page 11

268 29 0
                                    

RAYUWAR BAHIJJA.

*11*

  "Mujaheed!." Ta ambaci sunarsa da k'arfi.

Gyara tsayuwa ya yi yana cigaba da k'are mata kallo, juya masa baya ta yi cike da jin haushin kallon.

Murmushi ya sa ki mau sauti ganin aninda tayi cike da jan magana ya ce "Oh dubeta wai ita nan ta soma girma ahakan kwaila,kwanso kuma bera."

Juyowa ta yi ta kallesa ido cikin ido bata ce dashi komi ba ta sunkuya ta kwashe books dinta da hular kanta  wanda yafad'i k'asa sakamakon razanar da ta yi. Saida ta rungume littafan sannan ta dubeshi sama da k'asa, duba mai d'auke da raini ta ce "Amma dai girma ya riga hankali zuwa, anyi girman giwa ba wayau domin kaza tafita komi dukda tarin k'an-k'antarta." Ta yi shiru tana kallon yadda ya d'aure fuska sai ta sa ki murmushi ganin ta yi nasaran b'ata masa rai.

"Kaya dai nawa ne, ba zubewa su naske ina ruwanka kuma ba nuna ba tafasa ne basuyi ba, na mamajo kawai sarkin sa'ido to kasani dai Bahijja kwalelenka inma kana ciki ne akai kasuwa." Da mamaki yake dubanta ita kanta ta sha mamakin tsiwar da ta tsaya gabansa ta yi masa.  Bata ankaraba taji ya d'alle mata baki da yatsunsa biyu tasaki ihu tana liliya wurin, idanunta suka ciko da kwalla, ja baya ta yi.

"Wallahi Jaheed in baka fita anyata ba zan had'aka da Abba, azzalumi kawai kuma nabarka da mai duka."

Cikin fushi ya matso ta kuma ja baya zata gudu ya rik'o hannunta ya murd'a da k'arfi tsuwwan azaba tasa ta watsar da books din hannunta, kici-kicin son kwace hannunta ta keyi ya ta ke k'afarta da covershoe.

"Ya ilahil Alamina!." Ta ambata akidime, ganin baida niyyar rabuwa da ita sai ta sunkuya tana jan k'afarsa, amma yak'i motsawa.

"Don girman Allah yaya Mujaheed kayi hak'uri na tuba, ba zan k'ara ba."

Saida ya murzasu sannan ya d'aga yana sakin wani murmushi mai cike da k'asaita.

Harara ta watsamishi ta mik'e ta k'ara tattara littafanta ta juya tabar wurin tana sharan hawaye. Tarasa gane me yasa Mujaheed keson takurama rayuwarta, duk son kauce mishi da takeyi amma sai ya nemota yajata da magana.

Bayanta yabi da kallo har da shige ciki ya cije finger "Kai amma yarinyan can tasameni da yawa wato ni ta kira namajo, zan nunamiki aikin namajo kuwa inhar baki shiga hankalinki dani ba." Sai ya yi k'asa da murya kamar mai tsoron ka da wani yajiyo abinda zai fad'a. "Hak'i-k'a yin fada da ke nasani nushad'i Bahijja musanman sauraren k'aramin muryan ki mai sanyi dake jefani cikin natauwa." Yana gama fada ya yi hanzarin waigawa sai kuma ya tab'e baki yana wani yamutsa fuska, ya fice ta k'ofar baya zuwa waje.

"Yaya mujaheed dazun yazo nemanki, ina kika shiga?"

"Cikinki na shiga!."

"Tofa hajiya maida wuk'ar daga tambaya sai cibi yazama k'ari."

"Kunama ce."

"Yau naboni da mata, me ke daminki wai?"

"Shafa kiji."

Shiru Sumayya ta yi tana kallonta, ita kam tana ta rubutunta ko duban inda Sumayya ke zaune batayi ba. Haka nan takejin haushin kowa dik sabida Mujaheed.

Washe gari Mujaheed ya sauke su a school, batajira kowaba ta yi gaba ata bar su Sumayya. Haka ko da yazo d'aukansu bata kalli inda yake ba har suka isa gida. Lamarin da ya yi mugun b'ata masa rai shima ya k'udiri aniyar fita sabganta.

A gida mummy tasata gaba sai tafada abinda akayi mata sabida Sumayya tace yau bata kulaba kowwa ba har suka dawo.

"Mummy kaina kemin ciwo da kuma inajin marata na mintsilina."

"Kintabbata iya abinda ke damunki kenan?."

"Eh."

"Baawanda yabata miki arai a gidannan kuma?"

Tai jim zuwa can tace "Mummy kice yaya mujaheed yabar tsokanata fad'a, ban son irin abinda kemin."

Kai mummy ta gyada tana shafa sumarta "Barni da shi saina sab'a masa sakarau, babban kobo kawai."

Tun daga nan tasami lafiya da neman fad'an Mujaheed sai dai kuma yawan kallon dakemata na takurata, tarasa me ya ke kallo ajikinta dake yawan kafeta da idanunsa masu bantsoro kamar na mazuru.

Ranar wata asabar da hantsi dikkansu suna zaune a part din Umma hira sukeyi cike da nishad'i, Baba Lado yayi sallam bayan an amsa ya ce "Ga wani saurayi can a bakin get ya ce inkira mishi Bahija, sunarsa Bilal ya sanarmin."

Tsalle ta doka cikin ihun murna ta ce "Baba kai min shi parlourn bak'i dan Allah ganinan zuwa."

Dukkan su baki bud'e suke kallonta. Har tasanja kaya tafito taja hannun Sumayya "Zo muje ki rakani aminiyar."

Har sun kusa fita, umma ta ce "Dawo kifadamin daga ina kika roroshi?"

Cikin dariya kasa-k'asa ta amsa "Umma surukin kine dan sarkin nan dana fadamiki." Batajira amsawan Umma ba tayi gaba tana cewa "Umma bak'onka Annabinka, sai nadawo."

"Allah yashirya yaran zamani."Umma ta furta cikin girgiza kai.

"Amin ." Bashir ya amsa yana dariya.

Tsaki Mujaheed yaja tare da mik'ewa ya fice a parlorn. Da idanu suka rakashi.

RAYUWAR BAHIJJA.Onde histórias criam vida. Descubra agora