page 16.

210 27 0
                                    

RAYUWAR BAHIJJA.

*16*

Hawaye  tasoma sharewa dan taji zafin mintsilin, mumny ta janyota jikinta ta kwantar da kai saman cinyarta tana kallon Mujaheed wanda ke ta murmushi da alama ya yi farin cikin ganin hawayenta, tura baki ta yi tana share fuska. Abba ya yi gyaran murya duk aka natsu yasoma magana "Alhamdulillah ala kulli halin, lallai yau muna cikin farin ciki a karo na biyu masu kama da juna, munyi ta farko kamar wannan sanda Mujaheed ya had'a haddarshi to gamu cikin ta biyu, muna fatan samuwar ta uku har ma da ta kasa irga." Ya ja fasali sannan ya d'ora Bahijja da Sumayya kun sanyamu cikin farin ciki mara misaltuwa sakamakon haka watanni kad'an masu zuwa da ku za'a sauke farali ma'ana aikin hajji."

Kabbara d'akin ya d'auka sai kuma akasoma yiwa Abba godiya Sumayya da Bahijja kam baki har kunni anata murna zuwa can Abba yayi gyaran murya aka saurara.

"Abu nagaba kuma shi ne, ina son sanin ra'ayinku, shin zaku cigaba da karatu ne in sakamakon ku yafito ko kuwa aure kuke so?"

Tsit parlourn ya yi na tsawan wani lokaci zuwa can Bashir ya katse shirun da cewa "Ita dai Sumayya zata fara karatu, inta kai kamar shekaranta ta biyu sai tayi aure ta cigaba ad'akin mijinta."

Abba yasaki murmushi "masha Allah hakan ya yi kuma Allah yanuna mana lokacin lafiya."

"Amin." Su Momy suka amsa.

Abba ya sauke dubansa kan Sumayya ya ce "Dawa kuka dai-daita? ko sai lokacin yayi zaki fitar dashi?"

Ta sunne kai tana murmushi ta nuno saitin Bashir da yatsa. Dik aka zubawa Bashir idanu, ya sunkuyar  da kai yana shafa kyeya. Abba cikin murna ya ce "To Alhamdulillah abu yayi dad'i tunda kun had'a kanku muna murna da hakan Allah ya kaimu lokacin lafiya."

"Amin."

Bahijja ta matso ta sakarwa Sumayya dundu a baya sannan ta sa hannu dana k'ok'arin d'ago fuskanta da ta sunne a laps nata.

"Bahijja kina son ranki ya b'aci a parlon nan ko?" Cewar Umma.

"Yau dai da takurawa d'iyata kika tashi, ko ina ruwanki da shirginsu."

"Ba haka ba ne ta natsu ne ban son abinda ta ke yi."

"Ni ban ga abinda ta yi ba."

Kallon matan nasa Abba ya yi ya girgiza kai yana godewa Allah cikin ransa da ya had'a masa kansu.

Bahijja ta yi k'asa da murya "Gulma wuya d'ago ki kalli kowa domin nan ba bare ciki da kike wani soke kai kamar bushiya."

Buge mata hannu ta yi ta dago tana cillo mata hararanta, Dalla ni kikyaleni, mutum yanajin kunya kinzo kina damunshi da surutu kamar akun kuturu." A kasa dariya harda Abba. Sumayya ta kuma kulle fuska domin bata zaci maganar ta fito fili ba.

"Nadawo gareki Bahijja." Abba ya ce ta gyara zama tare da gyad'a kai.

Waye gwanin ki kuma kina da burin karatun ko a'a?."

Ta sunkuyar da kai ahankali ta ce "Ni kam Abba ina son inyi karatu mai zurfi kafin maganar aure, inson samune sai na had'a Degree d'ina sannan maganar ya taso kuma ga me da miji, na tsaida yaya Bilal."

Daram!! K'irjin Mujaheed ya bada sauti jikinsa yasoma rawa sam bai zaci zata kawo maganar Bilal ba sabida yasha jin tana fad'in ita baza tayi aure yanzuba karatu zatayi, jin haka yasa bai gwada nuna mata shima yana ciki da gaske ba, manufansa sai ta kusa kammala karatun sai ya bayya mata kansa dik kuwa da yasan tana tare da Bilal dan  a tunaninsa Bilal shadow ne kawai.

Can yajiyo Abba nacewa "Aina shi Bilal d'in yake?."

Mummy ce ta amsa "Alhaji yaron Sarki Ahmadu Rufa'i ne abokin Malam."

Shiru yayi zuwa can yace "Oh yaronnan mai yawan zuwa wurinta kenan? Dan fillo mai hankali."

"Eh shi ne Alhaji."

"Ok zan nemi Malam sai ya bincika mana maganar wurin mahaifansa."

Shiru ba wanda ya tanka har Momy. Murmushi ya yi dan ya hango wani lamari, ya gyara zama ya dubi Mujaheed wanda duk ya had'a uban zufa kamar ba ac a parlourn.

"To kai fa?, me ye labari ga me da wacce ka fitar."

Kallo ya k'ure Bahijja dashi wanda yasa gabanta fad'uwa yana dukan 100~100 hhhhh lol.

"Ina saurarenka." Muryan Abba ya dawo dashi tunanin da yafad'a.

  Da kyar yasaita kanshi cikin dakiya ya ce "Abba Labari na wurinta."  ya nuno Bahijja da fuskansa a had'e, ta zabura ta matsa jikin Adda Asma'u bakinta na rawa ta ce "Ni kam kada kasani a garejin hak'ora arasa mai taunani, wallahi kadai memo mai adana bayanenka can amma bani ba da bansan komi akai ba." Sosai tabawa kowa dariya a wurin, gogan kuwa ko murmushi baiyi sai wani haderai yakeyi yana watso mata harara.

"To ya isa nagano ba bayani agareka dan haka inajiranka bada jimawa barci domin tare zan aurad daku da k'annin ka."

Kai ya gyada yana sauke ajiyar zuciya, ya saci kallon Bahijja ta dalla mishi harara ta motsa baki ahankali "Mugu kawai." Murmushi ya yi domin sarai yagano me kirasa. Ganin ya k'i cewa komi Abba ya umurci Bashir ya rufeta tarom da addu'a.

Fruits da aka yanka aka umurci kowa yad'ebi yadda yakeso, Sumayya ta cika wani faranti mai fad'i tafice zuwa kaima su hindu.

Sun baje sunata shan abinsu sannan suna hira cikin nushad'i Bahijja ta koma gefe ta zauna shiru, cikin tsokana Sumayya tace "Uhm Ku karkad'e kunnuwarku kusaurari  labaran duniya wacce Ni Sumayya zan karanto muku."

"Muna saurarenko." Suka ambata a tare. Sai da tayiwa Bahijja gwalo afakai ce sanna tace "Aha yau wata yarinya ta fada tarkon k'aunar mazaje guda biyu, daya mai wuyar rak'umi daya kuma tubar kallah masha Allah, to ku aganinku waza ta zab'a cikinsu?"

Nana ce ta amsa "Ga d'an tuma-tuma tubarkallah me zatayi da mai siffan rak'umi."

Ai kamoSumayya tasa dariya har da ruk'e ciki, suma dariyan sukeyi gano Bahijja ta tsokana.

Tsaki Bahijja taja tana hararan su "Iska dai na wahalar damai kayan kara." Ta furta sai kuma ta bar musu parlon ta fice zuwa part din Momy, tana sanyo kai Mujaheed na fitowa parlourn zata koma da baya cikin zafin nama ya fizgota ta bude baki dan fasa ihu ya rufe bakin da hannunsa, yajata zuwa d'akin Sumayya ya tura k'ofar sabida yasan Momy bata cikin parlorn.

RAYUWAR BAHIJJA.Donde viven las historias. Descúbrelo ahora