwarta dan tun jiya bata gane mata ba, ganin bata da niyyar sallamewa yasa ta mike ta fice daga d'akin.

Bahijja bata tashi kan sallayar ba saida ta sallaci magriba da isha'i tare da shaf'i ta bar wutri sai tazo kwanci zatayi.

Sumayya ta lelota yafi a irga tana samun bata idar ba, yanzu ma ta kara lekowan ne taci sa'a dai-dai da ta na nad'e sallaya.

"Allah ya amsa wannan doguwar zama, dafatan dai kinsani a addu'a Allah ya saukeni lafiya, k'uda na barci."

Harara ta watsa mata "Kedai kin bani, baki ko jin kunyan cikin fari."

"Eh banajin abun arziki ne bana tsiyaba ehe."

"To Allah baki sa'a kiyi tayin rashin kunyar."

"Amin."

Murmushi ta yi ta zauna tasoma shafa lotion batare data kara kula Sumayya ba.

"Ke wai d'azun me sarakin ya yi miki naji kina za ki ci gidansu?"

"Ban sani ba uwar son jin gulma."

"Eh mana dan aji zance akayi kunnuwa."

"To sai ki tafi inda masu zancen suke kiyi ta saurara."

"Ke ni maida wukar cikin kube, bani na kar zomon ba rataya aka bani."

"In anki fa?"

Dariya ta sanya "Oh Adda B, yau masifarki ya motsa kenan? To kaina saman wuya."

Ta yi shiru tana cigaba da shafa lotion tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki.

"Yauwa Adda B, yaya Mujaheed yakira ya ce "Kije yana jiran ki a d'akinsa."

"Ki fada masa bazan zo ba."

"A'a kirashi ki fada masa da kanki sabida yanzuma ya kara kirana ya ce lallai fa kizo."

"To banda wannan lokacin, idan ya kuma kiran naki ki sanar masa."

Ta mik'e ta zira rigar barci ta daura zani akai ta sanya huta mai laushi ta rufe sumarta ta madai-daicin hijb wanda ya tsaya iyaka waist nata ta fice.

Sumayya tasa dariya kame da bakinta bayan ta tsagaita da dariyan ta ce "Kai jama'a duniya labari wai mace da mijinta tana kishin wani, au inyi shiru kada tadawo ta ji zancena na kuma samun yayyafin bala'i." Ta kara sanya dariya umma ta shigo ta dubeta ta girgiza kai batare da ta yi mata magana ba sabida tasan ita da Bahijja ce don taga fitowarta rai a b'ace.

Tana saman gadon mummy kwance karatun AL-QUR'ANI ta ke saurare tana kuma bi a cikin zuciyarta idanunta kulle. Cikin amincin Allah nutsuwa ke shigarta, ta tura yatsunta cikin sumarta tana motsa su a hankali tana kuma jin natsuwar ruhi a cikin haka sarkin sata barci ya saceta zuwa birnin ilimi wata Zazzau hhh lol.

Washe gari ta tashi cikin natsuwa ruhi ainun dan kowa ya kalleta zai hango walwala a tare da ita, wanda faruwar hakan ba karamin yayiwa mummy dadi ya yi ba. Cikin kula mummy ta dubeta " Yarinyar mummy yau kinfi kullum kyau da kike cikin walwala."

Murmushi ta yi ta amsa "mummy falalar addu'a kenan yanzu jin zuciya ta keyi babu kawo tamanin cikin dari na damuwar da ta ke ciki."

"Masha Allah sai a kara dagewa dayin addu'ar ka da a gajiya insha Allah ni'imar Allah na ke waye da ke."

"To mummy godiya na ke."

"Ke din tamkar Sumayya na ke dubanki dan kaha babu godiya tsakaninmu."

Gyada kai ta yi tana wasa da yatsunta cikin hasko da ace mujaheed ta aura tabbas da tafi kowa dacen uwar miji."

"Ba saura tunani d'iyata."

"Yes mummy." Ta amsa tare da fad'awa jikinta tana dariya k'asa-kasa, shafa kanta mummy ta yi cike da tausayin ta.

**** ****
'Yan biki sun watse kowa ya koma gidansa anbar ango da Amarya suna  gurzan amarci cikin kwanciyar hankali.

"Adda B ki zo mutafi kinga kowa ya halarta har da yaya mujaheed da yaya Bashir duk sun iso mukad'ai ake jira amma ke kina kwance dan nuna isa."

Juya kai ta yi bata furta kalma, Sumayya ta ja tsaki "Wallahi wannan Bilal din baiyiba da yafito dan sarki, don Allah dubi yarda ya koya miki mulki da wukakanci dik da shi din bai iya su ba, kai tir da wannan rasauta nasu."

Ta shi zaune ta yi ta ce "Ke dalla yanzu ni bata wani abin amai Bilal nake ba, ina tunanin yarda Abba zai d'au maganar ne in angama taruwa."

"Ban fahimce ki ba sister?"

"Wuce mu je parlourn Abba acan zaki fi fahimta amma a ha kikanin gaskiya ina jin tsoro ka da Abba yayi fushi dani dan Umma mai sauk'i ce."

"Wai dan Allah Bahijja me ne ne ke faruwa?"

Ta janyo hannunta "Zo muje kiji kawai mmn twins."

 Suna fitowa su kaci da Mujaheed zaizo kiransu jin sun jima. Wani harara ya watsa musu Sumayya ta yi gaba da sauri ita ko gimbiyar tafiyan tak'ma tasoma tana wani motsa mazaunai batare da ta san tanayi ba.

Da kallo ya bita yana cije lips yarsa wannan kalan jaraba da ya ke bibiyarsa na kaunar matar aure, addu'a ya keyi amma baijin lamarin na yin sauk'i. Siririn tsaki ya ja tare da rufa mata baya, ji ya ke kamar ana ingizashi gareta ya cimmata suka jera k'afafu ta kallesa kad'an ta d'auke kai domin haka nan taji  yana bata haushi.

Cike da jan magana ya yi kasa da voice ya ce "Kina motsa mazaunai a gabana to kisani jiya ba yau ba da na ke raji, yanzu ni kayan Badi'a ce ke kuma na tsukakken d'an fillo nan mara kuzari."

Ta juyo a fusace cikin harbawan zuciya na jin kalmar da ya fito bakinsa, kafin ta furta abinda ke ranta ya yi hanzarin bin gefenta ya shige parlourn yana dariya cike da tsokana.

Dai-daita natsuwarta ta yi sannan ta rufa masa baya.

Wattpad @mrsjmoon.

RAYUWAR BAHIJJA.Donde viven las historias. Descúbrelo ahora