page 21

406 26 8
                                    


RAYUWAR BAHIJJA.

   *Na Mrs j moon (Safiyya.)*

*21*

"Bahijja."

"Na'am Abba."

Ya muskuta kad'an sannan yasoma cewa "Yayanki Mujaheed yaxomin da magana akan kun had'a kanku har kin amince da ahada bikin tare danasu Bashir, shi ne nakiraki inji daga bakinki, shin kun had'a kan naku ne da gaske?"

Shiru ta yi kanta sunkuye tana wasa da yatsun hannunta. Tsawon wani lokaci taqi cewa komi. Abba ya kuma dubanta cike da kulawa "Bahijja kada kiji komi kifad'amin gaskiyan zuciyar, bazan miki auren doleba, domin ke amana tace dan haka abinda kikeso shi ne zab'ina."

 Nanma har ya dasa aya batace komi.

"Oya matsonan Bahijja." Ta miqe ta isa kusa dashi ta zauna ya dora hannunsa sama  kanta  "Shirunki yanuna alamun amincewa kenan."

Ta girgiza kai ta yi da sauri."

"To fad'amin abinda keranki kinji."

Ahankali tasoma magana "Abban Allah ni bamuyi wata magana dashi ba kuma ni ai da yaya Bilal mukayi alqawarin aure."

"Ok."
Ta k'ara yin k'sa da murya "Abba don Allah kayi haquri baqin jininka nakeyi ba kawai ina son cikawa Yaya Bilal alk'awari ne." Ta kai qarshen maganar cikin kallon Mujaheed ya dallo mata harara cikin dakiya ta cw da shi "Kaima Yaya Jaheed don Allah kayi haquri ka tayani ganin wannan alk'awarin ya cika."

Wani kallo yawatsa mata ta kauda kai tana kallon Abba cikin fuskan tausayi.

"Bakomi Bahijja, bakiyimin komi ba, ai matar mutum k'abarinsa, Allah yayi miki albarka ya tsareki ga duk abin k'i, Allah ya taimaki rayuwarki yasa Bilal ya zame miki mai amana kamar yarda kika rik'e masa."

"Amin." Ta amsa tana murmushi jin dad'i.

"Tashi kitafi abinki magana ya kare."

Abba ya umurceta, tafice da sauri tana hardewa sakamakon mugun kallon da mujaheed ke watsa mata.
  
"Kai kuma bani hankalinka nan." Maganar Abba yadawo dashi kogin tunnin dayafad'a. Motsa yatsunsa yayi sukayi qara yana duban Abba fuskansa ba walwala, ya kada kai alamar yana tare da Abban.

 "Ina son kacire ranka akan Bahijja, kanemi wata sabida tana da zabinta kuma ni bazan tursasata tasoka doleba, innayi haka nazamo azzalumi don haka nake umurtarka daka janye qudurinka na son kuyi aure, kanemi wata insha Allah kana tare da nasara."

"To Abba nagode Allah yaqara girma, na janye insha Allah."

"Madalla, Allah yayi maka albarka."

"Amin Abba."
  
Cikin dibara Abba ya yi ta jansa da hira har ya sa ki jiki daganan suka fad'a hiran business tare da maganar gina wani company na sarrafa abincin yara  har Bashir yashigo  shima yasoma bada nashi shawaran akai.

***
"Mama wallahi Allah nagaji da abinda hamma Bilal keyimin." sai kuma tafashe da kuka mai tsanani.

 "Munirat!." Maman ta kirata cikin bud'e murya bata amsaba sai dai ta tsagaita da kukan tana sauraron  ganin haka yasa tacigaba "Wallahi Allah indai ni hajiya yalwa mace ta haifeni sai kin auri Bilal kuma ke d'aya zaki zauna tare dashi har abadan abidina.."

Da hanzari Munirat ta dubi maman idanu waje ta ce "Mama zaki iya hanashi auren Bahijja ce?."

"A'a baruwana da wata Bahijja can, kuma bazan hanasa aureba amma zai soki kamar ransa kuma zai aureki dolensa sannan ke kadai zaki mallake shi, bazan bari kizauna da kishiya ba kamar yadda nake ni d'aya to kema doke kizamo kedaya awurin mijinki."

  Ta zubawa maman ido, zuciyanta namata d'aci ta ce "Uhmm mama don Allah don Annabi kada ki shiga malamai da 'yan tsubbu domin nemomin so wurin hamma Bilala."

Harara ta watsa mata "Sai kiyi kuma amma wallahi duk inda zanshiga sai nashiga naga kin auri Bilal"

Cikin bata fuska Munirat ta ce "Wallahi nahaqura dashi tunda ya fadamin yana da zabinsa kuma bazai iya yimata kishiya, to nayanke shawara zan fidda d'aya daga cikin masu sona in aura domin hakan zaifimin kwanciyar hankali akan na auri wanda baya yi dani sai don tursasawa."

  "Wayace miki tursasashi za ayi? To kisani da kanshi zai tako yace yana buqatar aurenki ido rufe."

"kai mama ana ga Annabi kina runtse ido, nifa bansonki da yawon bin malaman nan ne."

Cikin fushi ta amsa "To uwata! Sai nabi inkin isa ki hanani ingani, wawiyya kawai!."

Munirat ta miqe cikin fushi ta nufi hanyar barin parlorn tana cewa Waallahi indon ni zaki fad'a halaka to kisha zamanki, bana son hamma Bilal yanzu kuma Baba nadawowa  zan fad'a mishi zab'ina." Tana gama fad'a ta fice.

Mama yalwa tabita da wani mugun harara  "Zanci qaniyarki kuwa dagake har uban naki." Sai ta mik'e ta figa gyale tare da daukan key din mota tafice a fusace tana cewa "Da Zafu-zafi ake bugun dutse, bari insoma cin uban wanan mai dogon wuyan tukunna kafin indawo kanki 'yar banzan yarinya shasha kawai."

 Munirat tanajin tashin motar wasu sabbinhawaye masu radadi suka zubo mata ta share da bayan hannunta, ta daga hannayenta sama ta ce "Allah yashirya mahaifiyata hanyar gaskiya ka nesanta zuciyar ga bin aikin ashsha, yasa tagane gaskiya,Amin."

 Kwantawa tayi bisa bed dinta tare da dafe kanta dake barazanar rabewa biyu sabida tsananin ciwon dake mata.

*** Bahijja tun lokacin tasoma wasan buya da Mujaheed. Taqi barin ko hanya yahadasu sam da ta hangoshi zata arce da gudu, ganin haka yasa ya maida part dinsu wurin yin break dinsa da kuma dinner, yasan duk tsiyanta tabari su hadu domin hakik'anin gaskiya yakasa cire sonta aranshi duk da nasihan da Abba tare da Sumayya sukeyi masa na yahaqura da ita, shiko Bashir cewa yayi ya sauke isa da gadara yanemi so da qauna awurinta zaifi masa, jinsa kawai yayi amma yana ganin zubda ajine ya soma lallamin qanwarsa wai ta soshi.

  Da sanyin safiyar littini Mujaheed yashigo part din umma kamar yarda ya saba, dinning ya nufa yana kallon agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa. Tea yahada yasoma kurba ahankali yana kallon k'ofar d'akin Bahijja.

Tsam yayi yana sauraron motsin da akeyi a cikin kitchen,  sai yasami kanshi da addu'ar Allah yasa Bahijja ce ke ciki. Yana shirin tashi ya tafi domin sauri yakeyi yana da operation qarfe tara na safe yana son isa cikin lokaci. Fitowarta yasa ya dakatar, ta iso hannunta dauke da plate d'in indomie sai tururi yakeyi tare da tashin qamshi.

Bata lura da mutum a tsayeba sabida kanta na kallon plate din, tana motsa shi don yayi saurin hucewa. Shiko da ke aikin kallonta ya runtse idanunsa cike da jin tashin tsigan jiki. Dan sanye take cikin night wear wacce tabi jikinta ta lafe sannan tsayinta ta wuce gwaiwanta da kad'an, gashinta sanye cikin net. Yaja ajiyar zuciya mai qarfi, da hazari ta d'ago tare da tare da neman hanyar gudu yayi saurin yin bake bake a hanyar dazatabi yana qarewa surarta kallo ya ce "kingama wasan b'uyan?"

Ta ja baya da sauria tare da watso masa harara kuma ta d'ora hannayenta ta kare qirjinta

Murmushi ya kuma sa ki mai sauti sannan ya matso kamar zai rungumeta ta zaro idanu waje.

RAYUWAR BAHIJJA.Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon