page 9

224 29 0
                                    

RAYUWAR BAHIJJA.

*9*

Siyayya sosai mummy ta yi mata, sun d'auki a k'allah 3hrs acikin kasuwar sannan suka fito. Zaune cikin mota suka sami Muhaheed yana sauraron karatun AL-QUR'ANI muryan sheik Manshawiy yana fita cikin suratul TAUBAH.

Yana driving yanayin k'orafin sun dad'e, mummy tayi masa dak'uwa "Gidanku na ce sarkin wutar ciki."

D'an murmushi ya yi tare da duban Sumayya yanayimata magana k'asa k'asa sukasa dariya.

"Gulmanmun banza kawai." Momy ta ambata.

 Shiru sukayi dukkansu suna sauraren karatun wanda Bahijja ke bi ahankali, ta kwantar da kanta jikin mummy ta lumshe idanu.

Mummy tana kallonta tana murmushi a ranta tana mamakin yadda ta iya karatu haka alhalin tana k'auye, sai kuma ta tuno mijin gwagwgonta ai limami ne, Don haka ba abin mamaki ba ne don tasamu ilimin addini. 

Mujaheed ya saita mirror saitinta sosai yana kallon yadda d'an k'aramin bakinta ke motsawa ga idanunta a lumshe sai eyelashes nata suka kwnata zara-zara, haka gaban goshinta nan ma suma ne kwance luf luf, alamar tana da wadatacciyar suma akai. Baisan sanda yasaki murmushiba ya sa hannunsa yana sosa sumar kansa yana cigaba da murmushi.

Ajikinta taji ana kallonta, tako bude ido tar ta saukeshi akanshi, ya sakar mata murmushi ta daure fuska tana hararanshi saikuma tayi shiru ta bar bin karatun amma tana yi cikin ranta.
Mummy ta dubeta cikin kulawa "Cigaba mana Bahijja, muryan tanamin dad'in sauraro."

"A hankali tajuya fuskanta tana kallon titi, tacigaba da karatunta. Sumayya kam kwantawa tayi tana son yin barci sabida ta gaji sosai.

Saida suka biya shagon telarsu suka bashi ya dinka mata kayan sannan suka isa gida.

*
Abba yasa Bashir ya yi mata registration a makarartan hadda wacce take hade da islamiyya, tasoma zuwa tare dasu Sumayya. Ta maida hankalinta a karatu sosai, sannn tana taimakawa k'anninta wurin koyamusu karatu tundaga na islamiyya zuwa na boko, shi yasa sukayi shak'uwa dasu.

Zuwa yanzu Bahijja anzama 'yan gida, ta saba da kowa na gidan, kowa agidan na sonta domin tana da shiga rai, ga ladabi da hankali, Sun shaqu da Sumayya sosai, haka mummy, komi tasamu sai tace Bahijja amsa Sumayya tayi ta k'orafi, wai tafi son Bahijja ita kam dariya takeyi mata intaji haka. Mummy tayi ta k'ara tunzurata har sai tayi fushi ta tafi part din umma, itama acan umma zata karramata, tayi tama Bahijja kwalo. Haka suke rayuwarsu abin sha'awa da burgewa, sam iyayen nasu basa nuna kishi nan na hauka wanda ke hanyo rabuwar kan d'iyoyi.

Kaf gidan  Mujaheed ne kawai basa wani shiri da shi, dan haka nan yake bata haushi dan ko hira takeyi dazaran yazo wurin zatayi shiru haka in nushadi takeyi da ta hangosa zata hade rai tabar fara'a. Haka kawai,sam jininsu bai had'uba.

  Shi kam dariya take bashi sosai intana cin magani kuma duk bata ranta dazatayi inyaso sai yajata da fada kawai don yaji muryanta sabida shikam muryan ta nayi masa dad'i, a hankali yake fita koda kuwa fad'a takeyi, shi yasa ke yawan janta fad'a inda ke cemata budurwan k'auye ita kuma bataso sam, shi yasa bata damu tace mishi yaya ba sai dai in agaban su umma ke nan kam zata natsu dan gudun fad'ar Umma.

 Sanda aka koma makaranta Abba dakanshi yagama komi na karatunta, ya nemi abarta ajin da take ss1 dama ajin daza shiga kenan, sunce sai sunmata interview. Mujaheed yakaita, yasha mamaki dayaga ana tambayarta tana watso amsa bako gargada. Gashi turancinta mai kyau, da dad'in saurare, su kansu malaman sunji mamaki tare da yabama kwazonta kamar ba makar government tayiba. Atake suka bata aji ss1 science.
    
Ahanyarsu nadawowa yayi tajanta da hira tayi mishi shiru ya k'araci surutunsa bace dashi cikan kala ba. Hasalima ita haushinsa takeji  agefe daya kuma zuciyarta tafad'a kogin tunanin Bilal d'inta.

*mrs j moon*

RAYUWAR BAHIJJA.Where stories live. Discover now