page 37 to 38

152 14 0
                                    

*37 to 38*

Dik ya kosa mummy ta fito su wuce, ganin bata da niyyar fitowa sai ya haye saman motarsa ya  zauna ba jimawa wayarsa tasoma kara ya d'aga da sauri ganin sunan mummy.

 "Ka tafi da wanda zasufito yanzu gida, ni sai gobe zan dawo sabida har yanzu takiyin shiru sai kuka takeyi kamar almatsutsai sun shafeta."

  "Mummy me ye kuma almatsutsai?"

"Junnu na ke nufi."

"Subbahanallah! to Allah ya kyuta, ayi mata ddu'a."

"Shi na ke kanyi mata yanzu haka."

"Allah ya bada lafiya."

"Amin."

"To sai da safe."

"Mu kwana lafiya."

Yana driving amma hankalinsa ya kasa biyu tunaninsa yaushe junnu suka sami Bahijja, yana isa gida ya zarce d'akinsa cike da kasala ga sautin kukanta yaki fita daga kunninsa, alwalla ya d'auro ya hau darduma ya soma nafila bayan ya idar ya d'ora da karatun al QUR'ANI mai girma. Sai da yaji barci yasoma kasmahi sannan yashafa add'a ya kwanta zuciyarsa cike da nutsuwa.

*
Ganin Bahijja taki yin shiru yasa mummy janta suka shige d'ayan bedroom d'in. Jijjigata mummy keyi tana cewa "Wai me ye haka kikeyi Bahijja? Shin aurennan dole akayi miki ko kuwa zabinkine? Da za ki yi ta kuka tamkar wanda akayiwa dole."

Tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya. Mummy ta cigaba "Kin dagulamin lissafi har ina zaton ko junnu kike dashi suke sa ki wannan irin kukan ashe bakomi lafiyanki lau, to kimin shiru ko in saba miki yanzu."

Ta ke Bahijja tayi lamo jikin mummy tana jan hanci tare da dauke ajiyar zuciya, mummy ta d'agota idanunta lumshe ruwan hawaye na zubowa, d'an tsaki mummy ta ja "Sarkin kuka kamar baure kawai."

Saida ta zaunar da ita gefen gado sannan ta kira sunarta "Bahijja." Ts bud'e ido ta amsa "Na'am."

"Me ke damunki?."

Ta yi raurau da idannu girgiza mata kai mummy ta yi "A'a fa ka da kimin kuka, amsa kawai zaki bani domin na hango damuwa cikin idanunki."

A hankali tasoma magana "mummy bansan me ke damuna ba amma daga jiya zuwa yau zuciyata sai bugawa ta ke da karfi tare da jin tsoro na kamani, inaji ajikina wani abu maradad'i zai faru dani sannan tunda nashigo gidannan sai gaban nawa ya tsananta bugawa."

Mummy ta yi sukuti tana sauraren ta, zuwa can ta ce "Addu'a za ki dage dayi ba kuka ba sannan duk inkinji fadiwar gaba to ki yawaita istiggifari tare da fad'an lahaula wala kuwwata illa billahil aliyil azim, zaki sami sassaucin dik kan lamarin."

"Tam mummy zan dage da fad'a insha Allahu."

"Da kyau d'iyata."

Murmusawa Bahijja ta yi cike da alfaharin da ita.

Robar fresh milk mummy ta d'auko tare da cup ta zuba mata ta sha, a kallah sai da tasha kusan kofi uku sannan ta ce "mummy nakoshi."

Tana jingine jikin mummy ta yi k'asa da murya tavce "Mummy dik bugawan da na ke ji zuciyata na yi to ba kowa ke fadomin a rai ba face yaya mujaheed, wallahi daga jiya zuwa yau na tunoshi yafi ba adadi, kuma narasa wannan dalilin faruwar hakan."

 Tsawon lokaci mummy ta d'auka shiru kamar baza ta ce komi, zuwacan taja numfashi tana kallon Bahijja ta ce "Sonshi kikeyi shine yahaifar miki dajinsa aranki amma kisani dik yarda zakiyi to kiyi ki fiddashi aranki sabida ke d'in yanzu matar aurece yin haka zaisa ki d'aukanma kanki zunubi babba, kuma ka da ki da ke kiyi sanar da wani wannan zancen domin mutanen kirki sunyi wuya dai su nemi had'a miki fitina da mijinki."

RAYUWAR BAHIJJA.Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin