page 18.

212 15 0
                                    

RAYUWAR BAHIJJA.

*18*
A cikin d'akin barci ya d'auketa, hayaniyar su Sumayya ya tasheta ta fice zuwa part d'in Umma batare da ta kula kowa cikinsu ba.

Kwanarsu Hindu biyar sukayi haramar tafiya gida. Umma tabawa ko wacce kayan kyalliya masu kyau da tsada ita kuwa mummy kayan gyaran jiki tabasu dangin su humra da kulacca da dai sauransu, suna ta godiya. Abba yayi musu kyautan kud'i sannan ya fidda babbar riga na shadda waganbari mai kyau da tsada da hula tare takalmi yace su kaiwa Malam, ya kuma bada turamen zannuwa suka kaiwa su Gwg. Bintu domin ita washe gari suka koma da Malam.

Misalin 11:15am Bilal ya iso domin shi zai maidasu kamar yadda ya kawosu.
 Shi da Bahijja ne tsaye jikin motarsa magana sukeyi a hankali yadda bamaiji sai su, ganin tak'i sakewa ya dubeta cike da damuwa. "Princess yanaga ranki ab'ace, ko da matsala ne?." Ya ambata cikin lek'en idanunta wanda ta sauke k'asa.

Bata amsa ba  ta ja baya tasoma tafiya ya bita cike da fargaba. D'annesa kad'an ta tsaya ta juyo tana kallon motar, idanun Munirat na kansu wacce ke zaune gaban motar ya yin da su Nana ke zaune seat d'in baya. D'auke kai ta yi ta kuma had'e giran sama da k'asa. Cikin sauke numfashi Bilal ya kamo hannunta ya langab'e kai cike da marairaita ya ce "Qeen dan Allah me nayi miki? Da kike cimin magani?"

Kallon hannunta da ya rik'e ta yi da sauri ya sa ki hannun "Queen ba kyaso inyi driving mai kyau ko?"

Ta girgiza kai, "To in haka ne fadamin damuwarki inji ko na sami natsuwar ruhina."

Sai da ta kalli inda Munirat ta ke wacce har lokacin idanun ta na kansu sannan ta ce "Me ke tsakaninka da Munirat?"  Tambayar tazo mishi abazata sabida haka sai duk ya daburce bakinshi na rawa ya ce "Wani abu akace miki akanmu?"

Da Ido ta kafeshi ganin duk ya daburce sai tasamu kanta da fad'uwar gaba. 'Shin kodai maganar Sumy zaitabba ne.'  Ta fada hakan aranta. Shiru sukayi suna kallon kallo shi da ita zuwa can kau shirun "Tunda kak'i amsamin tambayata to kayi maza ka maidata seat din baya, maryam tadawo gaba domin ban amince da zamanta gefen ka ba."

Kallonta kawai yakeyi yarasa gane inda ta dosa. Tsayuwa ya gyara yama motsa yatsunsa ya ce "Queen ban fahinci inda zancen ki ya dosa ba."

"Baki ta tura tare da zabgaw motar harara "Ok to bara nayi maka gwari gwari, cewa nayi Munirat ta fita a gabar motar ta koma baya sai Maryam tadawo inda ta tashi, kafahimta yanzu ko?" Kai ya gyada yana share zufar da ya tsatsafo mishi agoshi domin in akayi hakan zai zamo cin fuska. Gyaran mirya ya yi cikin kallon eyeball d'inta ya ce "Queen kiyimin alfarma ta zauna a inda take, next time sai in kiyaye tunda ba kyaso."

Zatayi magana ya rigata "Dan Allah dan Annabin rahama kada ki musamin, alfarma na nema".

 kauda kai ta yi ta motsa baki kad'an "Too nabari amma sai kafadamin abinda ke tsakaninku."

"Allah bakomi Queen sai 'yan uwantaka najini wanda kika sami."

"Uhm naji amma bangamsu."

"Dan Allah kiyarda dani ni nakine ke daya tak har abada, bawata agabanki, haba my princess hasken ruhin Muhammad Bilal." Ya k'arasa cikin soka yatsarsa a dimple d'inta, buge hannunsa ta yi cikin murmushi, jinjina ya yi mata "Sai kayan saraki ita daya kwallin kwal."

Ta sa ki siririyar dariya tana jijjiga kai sama cike da jin dad'i. Suka jero zuwa wurin motar suna zancensu cike da nushad'i.

 Bayan ya daura belt ya dubeta "Haskena kada kiyi barci yau kwana hira zamuyi."

"Angama Saraki." Ra amsa cikin duban Munirat ta gefen ido, ta hango fuskan nan nata tamkar anyi gobara, zagayo gefenta ta yi ta dafa kafad'arta "Dear Neerat agaishemin da Mama, nagode sai nazo bangajiya bada jimawa ba."

Motsa kai ta yi batare da tayi magana ba.

Suka had'a ido da Maryam ta yimata jinjina da hannu afakaice murmushi ta sakar mata cikin cewa "Nana sai nazo bikinki."

"Kai Adda Bahijja ni sai kinyi zanyi."

Cikkn hararar wasa ta amsa "Ni sai nayi degree har da digir-gir yarinya, sabida haka kisawa kanki onga ki shiga daga ciki abinki."

Dariya sukasa dukkansu har da Bilal.

Cikin dariyar ta dubi Adda Hindu "Adda amik'amin dubun gaisuwa wurin Goggo da su Ado."

"Insha Allah zasuji."

  Tana tsaye har suka fice gate sannan ta juyo tayo ciki cike da kewa.

*
Kwanci tashi har lokacin aikin hajji yazo, suka tafi tare da su Umma, suna can result dinsu yafito. Suna dawowa  da watanni aka soma yin registration Bashir ya shige gaba har saida komi ya kammala, suka soma zuwa lecture cike da d'oki musanman Bahijja wacce batayi zaton rayuwa zata sauya mata haka ba. Sumayya mass com zata karanta Bahijja kuma computer science. Karatunsu na tafiya cikin nasara babu matsalar komi sai d'an abinda ba'a rasa ba. Hakan ya samune bisa maida hankali da sukayi akan abinda ya kawo su sannan suna girmama malamansu maza da mata sun tsame kansu daga cikin tsagerun jami'a domin har wasu nayi musu dubin wad'anda basu waye ba, sam hakan bai tab'a samunsa ba balle su biye musu, wannan halayya nasu ya janyo musu daraja ainun musanman ga samari dan suna shakkan tunk'ararsu da zancen soyayya balle na sha-shanci.

*
Soyayarsu da Bilal sai k'ara bungasa takeyi sai dai tana zargin yana boyewa mata wani abu amma tazuba mishi ido tagani ko zai fadamata.

Tsaye take tana daura agogo a tsintsiyar hannunta, ta tsinkayi k'amshin turarensa mai dadin shak'a dik da tasan da hakan amma batayi tab'a nuna masa ba sai ma kushewa da ta keyi kullum in ya sanyo. Amsa Sallamar nasa ta yi tare da abin gefensa zata wuri batare da ta gaishe shi ba. Ya rik'o mata gefen gyale wani kallo banza ta watsa mishi ta fizge gyalen ya yi gaggawan janyo kafadunta ya rik'e gam tare da matsasu ta runtse ido ta bud'e ta wullo masa harara murmushi ya yi tare da cije gefen lip.

"Haka aka ce miki ana tarban masoyi?." Ya ambata a saitin kunninta.

Ido ta zare tana waige-waige, sarai yagano manufarta kada wani yajiyo abinda ya ce.

Ganin bakowa a parlourn ta sauke ajiyar zuciya ta hankad'a shi ya kuma rik'e ta da kyau, cikin fushi ta nuna shi "Allah lafita hanyata Jaheed, wallahi Allah ya kyauta inzamo masoyiyanka, nafadama ni din kayan Saraki ne, kai d'in kam dai gani sai hange daga nesa duk kuwa maitanka sai kabarni, Bahijja dai kwalelen mai k'aton ciki." Tana gama fad'a ta kufce.

Yana murmushi ya amsa "Yo ai 'ya'yanki ne a ciki 'yan mata." Ya furta yana shafa tumbinsa.

Tsirtar da yamu tayi  "Kai Allah ya tsareni, can gasu gada wai zomo yaji kid'an farauta." Ya zaburo ta fice da gudu tana gyara ruk'on handout dinta.

Bayanta yabi da kallo cike da sauk'in k'aunarta "Insha Allah sai na mallaki komi naki yarinya." Yaa ambata a hankali. Dinning ya nufa dan yin break, yana cin break d'in yana sa kin murmushi.

RAYUWAR BAHIJJA.Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang